BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 83 END

83 End*

………Matsalar ba’a raye-raye bane kawai ko abinda bai dace ba ko mara amfani. Akwai canja abokai, dan dole ne yay abokai a wannan yanar gizon, tun ana ƴar nesa da juna har a kai ga haɗuwa, bai san tarbiyyar waɗan can ba ko inda suka fito, sai kiga an koya masa sabuwar ɗabi’ar da baki san yaronki ko yarinya da shi ba. Shaye-shaye ne, maɗigo ne, luwaɗi ne, fashi ne, sata ne, yahoo ne, kai da ire-irensu daban-daban. Wlhy ko a film naga yarinya na shan shisha inajin zafi a zuciyata, dan wata daga wannan abinda ake ɗauka faɗakarwar zataji daɗi ta cigaba, saboda mu a namu wautan ɗaukar shisha muke ba shaye-shaye ba ma. Daga faɗakarwa an koma feɗe tarbiya, an gyara goma biyar bata gyaru ba. Kullum ƴarki abokai da ƙawaye na janta/jansa bin joint-joint, inda anan zata haɗu da wasu masu buɗaɗɗen idon da yafi nata kuma ko yafi nasa. Ya ALLAH, iyaye dan ALLAH mu dake da addu’a. Sannan muma a karan kammu mu gyara halayen da muka san munayi marasa ƙyau. Dan ba media bace bala’i kawai muma a karan kammu bala’in kammu da kammu ne. ALLAH yasa mu dace.

       Ba Fadwa ba kowa ma a falon jikinsa yay sanyi matuƙa, hankalin iyaye da yawa da ba ɗaukar komai suke matsayin komaiba ya tashi matuƙa, dan kamar an farkar da su ne abinda suka kasa hangowa a tsayin hangensu. Fadwa kuka take matuƙa tana mai dana sani da nadama mara misali. Dan kuwa yanar gizo bata bata komai bai sai komawa baya da sakata a gurbin nadama saboda batabi hanyar da zata amfana da ita ba. Inama sauran wanda suke hali irin nata suma zasu farga da wuri kafin su rasa abinda ta rasa koma fiye da ita. Inama zata iya goge abinda ya wuce a zuciya da idanun mutane?. Sai dai kaico, duk da ta daina a yanzu ko waya bata riƙewa haka bai hana videos nata cigaba da yawo ba a media, saboda wasu sun adana a wayoyinsu, kuma suna cigaba da zama illa a garesu tunda suna koyi da su matsayin abin birgewa. Duk wanda ya koya daga gareta kuma ya lalace tanada kamasho na zunibi itama. Kenan ita baɗala koda kayita ka daina sharrinta na biye dakai har bayan ranka, wani lokacin ma har jikokin jikoki? Ya ALLAH ka ganar damu gaskiya tun kafin ta ƙuɓuce mana. Ka shiryar damu tun kafin guri ya ƙure mana, ka ƙuɓutar damu tun kafin ajali ya riskemu. Ka goge laifukamnu tun kafin ƴayanmu da jikoki su riskesu????????????.

         Abie ne ya katse tunanin kowa cikin gyaran murya. Hakan yasa kowa maida hankali a garesa. “Babban abinda ya taramu anan shine sake bada haƙuri da roƙo ga iyayenmu, yayunmu, ƴaƴanmu, kuma ƴan uwanmu. Yaya Muhammad, Alhaji Sadiq, Babana Shareff. Musamman abinda ya faru ya rigada ya faru, kuma hukuncinku dai-dai ne dan duk ɗan halak idan an zunguresa ya dace ya nuna yaji zafi kuma ya ɗau mataki.  Sannan wanda yay laifi idan anga nadama a cikin idanunsa da ayyukansa ya kamata ai masa afuwa koda kuwa bazai samu girman daraja irin ta baya ba. Kamar yanda na roƙa a tun sanda kukai sakin nan kuka maidasu bada sanin kowa ba har su a karan kansu dan mu barsu su horu muga kuma idan zasu gane gaskiya, to Alhmdllh sun gane, a tsahon kusan shekara guda. Ina roƙon alfarmar ku maidasu ɗakunansu, ya rage nasu su riƙe igiya ɗaya data rage musu kosu barta itama ta katse a yanzu. Fatanmu zuminci ya cigaba da gyaruwa ba ɓaci ba, sannan dama shi mai laifi ana masa gargaɗi idan yaji to falillahil hamdu, idan ya nuna kunen ƙashi sai a barsa da halinsa ALLAH ya hukuntashi da ikonsa. Halima da Nafisa kunada sauran igiya ɗaya na aure kuma mun roƙa alfarma an maidaku tun kan ku kammala idda, amma bawai hakan na nufin ku cigaba da abinda ranku ke so ba a wannan family, dan a wannan gaɓar mun shirya ɗaukar mataki akan kowacce dazata zame mana iblis wlhy, babu kuma wani cikinmu dazai sake mata alfarma.”
     Sosai Mommy da Gwaggo Halima ke hawayen daɗi, har basu san sun fara zuba godiya da addu’a akan Abie ba. Yay murmushi kawai dan kuwa bai taɓa tunanin ganin irin wannan ranar ba. Hankalinsa ya maida ga Shareff dayay kicin-kicin da rai, sai dai wani sashe na ransa ya masa daɗin maida Mommy, ya kuma sake jin kima da mutuncin Abie a cikin idanunsa da ransa…..
    “Babana”.
Abie ya katse masa tunani.
Ɗagowa yay ya dubesa, sai dai baice komai ba. Abie ya murmusa ganin yanda ya tsuke fuska. “Nasan a gareka abune mai matuƙar wahala iya manta komai, shiyyasa ko a wancan karon ban tunkareka ka maida Fadwa ba, na barka ka huce sosai da sosai kafin muzo a wannan gaɓar. Babu mai tilasta maka a cikinmu, amma zamu roƙeka alfarma. Dan ALLAH ka maida matarka tunda tayi nadama…..”
     Kansa ya shiga girgizawa a hankali. “Abie batai nadama ba, tana muku lumbu-lumbu ne kawai. Koda zan iya maidata domin darajarku bazan taɓa sake sonta ba, bazan taɓa ganinta da mutunci ba, bazan taɓa iya sauke dukkan hakkinta ba. Har yanzu ina ganinta a idona mai ɓakar zuciya, mai mummunan hali, mai karancin tarbiyya, ballagaza da bata san kima da mutuncin kanta ba, Abie mazafa kallonta sukeyi sunaji wani abu a ransu, shin yara matasa nawane da magidanta sukaji hakan? Mutane nawane suka kalleta a hakan? Ta daina amma har yanzu abinda ta shuka na yawo a wayoyin mutane? Bazan iyaba Abie, wlhy ko tunata bana sonyi, bana son ganinta sam……”
     “Karka tsaurara da ƙarfi babana. Nasan akwai ciwo, akwai ɗaci, akwai raɗaɗi. Sai dai muɗin ba masu shiryarwa bane ba. Sannan samun miji na gari na ƙwarai a gareta a yanzu abune mai wahala, duk da nasan wasu zasu iya amfani da nasibin da ALLAH ya bama mahaifinta na suna da dukiya suce zasu aureta, tunda wasu a gurunsu abinda ta aikata ba komai bane a wautarsu, sai dai bai zama lallai su zama na ƙwarai ba……”
     Fadwa dake kuka ta ƙatse Abie ta hanyar rarrafowa gabansa. “Wlhy Abie bazan iya zama da wani namijiba inba shiba. Ina sonsa, kuma ni kaina ina kaico wa rayuwata ta baya. Na ɗauka abinda nake ba komaiba sai nishaɗi kawai, na ɗaukesa matsayin zamanine kawai, na ɗaukesa matsayin lokacina ne kawai. Wasu tsurarun mutane da bazasu amfaneni da komai a duniya da lahiraba kwarzantawarsu a gareni na ingizani inajin babu yani. A tunani na abinda nake ba komai bane tunda ba’a zahiri baneba. Ashe mummunar rayuwace mai wargaza ƙyawawan ayyuka. Ashe ƙofofin matakin zuwa ga zina ce, ashe raguwar darajace a gareni matsayin ɗiya mace, ashe tanadin abin faɗa ne ga ƴaƴana ga ƴan uwana. Ashe makullun rusa dukkan farin cikina ne da rayuwar aurena. Ashe ƙanƙantar da kaina nake tamkar dabbar da bata san inane rufe ko buɗe ba. Kaico na da wannan rayuwa, kaicon duk wata mace mara kamun kai da fahimtar rashin daidai matsayin nishaɗi ko birgewa. Kaicon mace irina dake nuna rashin ingancin tarbiyya da mutuncin iyayenta wa duniya. Nima bazan matsa maka ka maidaniba, amma bazan daina son ka ba, zan mutune da sonka Soulmate, zan amshi wannan hukuncin domin nasan UBANGIJI ne yake horani ta hanyar aza sonka a raina fiye da komai. Na godema ALLAH daya saka maka da mace tagari tun kan kasan niɗin wacece. Na gode ALLAH daya fargar dani illar abinda nakeyi tunkan tsufa da mutuwa su riskeni……”
    Kuka ya sarƙeta, tausayinta ya saka Anaam fara kuka itama. Amma ga Shareff sai ma faman taɓe baki yakeyi alamar ko’a jikinsa. Dan shikam dai har cikin ransa baya fatan sake zama da Fadwan. Sai dai yana mata fatan shiriyar da tace tayi dan shima yana fatan ALLAH ya shirya masa nasa ƴaƴan daya fara haifa da ƙanensa dama duk ƴaƴan musulmi.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button