Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 83 END

Ad

_____

     Duk fa yanda aka buga Shareff bai yarda da maida Fadwa ba. Dole aka ƙyalesa dan har yanzu yana akan dokin fushi. Haka taro ya tashi su Mommy dai zasu koma ɗakunansu.

………………

     Rayuwa ta cigaba da shuɗawa har ALLAH ya sake bama Anaam ciki, a kuma lokacin su Abie suka dawo Nigeria, dan haka Muhseenah ta koma hanunsu, wani lokacin kuma tana wajen Mommy data dawo tuni, hakama Gwaggo Halima ta koma, sai dai kuma duk da mijinta ya ɗare karagar mulki ta koma ƴar kallo, komai amaryace ke zartarwa itama ake kira first lady. Haka Gwaggo Halima keshan kukanta, ta kuma ɗauka ɗammarar haƙurin zaman ƴaƴanta. Anaam aka cigaba da rainon ciki har ALLAH ya sauketa lafiya. Alhmdllhi wannan karon dai da kanta ta haihu ɗan ta namiji mai kama da Shareff, anyi farin ciki matuƙa an kuma sha shagali. Yaro yaci sunan Daddy. Wato Muhammad Ameen. Za’ake kiransa Muhammad ɗinsa. Anaam da Shareff suka cigaba da rainon ɗansu, wani lokaci Muhseenah takanzo tai musu har sati suma duk da dai kullum sai sun ganta idan sunje kai Muhammad gida idan zasu aiki ko sun taso. A haka shima ya girma yakai yaye. A kuma lokacinne ALLAH yayma Gwaggo data koma abin kwatance rasuwa, tanata kururuwa da ihun a kira mata su Daddy, sai dai kafimma suje rai yayi halinsa. Dolene kaga gawar Gwaggo ta baka tsoro, ta mugun komawa ƴar tsurut kamar ba gawar mutum ba. Ƙarshen Gwaggo ya sake sanyaya zukatan su Mommy matuƙa.

      Muhammad nada shekara uku a duniya rabuwar Fadwa da Shareff kuma shekara shida Abie ya sake roƙon Shareff maidata ɗakinta, dan har yanzu ta kasa aure, mazanma da ake tunanin zasuzo kodan alfarmar mahaifinta tamkar ALLAH ya dakatar dasu duk wanda yazo gareta sai da wata manufa amma ba aure ba. Takanci kuka matuƙa idan suna mata izgilanci da abinda ta aikata baya. A wannan karon dai da ƙyar ya amince, sai dai ya sake tabbatar mata bazai taɓa ƙara sonta ba, ba kuma zata samu wani farin ciki daga garesa ba.
     Tana sonsa dan haka ta yarda da hakan da tunanin zata iya haƙuri aka sake ɗaura aure. Sai dai kuma a tarewarta gidan ta tabbatar da abinda ya faɗa ɗin, dan ta kasa gane komai na Shareff, yana sauke mata dukan hakkin da ALLAH ya daura masa na ci da sha da sauran buƙatun rayuwa, amma ko fara’arsa bata gani balle samunsa a gado, kwata-kwata yaƙi kusantarta, babu wata soyayya a tsakaninsu yanzu, komai yana mata alamar tilasne zama da ita ya zame masa dan iyaye. Takanci kuka ta gode ALLAH musamman idan taga yanda suke soyewa da Anaam a gidan kamar suna mantawa da zamanta. Dan ma Anaam ɗin kan noke wani lokacin a gaban idonta. Ga wata irin soyayya da take gani yanama ƴayansa tamkar ya cinyesu. Dan cikin da Anaam ta samu na uku a gidan sai da taji tamkar ta haƙura da auren ma. Gaba ɗaya ya gama lalacewa a kan cikin, koda yaushe yana manne da Anaam ɗinsa da ƴan ƴaƴansa. Ita tsakaninta dashi kawai abinda yake wajibi. Ya hanata riƙe waya kuma sai rakani kashi, itama ya tabbatar mata zai barta da itane domin adalcin kiran iyayenta. Amma kuma kullum cikin bin ƙwafɗin wayar yake. Hakan na damunta, dan a yanzu sam babu wata yarda a tsakaninsu koda ta magana ce. Ko abu ta faɗa masa sai yace sai ya bincika. Tasan alfarmar Abie kawai takeci na zaman gidan. Amma ta rasa Shareff har abada. Ga haihuwa shiru kaleji babu labari har yanzu, koda yake ba’a kusanceka ba ina zaka haihu. Hakan ma na sake tada mata hankali dayin nadama mara misali.
      A yanzu ma kuka take tana kallon Shareff ɗin da su Muhseenah da tazo musu weekend ta window. A tsakar gida suke suna buga ball harda Anaam dake fama da tsohon ciki. A bisa tsautsayi Anaam ɗin ta gurɗe. Gaba ɗaya Shareff ya ruɗe shida yaran duk sukai kanta, jikinsa ya jawota cikin tsananin tashin hankali, itako tana faman riƙe ƙugu da kiran sunansa.
      “Bayana Yaya, cikina, ƙafata ta riƙe, Yaya muje asibiti wayyo Mamie na”.
    Ai babu shiri yay sama da ita yakai mota, dole Fadwan ta fita itama domin taimaka musu. Amma sai yay kamar bai ganta ba har saida Muhseenah tai magana tana kamo hanunta. “Mamah kizo kima Miminmu addu’a Please kinga tana kuka”.
      Cikin ƙarfin hali ta saci kallon Shareff dake ƙoƙarin saka Muhammad a mota. Amma yay kicin-kicin da rai. Muhseenah ta nufesa tana faɗin, “Abbu Please aje da Mama mana ta riƙeta tunda kai zakai tuƙi”.
     Har yayi niyyar ballama yarinyar harara sai kuma ya dake, ya ɗaga mata kai kawai dan yasan fitinar Muhseena ba barinsa zatai ba. Balle gata da shegen wayo, ba kuma ya son ko kaɗan tasan wani abu mara daɗi tsakaninsa da Fadwan. Dan ko Anaam bayayi a gabanta tsakanin shi da itane kawai yake horata. A dalilin Muhseenah suka tafi asibitin tare, suna zuwa babu jimawa ALLAH ya sauki Anaam ɗin lafiya namiji.
    Cikin ƙanlanin lokaci zance ya zagaye dangi. Kowa sai murna da fatan alkairi, dandanna asibiti ya cika da dangi. Sai da aka sallamesu ƙura ta koma can gidan aka cigaba da shagali. Shima dai yaro yaci sunan Abbah ranar suna. Wato Abubakar Sadiq, zasu kirashi da Saddiq ɗin. A wannan sunanma dai Anaam da jariri sunga gata, itako da iyayenta babu abinda zasuce ma ALLAH sai godiya. Dan yanzu dai family ya zama tsintsiya madaurinki ɗaya kowa na hakuri da ƙoƙarin kai zuciya nesa koda rai ya ɓaci.
Bayan suna da wasu kwanaki Fadwa ta zaɓi neman saki ga Shareff bayan tayi shawara da Gwaggo Halima, itama dai jikintane yay sanyi dan tasan dama an takurawa Shareff bisa komawar Fadwa gidansa, yana jin kunyar su Abie ne kawai shiyyasa ya amince. Amma a yanzu tunda ita Fadwan da kanta ta zaɓi haƙura da zaman ALLAH yasa haka shine yafi alkairi a garesu, dan insha ALLAH a yanzu itakam bazata sake bari wani abu ya shiga tsakaninta da ƴan uwanta ba, saboda komai Fadwa ta zama a baya itama ta bada nata gudunmawar wajen karancin bibiyar al’amarinta da tsawatar mata. A yanzu itama ta fahimci zamansu tamkar cutar da juna ne kawai, shi zuciyarsa a ƙuntace da ganinta, ita kuma zuciyarta a ƙuntace da buƙatarsa ta kuma kasa samu. Bai waniyi jayayyaba suka je gaban su Abie da kanta tai musu bayani, duk da sun fahimci hakan shine sauƙi da farin ciki a garesu basuji daɗi ba. Amma sun musu fatan alkairi, Shareff ya rubuta mata sakinta. Tana hawaye ta amsa dan harga ALLAH tana matuƙar sonsa, bakuma zata daina son sa ba har ƙarshen numfashinta. Ta zaɓi yin nesa da shine domin yazama cikin farin ciki, dan ta yarda da gaske baya son ganinta, ya tsaneta a yanzu. Shi kansa dai yaji tausayinta a wannan gaɓar, amma dai haka shine mafi sauƙi a garesu, dan yayi ƙoƙarin manta komai ya amsheta hakan ya gagara, bayajin zai taɓa iya ƙara kusantar Fadwa, badan komai ba sai dan daya tuna maganar samarin nan sai yaji tsananin tsanarta da zafinta, yanada kishi matuƙa akan duk abinda yake nasa, dan haka koya cigaba da zama da ita sai dai yayta cutarta dan yayi alƙawarin bazai sake kusantarta ba. Yana mata fatan alkairi, idan tuba tayi na gaskiya ALLAH ya saka mata da abinda zai zame mata alkairi anan gaba.✍

To nima dai bari nace Alhmdllhi, ALLAH ka ƙaramana haƙuri da juriya a duk yanda wasu zasu so ganin fushinmu ko ɓacin rai ko damuwarmu ALLAH ya hana. Ya ƙara mana haƙuri da juriyar ɗaukar komai da zaizo a ƙaddarorinmu, ka hanamu yin kuka da dana sani mara yankewa a rayuwa.

Ad

_____

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button