BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 83 END

ALHAMDULILLAHI
     ALHAMDULILLAHI.
            ALHAMDULILLAHI

Godiya ta tabbata ga UBANGIJIN talikai daya bani aron rai da lafiyar rubuta wannan ɗan gajeren labari. Abinda na rubuta dai-dai ALLAH ka amfanar damu a ladar. Kuskuren ciki ALLAH ka yafemin.

     Wanda duk naima ba daidaiba a yayin rubutunsa ya yafemin, abinda yazo ba’a haka kuka so ba kuyi haƙuri a haka labarin yazo. Ina fatan kuyi amfani da amfanin ciki ku watsar da marasa amfani, dan wani abun ana sakashine dan kawai nishaɗi. Yaranmu masu tasowa ba komai najin daɗin rayuwa dake zuwa a novels ake samunsa a zahirin rayuwa ba. Kowanne bawa da ƙadarar da ALLAH ya tsaro a tasa rayuwarsa. Idan kinga saɓanin rayuwarki dana littafi ki ɗauka wancan labarine dan fadakarwa da nishaɗi bawai dan sai kin tabbata ko kin samu irin rayuwar ba.

ALLAHU ka gafarta mana ka gafartama iyayenmu. ALLAH ka yafe mana.????????????

Kamar yanda na fada a tiktok akwai mutanen kirki, masu yada alkairi DA yawa, hakama akwai na banza, mun tabo irinsu fadwa ne Dan su san illa na abinda suke aikatawa, muna musu kuma fatan shiriya da gane gaskiya kafin komai ya kure musu fiye DA Fadwa. Kazama mutumin kirki sai addininka DA al’adarka suyi alfahari DA kai. Ka kuma zama cikakke a cikin al’ummar MANZON ALLAH (S.A.W) ba komai bane nishadi kamar handa muke kallo a rayuwar wasu yan tiktok, wani abun zubda mutunci DA darajane matsayinki na diya mace musulma.

Masoya muna godiya dan bazamu gaji da godiya a gareku ba akoda yaushe. Muna godiya matuƙa da kasancewar ku da zafafa biyar cikin tafiya mai nisan zango. ALLAH yabar zuminci ya kara mana zama lafiya da kaunar kauna. ALLAH ka bamu shugabanni na gari. Wannan zabe dake tunkaromu ALLAH kasa ayi lafiya a gama lafiya. ALLAH ya zaunar damu a gidajenmu lafiya bisa soyayya da kaunar juna tsakaninmu da mazajenmu. ALLAH ka shirya mana yaranmu damu baki ɗaya. Waɗanan fitintunu da wayoyi suka kawo mana da yanar gizo ALLAH ka bamu ikon tsallakesu. Wanda suka afka ciki ALLAHU ka shiryesu ka ganar dasu gaskiya kafin lokaci ya kure musu. ????????

Fatan alkairi ga kowa da kowa a duk duniyar dankuke. Kaunar kauna irin trillions ɗin nan masoya????????????????

Taku

Bilyn abdull ce????????????????.

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button