BABU SO 9
Typing????
*_❤????BABU SO....!!❤????_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*. *_Typing????_*
*_❤????BABU SO....!!❤????_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
09
………Murmushi Fadwa ta sakar masa, cikin narke murya taima hannunta kiss da hura masa .
“I miss you my Soulmate”.
Kansa kawai ya jinjina da wani ɗan guntun murmushinsa iya laɓɓa. Cikin iyayi da feleƙe ƙawayen nata ke gaishesa idanunsu kamar zasu faɗo a kallonsa. Ɗan tsuke fuska yay yana amsa musu sama-sama.
“Baby am sorry na saka wahala”.
Fadwa ta sake faɗa tana sake narke masa har tana saka tsigar jikinsa tashi. Nanma murmushi kawai yay mata da kauda kansa daga gareta dan shi kaɗai yasan halin da dama yake ciki ita kuma tana son sake kunnashi da wani. Cikin motar yay ƙoƙarin komawa da nufin ɗakko mata saƙonta, ita kuma batare da tunanin tare yake da kowaba ta nufi ɗayan side ɗin a zatonta anan ya ajiye saƙon nata ne, tana kuma son ƙara birge ƙawayenta da akaikaice tasa ake musu hoto acan gefe batare daya sani ba….
Sosai Anam ta cika tayi fam da takaici, tayi yunƙurin buɗe motar ta fita taji ya sakata a lock dan yasan dama abinda zata iyayi kenan tace zata fita kamar wancan ranar. Ya ɗakko ledar dake a back sit ɗin Fadwa ta buɗe ita kuma. Ido huɗu sukai da Anam, ta watsa mata wani kallon banza ta ɗauke kai dajan siririn tsaki da faɗin “Ballagaza” a hankali….
A yau kam tayi laƙawarin bazata ƙyale ƴar iskar yarinyar nan ba. Cikin jin ɗacin (ballagaza) data kirata dashi tace, “Kin yima ubanki dan uwarki.”
Duk da Anam bajin hausa take da ƙyau ba tasan zagi, amma sai tayi kamarma bataji Fadwa ɗin ba, taciro Bluetooth daga bag ɗinta ta fara ƙoƙarin maƙalawa a kunne Fadwa ta buge hanun Bluetooth ɗin ya faɗi ƙasa. Ƙafa tasa ta takesa da shegen takalminta mai tsananin tsini……
“Fadwa!”.
Shareff ya faɗa a ɗan kausashe…..
“……Amma dai Soulmate kanajin tsakin da taimin ai, ranar na ƙyaleta daboda darajarka, amma yau gaskiya bazan iyaba, ban son raini..!”
Itama ta faɗa da sauri cikin tarar numfashinsa.
Anam data sake cika tai fam tai yunƙurin hanɓarata baya ta futa. (Yo dama a gayama kura gayyar cin nama bayan bidirin nasu ne????. Ba’a takali Anam ba ma yaya aka ƙare balle anzo har gida da goron gayyata????).
“Idan kika fita a motarnan sai ranki ya ɓaci!!”. Yay maganar a tsawace da fisgota ya maida ya zaunar. Kuka ta fashe masa da shi dan zuciyarta tazo wuya. Baibi takantaba yay yunƙurin fita a motar sai ya hango Fadwa can ta nufi motarta a fusace ƙawayenta na take mata baya. Idonsa ya rimtse da taune hakwaransa, sai kuma ya furzar da huci mai zafi yaja murfin a fusace ya rufe, na side ɗinta ma shine ya rufosa ya tada motar suka bar wajen dan tuni su Fadwa ma sun fice a wajen har tana bulama mutane ƙura.
Cikin sake tunzurasa da kukanta keyi yaja birki da ƙarfi, firgita tai ta ɗago da sauri tana kallonsa. Harara ya watsa mata tare da gangarawa gefen titi ya kashe motar. “Nidai ka kaini gida, kuma saina sanarma Daddy mata na maka kiss a titi da rungumek….”
Bamm ya bige bakin nata, kukan ƙarya ta sake fashe masa da shi dan ko hawaye babu yanzu sai dai taji zafi sosai. “Har Abba ma saina faɗawa da Abie da Mamie da Mom da aunty Amarya”. Ta sake faɗa da ɓalle murfin motar zata fice. Riƙota yay ya maida murfin ya rufe yasa lock. Takaicinsa da haushin abinda Fadwa ta masa yasa takejin zafinsa batare data san dalili ba, cizo tai ƙoƙarin kaima hanunsa dake riƙe da nata….
“What!! Ni zaki ciza?”.
Bata kulashi ba ta sake kaima hanun cizo. Babu shiri tilas ya saketa, yana mai girgiza kansa. A hankali yakai kwance jikin kujera bayan ya kwantar da ita, hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa ya lumshe idanu yana mata kallon ƙasan ido. Tunba yanzuba yasan Anam fitinanniya ce dama, sai dai yayi zaton tabar tsiwa zuwa yanzu, amma tun tana ƴar ƙaramarta boss ce daman. Yasha zuwa hutu ya samu an kawo ƙarar Anam daga school ta naɗi ƴaƴan mutane babu dalili, idan kuma gidansu akazo nanma ta jibga, idan gidansu taje yaran ba tsira sukeba. Ƴaƴan aunty Mimi ba ƙaranar wahalar Anam sukaci ba duk da wasu sun girmeta bata ɗaga musu ƙafa……..
“Nidai ka buɗemin, bazan sake shiga wannan motar ba da akeyin wannan abun….”
Duk yanda yaso danne murmushin dake son fita ya gaza hakan, gefe ya maida kansa yay murmushin kafin ya tashi zaune sosai fuska a haɗe ya riƙo hanunta dake jikin handle ɗin ƙofar, baki ta buɗe zata saƙi ƙara dan matse hanun yayi yasa yatsunsa biyu ya riƙe lips ɗin nata fuskarsa a tsananin haɗe. Sosai idanunta suka sake firfitowa, ga tsoro ga tsiwa……
“Haɗiyemin wannan kukan, ki kuma faɗi miye abunda akeyin kona tattakaki”.
Tsaf ta haɗiye kukan zuciyarta na bugawa da sauri dan kusancinsu yayi matuƙar yawa, kanta ta fara jujjuya masa a hankali. Idanu ya zare mata da sakin lips ɗin nata, “Ai saikin faɗa mara kunya”. A tsorace take amma bakin yaƙi mutuwa. Taja jikinta baya da maƙurewa a jikin ƙofa, “To ka bari muje gaban su Daddy ɗin basai na faɗa ɗin ba….”
Bakin ya sake kaima ɗalli tai saurin duƙewa da cusa kanta a tsakanin cinyoyinta. Ƙwafa yay da komawa jikin kujerar ya lafe yana kallon waje, kusan mintuna huɗu suna a haka ring ɗin wayarsa ya katse shirun nasu. Iska ya ɗan furzar da kallon wayar, ganin Daddy ya sashi ɗagawa yakai kunne a ladabce yay sallama.
“Shareff kuna ina?”.
Ɗan jimm yay saboda jin muryar Daddyn, sai kuma ya gyara zama da ƙoƙarin yima motar key yana bashi amsa. “Daddy gamu a hanyar tahowa gida”. “To inna jiranku”. Kafin ya sake cewa wani abu ƙitt an yanke wayar. Shiru yay yana kallon wayar sai kuma ya sake furzar da numfashi. Ruwa ya ɗauka a baya ya miƙama Anam da itama ta ɗago tun ɗaga wayarsa. “Malama anshi ki wanke wannan banzan hawayen”.
Baki taɗan tura gaba kafin ta amsa, ta buɗe murfin motar batare data fita gaba ɗaya ba ta wanke fuskar. Bag ɗinta dake kan cinyarta ya ɗauka ya buɗe, zatai magana ya harareta. Komai babu na kayan kwalliya da ƴammata kan ɗan fita da shi a bag sai lipsgloss kawai. Baice komai ba ya maida jakar ya rufe, tissue ya ɗiba guda uku ya miƙa mata sannan ya harba motar saman titi.
Tafiyar mintuna ƙalilan ta kawosu gida, tunda aka buɗe musu gate ya sake tabbatar da babu lafiya, dan ganin masu baƙaƙen kayan nan yasan Aunty Halima ce a gidan. A karon farko yaji zafin hakan matuƙa, shikenan da abu ya faru tsakaninsa da Fadwa sai iyaye sun shiga ciki, to shikam idan anyi auren yaya kenan kuma?. Ita dai Anam ba fahimtar komai tai ba, dan tun kan ma ya gama kashe motar tai ficewarta sashen Mom a zatonta ma ko baƙi Abba ko Daddy wani yayi. Binta yay da kallo harta shige, ya sauke numfashi a hankali shima yana fitowa. Sashen Daddy ya nufa duk da yasan bai wuce ɓacin rai zai tarar ba.
Tun kafin ya ƙaraso yake jin hargowar Gwaggo Halima daketa masifa, ya girgiza kansa kawai ya shiga falon da sallama. Da Fadwa dake faman rusar kuka suka haɗa ido, ya ɗauke idanunsa fuskarsa na sake tsukewa. Sosai Mommy ke antaya masa uwar harara, hakama Gwaggo.
Daddy dai kallonsa kawai yakeyi cike da nazari. Shiko Abba murmushine ma akan fuskarsa yana sauraren ƴar uwar tasu kuma yayarsa. Ƙasa ya zauna ya shiga gaishesu. Abba ne kawai ya amsa da daɗin rai, sai Daddy daya sauke ajiyar zuciya. Mommy kam da Gwaggo hayayyaƙo masa sukai da masifa kamar yanda Gwaggo Halimar ta rufesa da tata. Shi dai babu wanda yacema uffan a cikinsu, kansa a ƙasa ma yake. Sai da sukai mai isarsu sukai shiru duk da Abbah nata son dakatar da su sunƙi saurarensa.