BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 9

    ★★

Tunda ya shiga ɗakin bai sake fitowaba. Kwance kawai yake a gado ko takalmi bai cireba balle maganar wanka har aka kira magrib. Tashi yay ya nufi bayi yayo wankan a gurguje da alwala. Tsabar bai buƙatar haɗuwa da kowa ta baya yabi ya fita massallaci. Bai kuma dawo ba dan koda akai sallar isha’i can ya koma kan wani dakalin maƙwaftansu ya zauna…..


       
      Tunda suka dawo gidan batabi takan kowaba. Tadai shiga ta gaida Mom sannan ta wuce ɗakinsu. Wanka tayi batare data ko shafa mai ba balle saka kaya ta kwanta da towel ɗin jikinta dan wani irin barci ke rinjayar idanunta kasancewar sanyin ruwan wankan dana jiƙar towel ɗin na ratsata. Barci sosai mai nauyi ya kwasheta, acikin barcin taji kamar abu na binta.

A ɗan zabure ta farka ta hau dube-dube. Ganin jini ya sakata zaro idanu da dafe goshi. Shaf ta manta da batun zuwansa duk da sai jibi ya kamata ta gansa ma. Gadon ta ɗan dudduba, ganin bai ɓaciba ta nufi toilet da sauri, towel ɗin dai ya ɓaci kasancewarsa sky blue ya nuna sosai.

Tasan yana mata zuba sosai shiyyasa bata wasa, gashi tanata son siyen audiga dama amma shiririta tasata mantawa dan ta saba sai da taga Mamie ta ajiye mata da lokacin yinsa yayi gareta. A gurguje ta gyara jikinta ta fito, baƙar abaya kawai tasa ta ɗauka atm ɗinta tayo waje.

Ɗakin Mom ta leƙa ta samu tana salla, bazata iya jiraba dan akwai matsala zai iya sake ɓatata. Yanzunma handkerchief ɗinta sabo tai amfani da shi kafin. A falo ma duk sauran yaran sun fita massalaci kasancewar duk yaran Mom mazane aunty Rahma ce kawai mace, Husna ɗiyar ƙanwartace take riƙo bayan auren Rahama.


        Su Daddy sun riga har sun shigo ciki, hakan yasa bata samu matsalar isa gate ɗin ba duk da batasan a ina zata samo audiga ɗin ba, kawai zatai dai tambaya ko gurin mai shagon layinne da sukan siyo ƙananan abubuwa wajensa koza’a samu kokuma ya faɗa mata inda zata samo….


       Cak ta tsaya tare da saurin ja da baya saboda karo da sukaci, sosai gabanta ya faɗi, ta zabura da zummar komawa da baya tana kauda kai dan har yanzu haushinsa takeji akan abinda ya faru, Juyawa tai da sauri…..


      “Idan kika ƙara stap ɗaya saina karya ƙafafunki”.
           “Wayyo Anam kin mutu kawai”.
Ta faɗa tana rumtse ido da cije lip ɗinta kamar zata fasa ihu. Sai kuma ta juyo tana wani tamke fuska batare data yarda ta sake kallonsa ba, ita ala dole bata son yaga lagonta……….✍

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button