BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 9


        “Ina ita mara kunyar dan ubanta? Kai yanzu Shareff ko kishinmu ma bakayi duk yawan ƴan uwanka da muka haifa karasa wadda zakai yawo da ita a motarka sai bare…..”
        Haka kawai maganar ta bashi dariya, amma sai baiyiba yay murmushi kawai da ɗagowa ya ɗan dubi Gwaggon tasa datai maganar.


    “Eh kalleni da ƙyau mara mutunci, ko kanada wata alaƙa da ita bayan ubanta dake matsayin ɗan uba a cikinmu da har kake wulaƙantamin yarinya akanta?”.
          “Dan ALLAH ya isa haka Halima, maganar yarinya ko matsayinta duk bashi bane ya taramu anan. Kai Shareff miya haɗaka da ƴar uwarka?”.


    Numfashi ya sauke a hankali da ɗagowa ya dubi Abbah da yay maganar ya sake sunkuyar da kansa. “Abbah ni bansan wani abu ya faruba. Ina office ta kirani tana buƙatar abu, duk da ina buƙatar zuwa na huta kuma tana ƙasa dani na ɗauka nakai mata har inda take badan ina jin tsoronta ba…….”


     “Amma daka tashi zuwa ai da wancan bakwainin yarinyar kazo. Dama ranar da ita kaje gidanmu taimin rashin kunya da marina ka hana na ɗauki mataki kace zaka ɗauka da kanka, yau kuma harda zagina tayi tanamun kallon banza irin like akwai wani abu tsakaninku. Ni gara idan sonta kake ka faɗamin na barmata kai kawai dan bazan iya shearing ɗinka da wancan jakar ba….”


       Idanunsa yay bala’in rumtsewa tare da dunƙule hanunsa da masifar ƙarfi. Daddy dake kallon hanun nasa ya ɗauke kai yana ɗan murmushi, sai dai kamar yanda tun ɗazun baice komaiba yanzunma baice ba. Fadwa ta cigaba da sakin zance tana kuka har sai da Abbah ya ƙwaɓeta dan sai zagin Abie take da Anam….


      “You’re vary stupid. Baki san shi ɗin wanene ba a gareki? Ashe muma zaki iya zaginmu mara kunyar banza……”
     A zabure gwaggo ta tare numfashinsa da faɗin, “Yo Abubakar wane matsayi Usman kedashi a wajenku bayan ɗan uba da zaka balbaleta danta zagesa?”.


        “Haba Gwaggo wane irin magana ne wannan?”. Abba ya katseta ransa a ɓace. Gwaggo Halima zatai magana ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. “Bana sonji, daga yau kuma idan na sakeji a cikin ƴaƴanki wani ya zagi Usman to lallai ke kanki sai ranki ya ɓaci tunda akoda yaushe ke hankali baya isa miki cikin jiki.

Wannan magana kuma na kasheta anan, sannan Mamana nine nace kullum Al-Mustapha ya sauketa a wajeb aikinta ya kuma ɗakkota tunda shine babba wataran sunan uba zai amsa a garesu. Bana son sake jin ƙananun maganganun nan daga yau, nakuma dawo da bikinsu baya zanje na samu Alhaji Sadiq ɗin, magana ya ƙare ok”.


       Babu wanda ya iya sake cewa komai, sai dai har cikin rai maganarsa ta farko ta zafi wasu a cikinsu, ta ƙarshe kuma ta musu daɗi kusan su duka idan ka cire uban gayya daya shaƙa yay fam. A wannan gaɓar yaji mugun haushin Gwaggo a ransa fiye da koyaushe, dan ya gama gane itace ke assasa tsanar juna a tsakanin iyayensu da ƴan uwansu guda biyu kacal dan kawai suna matsayin ba uwarsu ɗaya ba. Shi ya fara ficewa a falon batare da ko kallon wani ya sakeyi ba.


     Da sauri Fadwa ta mike tabi bayansa har tanayin tuntuɓe zata faɗi. Tana kiransa ko waugota baiyiba duk da sarai yajita. Duk da taji zafi haka ta cigaba da binsa har part ɗinsu, yana ƙoƙarin shiga ɗakinsa tai azamar shan gabansa ta tare ƙofar. Mugun kallo ya watsa mata, sosai hanjin cikinta suka kaɗa amma saita daure ta marairaice masa fuska.


      “Haba My Soulmate yanzu ɗinma wulaƙancin zakamin?”.
          “Bani hanya!!”.
    Yanda yay maganar a tsawace idanunsa har suna firfitowa yasata saurin matsawa. Hannu yasa ya ƙarasa ingijeta ya buɗe ɗakinsa ya shige tare da bugo ƙofar da ƙarfi har sai da ta sake zabura….

     Acan falo kuwa Daddy ne yay amfani da damar fitar su Shareff ya shiga yimusu nasiha musamman Gwaggo da Gwaggo Halima da Mommy da duk matsalar take daga garesu. Duk da a cikin lalama da son bada shawara yay maganar sai Gwaggo ta fashe da kuka tana matsar ido da fyatar majina wai ta fahimci laifinta suke gani dan bata haifesuba.

“Shikenan Muhammadu nadai fahimci laifina kake gani, nidai ALLAH na gani ba inayi bane dan na rabaku da su kamar yanda kuke kallo sai dan kare martabarku da takaicin da uwarsu ta shaƙa mana a gidannan wajen mahaifinku. Babu annamimanci da kutungula da Zuwairah bataiba agaremu, akwai randa har sakinmu tasa mahaifinku yay a daren duk da ana ruwa yace mubar masa gidansa. Akwai randa ta ɗau hanun Halima ta turɓuɗa cikin murhu wuta naci wai dan ta zungurar mata icce.

Kai har kusan jefa mahaifiyarku tai a rijiya lokacin tana goye da Umaru. Taya azzalumar mace irin wannan zanso ƴaƴanta kuma na baku goyon bayan kusota duk da abinda taima ƴar uwata. Ai shara’armu da Zuwairah sai dai a lahira, gashinan makirar jikarta ta gadota a komai na makirci. Dan haka bazaku taɓa samun nutsuwaba a gidannan tunda annamimiya tazo jinin munafukai…..” Fyaaaatttt. Ta face majina da ƙarfi da nufar hanyar ƙofa ta fita.


     Mommy ma tashi tai a fusace tabi bayan Gwaggon tata. Cikin ɓacin Rai Gwaggo Halima ta dubi su Daddy. “Yaya kaji ko, duk da abinda uwarsa taima tamu uwar amma kuke nuna sonsa kamar…..”
      “Halima!!”.


Daddy yay saurin dakatar da ita shima ransa a bace. “Amma Yaya itafa gaskiya ɗayace daga ƙinta sai ɓata. Wlhy wlhy kaji na rantse bazan taɓa son su Usman ba a gidannan. Har duniya ta tashi sunansu ƴan ubane a gareni, bawai ƴan uwa ba”. Fuuu ta figi jakarta ta fice. Duk da kallo suka bita.

Abbah ya fara sauke ajiyar zuciya da maido kallonsa ga Daddy da ransa ke matuƙar ƙuna. Ya rasa mizai fassara Gwaggo da shi. Tun basu san kansu ba take ƙulla raba kansu, ALLAH gafurun kuma rahimun ya ganar dasu gaskiya hakan taƙi yuwuwa, amma bata barsun ba har saida haƙanta ya cimma ruwa. Sukazo babu dalili suka tsani ƴan uwansu da basu taɓa masu komaiba su da mahaifiyarsu sai alkairi, ALLAH ya ƙara taimakonsu suka gane suka canja.

Gashi yanzu tana son saka ƙiyayya kuma a tsakanin ƴaƴansu, wace irin fitinace wannan, kenan itama data haihu a gidan basu isa su jitu da nata ƴaƴanba……”
           Taɓashin da Abba yayne ya maidosa hankalinsa. Ya sauke numfashi a hankali da ɗago idanunsa irin na Shareff da sukai jajur yana kallon ɗan uwan nasa.

Cikin ɗacin murya yace, “Abubakar itace silar komai. Duk wata ƙiyayya tsakanin Umma da Mama itace taita haɗata. Bata barsu sun zauna lafiya ba muma ta hanamu gashi zata hana ƴaƴanmu ma. Yanzu ƴar ɗaya tilo da ALLAH ya bama Usman ma bazata barta tasha iskar farin ciki a cikin namu ƴaƴan ba. Kana ganin Maryamu ta daina zuwa da ƴaƴanta ƙasar nan saboda Gwaggo. Haka kuma zamu cigaba da zuba idanu kenan Abubakar?!”.


      “Bazai yuwu ba yaya. Dolene a wannan karon mu ɗauki mataki. Yaya Halima tafi kowa bani haushi. Sam ta kasa fahimtar halin Gwaggo tamkar ita ɗin ba mace bace ba. A zatona da ake cewa mata sunfi kowa zuminci ita ya kamata ta fara farga da son ganin mun dunƙule abu ɗaya amma da ita ake makamin rusamu. Bazan ɓoye makaba ina tausayin Shareff akan wannan auren.

Bazasu barsa ya zauna lafiyaba dan itama yarinyar nan da kake gani shaiɗaniyar kantace Yaya”.
     Sosai zuciyar Daddy ke ƙara tafasa dan yasan duk gaskiya ɗan uwan nasa ya faɗa. Shi kansa yana tausayama Shareff dan yana cikin kwatankwacin irin halin da suke neman jefasane akan mommy. Tunda ya aureta Gwaggo ta hanasu su zauna lafiya saboda kawai tana taƙama ɗiyar ƴar uwartace……

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button