BAK’A CE Page 21 to 30

Kansa ya shiga shafawa ya bude bangarensa ya shige ,
Kamar koda yaushe, sansanyen kamshi ne ya taro shi, wannan fa ba.a wasa da shi,
Agogon hannunsa ya fara kuncewa yana kokarin karasawa cikin dakinsa na baci dan ya samu ya yi wanka,
Wardugu” ta yi kiran sunnansa tana mikewa ta nufo shi,
Tsayawa ya yi yana kallonta, domin yanzu ya dan saka mata haushinta da yake ji na ta tafi ta bar su wai ba zata hada numfashi da yar gidan Anna ba,
Karasowa ta yi ta shige jikinsa du da yanda yake tarewa,
Murya a kasalance ya ce” Walyn bari na yi wanka , aiki na yi jikina ba tsafta,
Kai ta girgiza ta kara shigewa jikinsa tana rungume shi sosai a jikinta ta ce” baka wari kuwa Wardugu, kamshin turarenka na nan,
A hankali ya raba jikinsa da nata ya ce” aa tsaya na yi wanka, na yi zufa sosai kin ji?
Ya karasa yana mai zaunar da ita saman tsareren bed dinsa mai ruwan zeba,
Bayi ya zarce ya samu ya shige kasan shower,
Ruwa mai sanyi ya sakarwa kansa a jikinsa dan yana son jin sanyi
A hankali ya lumshe idannuwansa yana jin sanyi mai dadi na ratsa shi,
Sai da ya gama ya yi wanka na kirki ya dauro alwallah ya fito daga bayin , zuwa wannan lokacin har karfe tara ta kusa cikewa,
Yana fitowa , Walyn ta kara nufo shi
Tsayawa ya yi yana kallon yannayinta, magana ke tafe da ita domin batai masa yannayin tana bukatarsa ba,
Dan haka ya zarce ya dauko jalabiyarsa ya saka ya dauko salaya ya shinfida yana kokarin tayar da sallah,
Wardugu mana! Ta fada da yannayin damuwa,
Juyowa ya yi yana kallonta bai amsa ba,..
Ta karaso ta ce” su Mamanmu ne fa ke zaune a falona ka fito ku gaisa ,.
Wardugu yana kallonta, mamansu, har wannan lokacin?
Bai bata amsa ba ya tayar da sallarsa, dama dan ya yi shafa.i da wutiri ne,
Zama ta yi har ya karasa, ya zauna ya yi doguwar adu.o.insa na tsari da komai ya mike ya cire rigar daga shi sai gajeran wando ya yi bismillah ya haye bed,
Da mamaki take kallonsa, ranta ne ya baci ta ce” aman baka ji wace nace maka tana jira ba?,
Domin ta sani ne, yana mugun daraja mahaifiyarya, ko gaisar da ita zai yi sai ya dan duka, aman yanzu ta fada masa ta ga ya wani kwonta abinsa,
Wardugu ta kara kiransa tun karfi,
A fusace ya dago zaune , murya a bace ya ce” ba zan je na gaisar da mamanki ba, na gaji baci nake son yi ki fice mani a daki!
Ido ta kwalalo tana kallonsa, kafin take juyawa ranta in yayi dubu a bace yake, tana son tsayawa ta ja maganar aman wani abin na hanata, dan kuwa dukan alamu sun nuna idan ta yarda ta kawo masa raini komai na iya faruwa ,
Juyawa ta yi tamkar zata tashi sama ta fita a dakin,
Karamar wayarsa ya bude,
Sheik ibrahim ya danawa kira,
An jima tana ringin kafin yake dagawa da salama,
Wardugu ya gaisar da shi da tambayarsa jama.a,
Sheik ya amsa yana mai tambayar Wardugu Aiki,
Wardugu ya amsa shi a nitse ya ce” Malan, a kara saka mu a adu.a,
Sheik ya yi murmushi ya ce” Wardugu , na ganka a tv, fatan Allah ya tayaka, Allah ya baka ikon yin aikin kirki, sai dai zan kara fada maka, a duniya karka ce sai ka birge kowa, ka yi lamarinka domin Allah, kar ka saka fushi ko gaba dan Allah ya baka dama mai girma ta jan wanda ka yi niya, ka ci gaba da kawar da kanka a kwadayi , sannan ka ci gaba da jan istighfari kana kaiwa allah kukanka ka ji?
Wardugu ya amsa a mutunce sukai salama,
A hankali ya lalubo cazbaharsa fara kar tana ta kanshin turaren ruwa ya shiga ja daga kwoncen yana ta jan astghfari,
Me mijinki ke takama da shi a duniya Walyn? Ya rasa wa zai rufe sai aban iman? Ko dan yana auren yar yayata ai sai ya daga masa kafa, dan kawai ya kama da shi a wannan wajen, wajen ba na ubansa bane? Zance wajen sunnansa ma gare shi! Me yake tunani? Dan yana sanye da rigar iko shikennan ? Ai idan shine yau gobe ba shi bane zai ringa yiwa mutane rashin mutunci! Tunda haka ta faru muke gidannan aman ya zo ki wani zo ki ce wai ya gaji? Gajiyar kaniyarsa, mu da muke nan bamu gajin bane? To idan mijina ya kwana a cel nima na dauki alkawain sai na tozarta Wardugu sai na saka wardugu ya shiga uku, sai na
Aunty! Walyn ta fada tana daga murya sosai,
Da yatsarta daya ta ce” ke a wa? Wacece ke? Kike ikirarin tozarta Wardugu bayan Allah ya rike? Ke kin san da za.a shige shi da an shige shi ba yau ba Aunty! Wardugu baya zuwa maula, hukunci kuwa idan ya kama zai yiwa ko wani dan buro……..ba, meye? Takamarki ki yi masa shari, ki hada shi da malame, ko ki same shi ta hanyar abin duniya?
Ban ce sihiri ba zai kama shi ba domin wanene shi, sai dai na miki alkwarin tunda kika fadi haka , sai dai mu mutu baki daya,!
Mahaifiyarta ce ta kasheta da mari, rai bace ta ce” kan namiji? Kan namiji zaki ciwa kanwata mutunci? Namijin ne ya kai dan goyo har haka? Ke Wardugun da kafin aurenku ma sai da ya karya maki hannu sau biyu shine kike daga jijiyoyin wuya dan ance za.a taba lafiarsa? Kin manta dan ya kauce ki malaki wannan daula na yarda yake tata maki rashin mutunci? Idan kin canza ra.ayi na sani da wuri dan Ubanki!
Wakyn dake yashe tun marin magaifiyarta, jikinta a mace, takan mance du wani kudirinsu idan tana tsaye gaban gwarzonta, namiji ne Wardugu, can dama tana sonsa sosai, damuwar kuna tana son kudi sosai!
Mu.azam, tashi ka kai ni ya sha maganin bakin nan ,
Ayya ta fada tana nuno masa wani dan kuli wai maganin baki ne dan kar baki ya fada masa
Mu.azam dake zaune kafa tankwashe Agaishat na koyar da shi bakara ya dago da mamaki yana kallo Ayya,
A hankali ya ce” Ayya, idan muka yarda muka fita a yau fa kama mu za.a yi a rufe, sai karfe takwas na safe za.a tsayar da kamen nan, ki rufa mana asiri Ayya kin j?
Ayya ta zaro ido ta ce” dan ubansa a rufe mun, bafa zai yi baci ba sai ya sha maganin bakin nan yau yanzu yanzu dan haka tashi mu je Mu.azam,
Mu.azam ya mike yana ayyana ta faru ta kare a ransa, dan ya san in dai suka fita titi za.a kama su ne, za.a rufe su, daga shi har Ayya har Agaishat din,
………..to fah????????????????????✌????
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣7️⃣
Mu.azam ya ce” Ayya, ki bani na je na kai masa, kin ga ko an kama ni kadai ne za.a kama,
Ayya ta ce” yo kai na d’a bane, a hada har mu a rufe, ba yace doka ta hau kowa ba? Na tabata an hada da iyayen mutane a wajen,
Mu.azam kam ya rasa ya zai yi da Ayya , ta kuwa coge kofar daki inda Agaishat ma ta fito tace ba zai yiwu Ayya ta tafi ta barta ba,
Kallon agaishat yake kasa kasa, a hankali ya ce” idan aka rufe ki Agaishana, ba zan iya hakura ba, kar ki biyo mu na roke ki,
Irin na yara ta yi masa da kafadarta irin ta kiya, tama rigayi kowa karasawa wajen motar bayan ta amshi maganin bakin na hannun Ayya,
Haka Mu.azam ya fitar da motar dake da lambar Wardugu, ya dauko carte dinsa ta shaidar shi likita ne, da carte didentité dinsa,
Fitowa ya yi da motar Ayya ta shige baya ta hakimce, Agaishat ta shiga gaba aman a ranta a tsorace take, tana tsoron sojojin garinnan, daman ba.a saka soja a lamari a niger sai abin ya baci, su fa ba ruwansu hade kowa suke, idan ka yi masu gardama su tataka banza su barka nan zubde tamkar kayan wanki,