BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 21 to 30

Yana kokarin kara magiya Marahut ya shigo inda sojan nan ya biyo bayansa yana dan kame kame ya rasa me zai yi, su dai ba wanda bai san oga Marahut mahaifin uban gidansu ba, shi ya isa ya masa iyaka ne? Tun daga babar kofa ya samu shigowa ya ratso du zone na control ba.a hana shi ba sai shi tal dake tsaye dan kula da bude kofa da kuma rufewa da kyau ne zai hana shi shigowa?

Kallon Lawali Marahut ya yi kafin yake girgiza kai yana murmushi daga cikin rawaninsa,,

 Kai sade Lawali ya fice domin ya ji kunyarsa ainun

Marahut ya bi tsararen tankamemen office dan nasa, bMarahut ya ce” ya aka yi ka canza kanshin turarenmu ne Wardugu? Kuma ya aka yi ba hotona a office dinka bayan kai din dan halal ne koda shege ai ado yake da ubansa bale dan halal ,

Wardugu dake ta cika takardu yana dan dana laptop bai ce da shi ci kanka ba,

Marahut ya ce” Warsugu Abanka ne fa ni ? In ba ruwanka da mutane su ga kana min haka ba ruwanka da Allah ne??

Wardugu ya ajiye biron dake hannunsa ya dan shafa kansa ya dago da kallonsa wajen mahaifinsa wanda a kamaninsu haske ne kadan ya dan fi shi domin farin wardugu ba irin cancan din nan bane, 

Warsugu ya ce” Aban Wardugu ra.ayi ne ya sa na daina anfani da turaren da ka sanni da shi, sannan ni ba mace bane da zan kawo hotonka office na buga, kuma shegema mutun ne! 

Murmushi marahut ya yi ya karasa wajen kujera ya zauna ya ce” to ka fido mani matata mu tafi gida Wardugu,

Wardugu ya yi murmushi a bayane shima ya ce” ba zan so shakar iskar da kuke shaka ba ko na second daya, sai dai ya zama dole ne, matarka mai laifi ce

Meye laifinta wardugu? Me ta yi da tsanani haka? Ka san yara da kin ji suke,aman ai koma me ta yi ina gannin sai mu kashe mu birne abinmu a tsakaninmu ko wardugu? Marahut ya fada yana dubansa

Wardugu ya ce” zan so haka, sai dai ka ga rashin jin nata ne ya yi kamari, tana shigo da kwaya ne tana siyarwa wannan ba boyayiyar shaida bace, abinda nake bincike kawai na samu hanyar da take shigo da ita ko wanda ke bata sai na mika su kotu koda kuwa *kai ne*, sai dai ban san ba yin hakan ko Allah zai kama ni da shi?

Da sauri marahut ya ce” Quoi? (What?), wani irin kwaya? A Wardugu place din? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, wardugu ka kara mani haske a lamarin nan

Wardugu da ya ji ya dan samu sasauci, domin a sama yake, jininsa a saman akaifa, tsoro yake kar a je rinjayar nata ya kai ta saka Marahut a wannan harka? Aman yanzu ko ba komai ya ji dan sanyi a ransa dan kuwa har gobe da sunnan mahaifinsa yake anfani,

Wardugu ka fada mani mana, Marahut ya fada yana dubansa da yannayin serius

Wardugu ya yi umarnin a kawo AISATA,

Shigo da ita aka yi, dare daya tak du ta fara fita hayacinta abinka da wada ya saba da hutu,

Tana gannin Marahut ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi kafin da sauri ta nufi wajensa ta saki kukan kirsa,

Tana kukan ta ce” ka ga abinda Wardugu ya yi mini? Wannan wani irin tsana da cin mutunci ne? A gaban jama.a ya saka mini anker tamkar wada na yi sata, ai a tunanina ya dace komai ya fice tsakaninmu ko me na yi sai ya hukunta ni a gida ba wai a gaban duban mutanen da zasu yi min dariya ba,

Hannunsa ya saka ya dagota daga jikinsa yana dubanta, kadara, Aisata kadara ce mai wutsiya, a dalilin Aisata ya rabu da farin cikinsa da girmansa a idannuwan iyalinsa, maciya ce Aisata, Aisata zinari ce,

A nitse ya ce” me da me kuke aikatawa a Wardugu place?

Aisata ta yi tsam kafin ta shiga cicira ido ta kali dan ta kali uban, cikin yannayin barikinta ta ce” me muke yi kuwa banda neman kudi? A wardugu place ba abinda muke yi,

Wardugu dake rubutu a takarda ya dan yi tsam ya dago ya dube su ya maida kansa ya ci gaba da aiki,

Bai jima ba ya daga wayar office din ya danna kira,

Cikin girmamawa ya gaisar da jujun kafin yake fadin” mai girma na gama nawa binciken, yanzu ana kawo maka takardu ka duba, daga nan na mika maka su kawai ,

Amsa shi ya yi kafin yake kashewa,

Marahut da ya gama fahimtar wayar da Wardugu ya yi shima yana dubansa, cikin yannayin nutsuwarsa dai ya ce” har yanzu baka daina jin haushina kan Aisata ba?

Wardugu ya juyo da sauri, ido ya zazaro baki daya kafin yake mikewa ya tofar da yawu a nan cikin office din ya ce” kan wannan? Ya fada yana nuna aisata, 

Ya girgiza kai ya ce” ai koda me daraja ce bata kai na yi anfani da damata dan wulakanta ku ba, ka gane laifi ta yi, idanma baka yarda ba ai kai din oga ne kawai ka je wajen wa.inda zan mikawa takarda idan sun baka matarka ruwansu ni dai ai na tono barnar ko? Ka fi kowa sannin waye wardugu domin kaine mutun na farko da ka rikeni a duniya bayan likitar da ta fitar da ni daga cikin mahaifiyata! 

Yana gama fada ya ja kys din motarsa ya dauki gilashinsa ya fice a office din yana mai jin haushin yanda mutane ke magiya kan a bari a ci gaba da yada barna! 

Jikin Ayya ne ya yi sanyi bayan korar Agaishat da ta yi, a hankali ta mike ta nufi dakinta tana mai jin wani iri me ya yi zafi harda laifin wani zai shafi wani?

Tana zuwa ta shiga da salama,

Agaishat dake zaune kasa ta dora kanta a gefen gado tana jan carbi da hannunta ta dago da sauri tana kokarin mikewa tana duban Ayya,

Karasawa Ayya ta yi ta riketa ta zaunar da ita gefen gado,

         A nitse ta ce” ki yi hakuri yar gidan Ayya, ba zan kuma yi maki irin haka ba ,

Agaishat ta sauke ajiyar zuciya tana dubanta,

Ayya ta ce” bara na baki labarin mu….. na fada maki wacece *AYYA?*, na fada maki waye *MARAHUT a rayiwar Ayya?*, na fada maki wanene *WARDUGU* sannan wani irin girman daraja yake da shi a rayuwar Marahut da Ayya? Yarinta bara na baki labarin da ba kowa ya sani ba…………….

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        3️⃣2️⃣

                labarin Wardugu da tushensa a gajarce

.

…….. ………………

Sunana *Zanaba SHAU*, sunnan Mahaifin Wardugu *MARAHUT ELUM*, ni marainiya ce gaba da baya, na taso a hannun kakata ta wajen uwa da ta yi min saura,

Marahut dan gata ne gaba da baya, ya kasance a lokacin anguwarmu daya domin gida uku kawai ke tsakaninmu,

Tun wayona bai gama fahimtar Marahut na sona ba har na gane domin kiri kiri idan na yarda wani lokacin na yi dan shirin atampa na yafa mayafi na fito zai rufe ido ya kora ni yana masifa,

A anguwa ana girmama kakata domin mace ce da ta san girmanta, ba abinda ya shafeta da abin hannunka, ga mutunci ga zumunci,…du juma.a zaki ga an kawowa kakata abinci daga gidajen anguwar nan ciki kuwa harda gidan su Marahut inda mahaifiyarsa shuwa arab ke turowa kakata da gurasa ta kasa, irin wace ake yi a kasa ta ainahin da miya mai dadi harma ki ga an zuba tawa miyar mai magi domin a lokacin an hana kaka shan magi.

Sosai muke soyaya da Marahut, duk da wani lokacin nakan zauna na yi shiru ina tunanin Marahut na so na kamar yanda nake son sa kuwa?

Hakan sai ya tayar min da hankali sosai domin Marahut dai jarumin namiji ne mai cike da abubuwan da mata ke marari har suna kai wawa, harma wani lokaci na kwatanta masa….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button