BAKAR INUWA 22
Typing📲
Episode 22
………..Ganin taƙi cin komai Anne ta kira sunanta. Ta ɗago domin amsawa taci karo da wata wulaƙantacciyar harara data saka zuciyarta da hanjin cikinta tsargawa da ga gimbiya Su’adah. Saurin maida kanta tai tana amsawa Anne da rawar murya. Babu wanda ya lura da hararar sai Pa da Hajiya Shuwa. Dan haka Pa shima yay ɗan gyaran murya da sakin murmushi yana faɗin, “Ɗiyata ki saki jiki kici abinci kinji, munan family nakine na biyu insha ALLAH. Dan haka kar kiji komai kici duk abinda kike buƙata, kema mai baiwa wanine”.
Kai Raudha ta jinjina. Muryarta a risine ta ce, “To Abba nagode”.
Kiran da Ramadhan yayma Bilkisu ya hana kowa sake magana, ta miƙe tana amsa masa. Babu jimawa ta dawo ta fara zuba kunun gyaɗa a kofi. Anne ce tace mizatai da shi.
Cikin ɗan tura baki tace, “Yayane yace na haɗa masa nakai masa can”.
“Kunun kawai?”.
“Eh Anne shi kaɗai yace”.
“Bazai yuwu ba haɗa masa abinci, ni bansan mike damunsa ba yanzu bai son cin abinci duk ƙaunar dake tsakaninsu ada, yanzu babu ita.”
Bappi da tun ɗazun baice komaiba ya ɗan kalli can cikin falon inda Ramadhan yake yana faɗin, “Wannan hayaniyarce kawai ba wani abu ba, bara kiga ya samu nutsuwa zai koma cin kayansa.”
“Hakane”
Anne ta faɗa cikin tausayawa.
Raudha kam duk abinda ake tanaji kamar kowa, sai dai tana tsakurar abincinne da satar kallon yanda aka loda masa uwar madara a cikin kunun da bai gaza rabin kofi ba. A ranta take gulmar kunu zai sha ko madara?. Bata da mai bata amsa dan haka ta haɗiye gulmarta a ciki.
Koda Bilkisu takai masa kunun kawai ya ɗauka da farfesun kan rago, sauran kuwa ta dawo dasu. Adalilin dawo da kayanne take jin Yafendo na faɗin, “Ai kunga dai bazai cin ba, amma ya ɗauka masoyinsa Nama da madara, dan wancan kunu dai madarace kawai ba kunu ba”.
Dariya suka sanya, yaran nayi ƙasa-ƙasa. Anne tace, “Ai Ramadhan da nama sai kace wani kure, shi dai yaci nama. Bansan irin wannan ƙauna ba. Ko rai aka ɓata masa baya ƙin cin nama saboda son shi da yakeyi”.
Nan ma dariyar suka ɗanyi, ita dai Raudha nata murmushi ne kawai.
★★★
Da zasu koma batare da shi da Pa da Bappi ba, su sun wuce cikin masarauta ne, su kuma direct airport. Hakan ya saka Raudha jin daɗin komawar, dan sai ita kaɗai a vip ɗin. Sai dai tanata kallon tarkacensa daya bari a wajen da shaƙar ƙamshinsa tamkar yana nan, ta sake rimtse agogonsa dake cikin hannunta wanda da zasu fito daga falo a Taura Anne ta lura da shi ya manta a inda ya zauna, shine ta sata ta dakkosa. Koda ta ɗakko ta bama Anne cewa tai ta ajiye a wajenta ta bashi da kanta. Wannan shine dalilin tahowa da agogon har cikin jirgi tunda bata gansaba har suka baro Taura, yanzu kuma sai take ganin kamar bai dace ta ajiye anan ba gara ta bari ta bashi hannu da hannu. Sai dai kuma a ina? Yaushe kuma?. shine ke mata kaikawo a zuciya har jirginsu ya iso Bingo city batare da ta yanke kwakwarar shawara ba. Daga ƙarshe ma sai ta turashi cikin bag ɗinta batare da tasan dalilin yin hakan ba..
Koda suka sauka Anne sawa tai a maidata gida direct. Tai godiya batare data iya kallon kowa ba. har mota su Fadila suka mata rakkiya da nacin ta basu number ɗinta. Fuskarta ɗauke da murmushi tace musu itafa bata da waya.
A tare suka waro idanu waje. Rumaisa tace, “Kamarki matar Yaya guda baki da waya? To miyasa? Dami kuke gaisawa da Yaya kuma?”.
Cikin son kauda musu zargi tace, “Dokar Abbanmu ne sai kayi aure zaka riƙe waya”.
“Woow imagine! Dama akwai masu biyayya irinku har yanzu game da waya?”.
Basma ta faɗa da mamaki, dan su tun suna jss 1 ma sunada wayoyi, koda Ramadhan ya ƙwace a wancan lokacin basu ƙulla wata gudaba iyayensu mata suka saya musu wasu sukace su dinga ɓoyewa kar Ramadhan ɗin ya gani. Kuma haka akai har suka shiga ss 1 bai san sunada waya ba. Sai da ya saya da kansa ya basu.
Murmushi kawai Raudha tayi, yayinda Rufaidah ke faɗin, “Ai yanzu an saka miki ranar aure ya kamata Abba ya barki ki riƙe, zan faɗama Yaya kuwa”.
Kafin Raudha tayi magana har sun ɗaga mata hannu sun bar wajen saboda kiran da Sumayya ta ƙwala musu.
Alhmdllhi an kammala zaɓen shugaban ƙasa, duk da dai a wasu sassa an samu ƙananun hatsaniya na matasa da kuma sace akwatin zaɓe. Sai dai Alhmdllh abun bai tsamari ba jami’an tsaro suka tsawatar. Zuwa yanzu babban fatan kowa shine hayewar wanda ya zaɓa. Inda wasu ko barcin kirki basayi musamman ga ƴan takarar idonsu kyam a tv, wasu kuma a redio ana sauraren sakamakon zaɓuƙan jihohi.
Sai dai abin zai baka mamaki idan nace ga Ramadhan ba haka bane, dan shi tamkar ma an basa lokacin samun damar yin barci ne. Ko sau ɗaya bai taɓa zama kallon sakamakon zaɓe ba balle damuwa da yaya komai ke tafiya. Lokaci-lokaci dai yakanji ihun yaran gidansu na faɗin Yayanmu ya haye jihar kaza. Daga haka bazai iya ƙaras da komaiba kuma.
A randa ake tsumayen jin sakamakon zaɓen kuwa ƙasar tayi tsitt kowa ya kasa kunne, inda masu shirin kota kwana ke shirye tsaf na tada tarzoma ta kowanne sashe. Dan dayawan sauran ƴan takarar sunfa fahimci wanda zai iya kai labari kai tsaye. Dan haka suka shirya sai dai kowa ya rasa. A sashen su Alhaji Yaro glass duk da sunga alamun nasararsu hakan bai hanasu shirya nasu ƴan tada zaune tsayen ba suma, dan a cewarsu ko da zata kwaɓe sun shirya.
To suma dai jami’an tsaro sun shirya tsaf dan bada kariya ga al’umma kamar yanda Ramadhan yasa Bappi kiran I.G da General da sauran manyan shugabannin hukumomin tsaron ya nema alfarmar su tsaya da ƙarfinsu wajen ganin wani harmutsu bai tashiba dan ALLAH…
★A ranar talata ƙarfe huɗu da mintuna talatin da bakwai na yamma shugaban zaɓe prof. Rabilu S Barde ya sanar da sakamakon zaɓe ga wanda ya lashe kujerar shugaban ƙasar NAYA.
Sabon shugaban ƙasa da komai nasa yazo da mamaki da sabon sauyi. Matashi na matasa, Barr Ramadhan B. Hameed Taura.
A hankali kofin fura dake hanun Ramadhan da fitowarsa kenan daga kitchen ɗin Anne yaje ya ɗebo furan dan yasha saboda barci daya tashi a makare yay sallar la’asar a ɗaki ya sulale ƙasa ya tarwatse saman Mable’s ɗin da aka ƙawata falon da shi. Babu zato babu tsammani jikinsa ya kama rawa, dan harga ALLAH sakamakon zaɓen yazo masa a bazata, bai taɓa saka ran zaici ba dan yasan akwai manya a gabansa, duk da shike da ɗaurin gindin masu mulkin ƙasar da manya. Wasu irin hawayene masu ɗumi suka silalo masa a saman kumatu, ƙafafunsa da suka nema gaza ɗaukar gangar jikinsa sukai ƙasa ya durƙushe akan gwiwoyin sa biyu har ɓallin ƙofi na ji masa ciwo. Amma sai bai kulaba duk da zafin daya ratsasa sai ya tafi sujdah.
Anne da Bappi, Yafendo, Inna, Pa Siyama, Bilkisu ma dake falon duk Sujudan suka tafi kamar yanda yayi. Kafin su ɗago su bilkisu su cika falon da ihu saboda shigowar sauran ƴammatan gidan da gudu suna ihun murnar yaya ya haye.
Duk wannan ihu dake faruwa Ramadhan ya kasa ɗagowa daga sujida sai da Pa yazo da kansa ya kamashi ya ɗago da shi. Sai kawai ya fashe da kuka ya rungume Pa ɗin.
Pa dake murmushi shima idonsa cike da ƙwalla ya shiga shafa bayansa a hankali. Tsit falon yayi suna kallon yayan nasu, dan da yawansu zasu iya rantsuwar basu taɓa ganin kukansa ba kamar haka. Garama irinsu Mardiyya dake bimasa a yanzu kuma duk suna gidan aurensu.
Taɓa kafaɗarsa da Bappi yayi ya sakashi sakin Pa ya juyo ya rungume Bappin. Anne sai tazo dukansu ta rungumesu. Hakan yasa yaran gidan duka zuwa suka rungumesu su duka suma.