BAKAR INUWA 22
A É“angaren gimbiya Su’adah kam ai tsabar farin cikin ta zama uwar shugaban Æ™asa jitai tamkar ta ciji uwawunta. A take ta fara amsa wayoyin taya murna ga Æ´an uwa da abokan arziÆ™i. Yau sam babu É—aure fuska sai farin ciki.
A É“angaren Raudha ma shujuda tayi lokacin da aka sanar da Ramadhan matsayin wanda yay nasara. Batayi domin shiÉ—inne taso yaci ba dan dole. Tayine saboda fatan ace shine ahugaba na garin da suketa fatan samuwar mulki a hannunsa.
Su aunty Hannah kam gidan suka cika da ihu ita da ma’aikata. Ganin haka su Yasmin suka tayata suma. Farin cikinta uku ne a yau. A gobe za’a maida aurenta da Alhaji yaro glass kamar yanda sukai mata alÆ™awari. Na biyu zata zama matar vice president, na uku nan da shekar biyu itace matar president É—in.
A fadar shugaban ƙasa ma da duk wani dake tare dasu ransa fal farin ciki. Hakama jama'ar gari magoya bayan jam'iyya da Ramadhan. Dan tuni an fara bikin murna ta ko ina saboda jami'an tsaro sun taka rawar gani na hana kowacce irin fitina yin tasiri. Yaran su Alhaji Audi ƙaura duk wanda ya fito ram ake da shi. Ta ko'ina ka zaga kiɗe-kiɗe da bushe-buahe ke tashi a ƙasar NAYA birni da ƙauye.
A lokacin da wasu ke murna wasu kuka sukeyi, dan da gaske irinsu alhaji Audi Æ™aura Æ´an takara wasunsu suma suka dingayi sai da aka zuba musu ruwa. Yayinda magoya bayansu da iyalansu ke cikin tsantsar baÆ™in ciki. BaÆ™in cikinsu bai sake ninkuwa ba sai jin cewar Jami’an tsaro sun kafa sun tsare ko’ina domin hana kowacce irin tarzoma tashi. Idan ma tsautsayi ya fiddo mutum kamesa sukeyi.
★★-★★
Bazamuce hankali ya kwanta a ko’ina ba. Sai dai Alhmdllhi masu tada tarzomar basu sami yanda suke so ba. Jami’an tsaro ta kowanne fanni kuma sunyi Æ™oÆ™ari, sai dai ALLAH ya saka musu da alkairi. Shi kansa shugaban Æ™asa duk da akwai manufarsa ta É—ora Ramadhan akan mulkin yayi Æ™oÆ™ari sosai wajen jadadama jami’an tsaro harkar tsaron. Shine ya fara kiran Ramadhan ya tayasa murna. Sai kuma alhaji Yaro glass dake matsayin vice president a yanzu.
Alhaji Audi Æ™aura ne na huÉ—u bayan mai-martaba kakansa, saboda shawarar da god father É—insa ya bashi na kiran Ramadhan ya tayasa murna. dan shine babban abokin hammaya dake bi masa a Æ™uri’a, ido zai fi yawa a kansa fiye da sauran Æ´an takarar.
Hakan kuwa akai, ya kira Ramadhan ya tayasa murna. Ramadhan dake kwance a doguwar kujera ya ɗora kansa bisa cinyar Anne an lulluɓesa da bargo saboda sanyi da yace yanaji ya amsa masa cikin muryar dake nuna rauninsa a yanzun. Duk da halin da yake a ciki ya cigaba da amsa kiraye-kirayen waya har sallar magrib, koda aka idar ma bai huta ba. Dan duk da zazzaɓi daya rufesa har kusan sha biyun dare yana amsa wayoyin taya murna daga sassa daban daban na duniya.
Abokai, yan uwa. Da iyaye, Æ´an siyasa da shugabanin gargajiya. Wasuma bai sansu ba sai a yau.
Duk yanda Ramadhan dai yaso samun nutsuwa a ranar bata samu ba. Hasalima da zazzaɓi ya kwana da ciwon kai mai tsanani. Da safe har sai da doctor yazo ya duba shi. Duk da halin da yake ciki dole ya cigaba da amsa kiraye-kirayen taya murna a wannan yinin ma..
Kwanaki huɗu bayan faɗar sakamakon zaɓe ƙura ta lafa, sai shirye-shiryen zaɓen gwamnoni kuma da akeyi ta ko ina. Dan tsakaninsa dana shugaban ƙasa sati biyu ne. A kuma wannan tsakanin su Bappi suka sake zuwa Hutawa aka tsaida ranar ɗaurin auren Ramadhan da Raudha. Suka kuma ajiye komai har sadaki.
Mal. dauda baki har kunne ya zama surikin shugaban Æ™asa. Dama tunda ya dawo da Æ´an kuÉ—aÉ—ensa sai ya zaÉ“i dawa zaiyi magana yanzun. An bige gidansa ana sabon gini, gefe kuma yana neman aure batare da sanin su baba Nafi ba. Dan Larai anata hura hanci sune da gida yanzu, duk da ta shiga É—unbin baÆ™in cikin jin daga inda tushen kuÉ—in suka fito. Sai dai abinda malaminta ya faÉ—a mata game da watsa auren na Raudha da Ramadhan yasata shiga walwala ta maida komai ba komai ba. Yanzu sakamako kawai take jira na fasuwar auren a haukarta (😹😹).
_★__
SANNU-SANNU bata hana zuwa, a na gobe zaɓen gomnoni aka maida auren Alhaji yaro glass da aunty Hannah. Duk da ba wani taro sukaiba aure kawai aka ɗaura ƙawayen aunty Hannah sun ɗan haɗu a gidan, ciki kuwa harda first lady. Wadda a ranar kowa ya sake tabbatar da alaƙarta da Aunty Hannah ɗin. Su Asabe ma dai nan gidan sukazo suka kwana, hakan yasa Raudha da mominta samun damar keɓewa da ƴan uwanta. Kuka ta dinga rusa musu akan wlhy bata son auren nan dan mutanen nan sunfi ƙarfinta. Duk da wasu sun nuna soyayyarsu gareta wasu ƙuru-ƙuru a ƙannensa da wata babbar mace da take ƙyautata zaton mahaifiyarsa ce saboda kamanni da suke ɗanyi suka nuna mata tsana da gargaɗi. Nan dai duk ta basu labarin abinda ya faru ranar zaɓen shugaban ƙasa.
Hankalin Asabe ya tashi, ta shiga yima Raudha faɗa akan miyasa ta amsa a wancan karon, dama irin wannan take guje mata tun farko. Maba danginsa ba ko shi bata ƙyautata zaton zai so ta. Mutumin da tun yana ciki ake ajiye masa kuɗi a asusun banki, ya girma yasamu ingantaccen ilimi, babu kalar ƙasar da bai zagaba yaga mata ƙyawawa ƴaƴan manya irinsa, amma tai tunanin zai iya dubanta matsayin mace. Kawai dai kakansa ke son wannan haɗin saboda alkairin datai musu.
Lallashinta su Fatisa suka dingayi da bata baki harma da shawarwari, dan harga ALLAH suma suna son ƴar uwar tasu ta auri shugaban ƙasa. Koba komai zasu fantama matsayin yayyen matar shugaban ƙasa. Zasu huce gajiyar wahalar da sukasha a hutawa a baya.
Sosai Asabe ta kasa zaune ta kasa tsaye, ji take kamar ta gudu da ƴaƴanta daga Bingo. Dama tasan idon Gwaggo idan yaranta sai wanu abu ya biyo baya. Dama wannan taita fargaba tun farko. Tunanin inda zataje da su ne ya sakata sake shiga damuwa. Har aka ɗaura auren aunty Hannah bata da wata walwala. Kowa tunaninsa aunty Hannah zata tare ne acan gidan Alhaji yaro kamar auren farko, sai sukaji saɓanin haka wai anan zata cigaba da zama tukunna. Hankalin Asabe ya sake tashi, dan tasan kuma babu danar sace Raudha kenan.
A ranar dai ko leÆ™e ango bai leÆ™o gidan ba, washe gari akai zaÉ“en gwamnoni. Wannan karon babu inda Raudha taje, hasalima wuni tai murÆ™ususun ciwon mara har sai da suka dangane da asibiti. A asibitin ta kwana, washe gari suka dawo gida. Haka kwanakin suka cigaba da shuÉ—awa batare da Raudha ta ko sake jin labarin wani Ramadhan ba sai a tv kawai idan an ambaci sunansa ko an nunasa. Sannan Asabe ta kasa samo mafita game da auren na Raudha. Sai da auren aunty Hannah da Alhaji yaro ya cika wata guda cif suka fara ganinsa a gidan. Dan zuwa yanzu an kammala duk wasu zaÉ“uka sai jiran rantsarwa kuma. A ranar gyaran da ma’aikatan sukaima gidan ma na musamman ne, bai isoba kuma sai wajen tara na dare.
Raudha ta haɗo kan su Yasmin sukazo suka gaishesa. Baki ya saki da hanci yana kallon Raudha ɗin yana haɗiyar yawu. Dan harga ALLAH baisan haka yarinyar take ba. Bai taɓa ganinta ba sai a hoto, sai dai kuma a yanzu canji waje data samu ya sake fiddo mata da ƙyawunta da cikar budurci. Dan tana akan shekarunta ne na girma.
Harga ALLAH Raudha ta tsargu da kallon da tsohon ke mata, dan haka ta shiga ambaton sunayen ALLAH da jifansa da addu’oi. Tunda ta samu ta gudu É—aki kuwa bata sake leÆ™o waje ba harda safe. Tanaji Yasmin tazo tana tashinta wai tazo a karya inji sabon Abba tai mata banza. Dole ta koma tace barci take.
Har Alhaji Yaro yace Yasmin ta koma ta tasota Aunty Hannah ta hana cikin kissa. Acewarta a barta tai barcin batajin daÉ—i, kuma anjima sunada wani trianing akan Raudhan. Badan yasoba dole ya haÆ™ura, sai dai a ransa yana fatan ALLAH yasa kafin yabar gidan ta fito. Sai kuma akai rashin sa’a addu’arsa bata karÉ“u ba harya fitan batako leÆ™o waje ba………✍