Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 23

Typing📲

Episode 23

…………A ɓangaren Ramadhan kam yama manta da wani batun aurensa balle Raudha. Harkokin gabansa kawai yakeyi na shirye-shiryen rantsarwa da zaman meeting-meeting da suke yawanyi da ƴan jam’iyya a gidan gwamnati. Shi kansa ma haushi meeting ɗin ke basa a mafi yawan lokaci, dan wasu yakan rasa gane kansu balle inda suka dosa. Sai dai yana nutsuwa dai wajen maida kansa yaron da suke kallonsa yana karantar komai da nanufofinsu.
     Sai dai abinda Ramadhan bai sani ba a garesa ne kawai ya manta da abatun aure, ga jama’ar gidansu da masu so da masu ƙi duk abin na ransu. Domin shiri su Anne keyi na musamman akan auren, lefe ya kammala haɗuwa tsaf, hakama abubuwan da duk za’a buƙata ga taron biki.

          A ɓangaren su gimbiya Su’adah ma dai suna nan akan bakansu na hana tabbatar wannan aure, sai dai kuma tun randa Pa ya ritsata tana waya da Asma yaji kuma mi suke faɗa yaja mata dogon gargaɗi, tare da alwashin inhar wata matsala ta shigo a auren nan ta shirya amsar matsala a nata auren itama. Wannan ne ya tada mata hankali ya kuma ja mata birki, sai ta koma zungurin Ramadhan akan auren. Sai dai kuma rashin zamansa a gidan ya taimakesa da masifarta.
    A yanzun kullum cikin ƙulla yanda zasuci uban Raudha suke inhar ya tabbata sai anyi auren. Tare da ɗaukar alwashin aurama Ramadhan Aina’u koda daga baya ne.

     A hutawa ma dai Mal. Dauda ya shirya tsaf, dan gyara na haƙiƙa yayma gidansa tamkar bashi ba. Ya baza ɗinkuna yayma kuma kowa na gidan. A yanzu haka Innarsa da ƙaninsa da iyalinsa suma sun dawo nan gidan da zama. Hakan yasa Larai ta rasa kataɓus dan Inna cin uban surukai take babu ɗaga ƙafa. Balle ma yanzun da take ganin ɗanta yay arziƙi, ai koda wasa babu wanda ya isa zagin Asabe a gabanta duk da bata nan. Takance Asabe ai farar uwa ce tunda gashi sanadin ta haifi Raudha suna hutawa. Takanji takaicin saki ukun da ta saka Mal. Dauda yay ma Asabe a yanzun. Inama ɗaya ne ko biyu da yanzu sai ta dawo abinta.
        To anan ma dai shirinsu suke tsaf duk da babu amarya har anko an fitar ma.

       SATIN BIKI

  Shiga satin biki ya saka ango da amarya dawowa cikin hankalinsu. Dan kuwa sun tabbatar yanzu kam da gaske ake ƙwarai. Ta ko ina sanar da wannan ɗaurin aure ake a kafafen yaɗa labarai dana yanar gizo, yayinda wasu baƙi dake ƙasashen ƙetare suka fara sauka ciki harda su Sultana daba taron bikinne ya kawotaba kai tsaye. Dan tunda akace Ramadhan ya fito takarar shugabancin ƙasar NAYA take son zuwa, sai kuma ga batun aurensa da yay matuƙar tada hankalinta har takaita da kwanciya asibiti. Halin data shiga yasa Babanta yarda su Mufeed suzo da ita taga Ramadhan ɗin.
     Sai dai kuma tun jiya suka iso amma ganin Ramadhan yay musu wahala saboda yana can suna shirye-shiryen zancen rantsarwa. Za’a ɗaura auren ne juma’a, asabar ayi rantsuwa, lahadi su tare gidan gwamnati tilitin shugaban ƙasa ya fara shiga office.


     Ga amarya kam itama ta yarda dai auren nan babu fashi, tunda aka shiga satin bikin aka sake ninka yanayin gyaran jikinta da akeyi, tayi ƙoƙarin toshe duk wata hanya bata sake haɗuwa da Alhaji yaro glass ba duk da yana yawan zuwa gidan yanzun. Ana saura kwanaki biyu ɗaurin aure daren da washe gari za’a maidata Hutawa kusan sha biyu yunwa ta addabeta, dan duk yinin yau bataci wani abincin kirki ba saboda damuwa. Bata son auren nan ko ɗigo a ranta, gefe ga tsoro da fargabar tsantsar ƙiyayyarta data hanga a cikin idon Gimbiya Su’adah da wasu a ƙannen mijin nata. Jin har kamar zuciyarta na tashi dan yunwa ya sata fito da nufin zuwa kitchen ko tea ta haɗa.
     Da sauri taja birki jin kamar ana magana ƙasa-ƙasa dai-dai tana ƙoƙarin sanyo ƙafarta a falon, ta ɗan laɓe tana leƙe daga corridor ɗin ɗakunan barcinsu ita da su Yasmin. Aunty Hannah ta hango da wasu mutane uku, babu wanda ta gane a cikinau sai Alhaji Yaro glass kawai. shima dan rabin jikin aunty Hannah nakan nasane. Dan tana zaune kusan a jikinsa ne ko kunyar sauran mutanen bataji. amma sauran ukun babu wanda ta sani.
     Jin an ambaci sunanta yasa gabanta faɗuwa. taɗan sake matsowa daf da hanyar fita corridor ɗin ta kasa kunne taji da ƙyau.
      Wanda yake a kujerar ƙarshe mai sanye da jallabiya baƙa ya ƙara fuskantar aunty Hannah yana faɗin, “Hannah kinga dai mun matuƙar yarda da ke, dukkan wani shirinmu a yanzu tamkar ya rataya a wuyanki ne. Bama son kuskure ga yarinyar nan, dan idan aka samu kai tsaye ke zamu ɗaurama alhakin hakan”.
        Kanta ta jinjina masa tana tashi zaune sosai. “Alhaji Wada karkaji komai, na riga na ɗaura Raudha bisa kowacce irin hanya da bazata iya bijire mana ba. Ku ɗauka tamkar yaron nan ya mutu ya gama a shekara biyun da kuka ɗeba masa. Adai ɗaura auren jibi, da zarar sun tare za’a fara bata maganin tana saka masa a abinci, ko abin sha kamar yanda first lady ta sanar min..”
        “Hakan shine dai-dai, dan munaso ya fara masa aiki a hankali yanda ko bayan mutuwarsa za’a ɗauka diabetis ɗinsa ce ba wani ba, tunda dama maganin zai ƙara ƙarfin diabetis ɗinne ya kuma haifar da hawan jini mai ƙarfi. Sannan a yau da safe duk wani poison an sakashi a cikin ac ɗin falonsa da bedroom dan a hankali mukeso ya fara ratsa jininsa shima ta yanda zai zama bashi da wani kuzarin nutsuwa yay aikin ma, dan cikin idon yaron nan ka kalla kasan bazaiyi mutunci ba. Yana gama gane kan mulkin nan mukanmu ba ɗaga mana ƙafa zaiyiba wlhy.”
         Alhaji Yaro glass ya karɓe da faɗin, “Ai dama shegene yaron nan, yanda kaga kakansa da taurin kai haka shima yake. Ni gani nakema mizai hana ita Raudha mu fito mata ƙuru-ƙuru akan aikin da muke son tai mana kawai dan yarinyace sai yanda mukai da ita.”
      “A’a wannan ganganci ne, idan kuma aka samu akasi ya faɗa sonta fa? Ko kuma itama tana sonsa yanzu haka? Dan yaron nada qualitys ɗin da mata zasu so sa a ƙanƙanin lokaci. Giyar soyayya kuwa zata iya janta ta sanar masa. Kawai muyi yanda muka tsara ayi amfani da ita”.
          Cikin zafin rai Mr MM yace, “Idan ma mun sanar matan tace zata tona mana asiri halakata zamuyi itama a banza….”
      “Ai ko yanzu ɗin ba tsira zatai ba. Kana tunanin zata dinga shaƙar gubar nan ta cikin ac ta tsallake itama. Yanda zata dinga masa illa a hankali itama hakanne zata kasance. Sai dai akwai wata allura da za’ai mata wadda gubar bazata yi tasiri a jikinta da wuri ba kamar shi”.
       A tare duk suka kalli Aunty Hannah bayan sun ɗauke idonsu ga Dr Bonba daya gama bayanin.
     Kanta ta kaɗa musu tana watsa hannaye baya. “Miye na kallon nawa?, kun san dai Raudha ɗiyar ƙanwata ce. Duk da kuwa ina son zama first lady bashike nuna bana son abata ba. Nasan bai wuce kuce ya shawarar ta canja ba game da allurar riga kafin guba. Ku zauna kuyi tunani da hankalinku, babu ta yadda za’ai mu bari gubar tai tasiri a jikinsu lokaci guda, dan komai zai fito ne. Amma idan bayan ya shi ya mutu ne itama ta mutu za’a iya cewa zuciyartace ta buga saboda rashinsa itama tabisa”.
       “Woow!”.
Suka faɗa a tare suna tafawa. Shugaban ƙasa mai sauka yace, “Hannah kinada basira, anya kuwa idan mutumina ya zama shugaban ƙasa bake bazaki koma juya ƙasar ba kuwa?”.
        Wata shegiyar dariya tayi tana juya idanu, Alhaji Yaro glass ya sake rungumota jikinsa da manna mata kiss a kumatu. “Inaga shugaban ƙasa biyu kam zakuyi”. Ya faɗa cikin raha. A can ƙasan ransa kuwa yana ayyana ashe kuwa itama zata mutu nan kusa, dan Hannah bata isa shiga masa hanci bai fyatota ba duk da take matarsa………

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button