BAKAR INUWA 23
Zuwa yanzu sosai hajijiya ke neman yadda Raudha a ƙasa. Tai azamar dafe bango jin zata zube a ƙasa. Laɓɓanta sai faman rawa sukeyi amma sun gagara furta komai, dan ko tace zata furta ɗin batasan mi zata furta ba. Da ƙyar ta cigaba da laluben bango ta koma ɗakinta, batasan a yaya ta zube saman gadon ba harda jan bargo ta lulluɓe, jikinta ya shiga wani irin karkarwa na rawar sanyi
Yanzu ta fahimci ba ahalin Ramadhan bane zasu zama BAƘAR INUWAR ta ba, ba Ramadhan bane BAƘAR INUWAR ta ba, aunty Hannah itace BAƘAR INUWAR ta. Shi kansa Ramadhan sun tittiÉ—ashi ya hau kujerar mulki ne badan ya ni’imtu ba, badan ta zame masa INUWA da irinsu talakawa suke hangen masu mulki na ciki ba. bai san sun kaisa BAƘAR INUWA bane, gara ace a rana yake da shiga cikinta. ta sake fashewa da kuka.
ALLAH sarki talaka. A kullum gani yakeyi shi a RANA YAKE, mai mulki shike cikin Ni’imtacciyar inuwa, ashe baisan da wata BAƘAR INUWAR MUKIN gara ranar da shi yake a ciki ba. Yau gashi saboda mulki yayar mahaifiyarta ta É—auketa da hannunta ta kaita BAƘAR INUWA. Shiyyasa suka dage ashe, shiyyasa suka hana mahaifiyarta nuna Æ™in auren, shiyyasa suka babbake ko ina da ina. Miye mafita? Zata bijirema auren ne ta hanyar guduwa ko zata haÆ™ura ta zauna ta ceci rayuwar wanda a yanzu take kallo da fatan ya zama adalin shugaba madubin al’umma kamar yanda talakawa suka É—ora yaÆ™ininsu a kansa da Æ™warin gwiwarsu?.
A take kanta ya fara sarawa, dan tama rasa kalar tunanin da zatayi saboda Æ™arancin shekarunta. Ga wani irin tausayin Ramadhan É—in da ahalinsa na dirar mata a zuciyarta, dan ta taÉ“ajin cewar kakansa Baba alhaji aka bama takarar shi kuma ya bashi saboda yace bai ra’ayin mulki a shekarunsa. Ashe baisan ya kai jikansa BAƘAR INUWA bane. Tabbas bazata iya fahimtar komaiba a yanzu dole saita san komai, sanin komai kuma bazai yuwu a gareta ba sai ta yarda da auren Ramadhan. Sai dai kuma tana buÆ™atar shawara wajen na sama da ita, wazata tunkara? Hajiyar birini! (Kai a’a gwaggo sai a hankali ce) Hajiya mama (kai itama a’a duk tafiyar É—aya ce) Mommynsu! (Ina bazai yuwu ba zata sake tada mata hankali) Su Fatisa! (Ina basu da hankalin da zasu iya fahimtarta ta wani fanin ma gara ita). Take wani irin zazzaÉ“i mai zafi ya rufeta, sarawar da kanta keyi ya Æ™ara Æ™arfi..
Koda suka wayi gari da safe Raudha babu lafiya aunty Hannah bata kawo komai a ranta ba sai tunanin fargabar aure da akasan kowacce amarya da shi. Tunda sassafe suka nufi can gidan dan yau zasu wuce Hutawa su duka har Hajiyar birni. Su Fatisa kam tun jiya suka wuce harda su Yasmin.
Asabe ce kawai ta damu da ganin halin da É—iyar tata take ciki. Suko hankalinau nakan kuÉ—aÉ—en da aka aiko daga gidan su Ramadhan injisa aba amarya na hidimar biki, sai tarin kayan rabo. Ko irin É—an faÉ—a da nasihar da akema amarya babu wanda yay mata a dangin mahaifiyar tata. Sai ita Asaben ce ta jata gefe taita lallashinta da mata nasiha. Tare da Æ™arfafa mata gwiwar ta É—auka Ramadhan shine zaÉ“in ALLAH a gareta. Maybe shine kuma mafi alkairi. Dan ita kanta tayi addu’a tayi sadaka akan rushewar wannan aure amma babu alamar zai rushe É—in.
Raudha ta yarda da maganar Mommy takuma É—auki aniyar haÆ™uri, dan ita kanta tayi addu’ar sosai akan zaÉ“in ALLAH game da auren komai kuma bai canja ba, tunda gashi har gobe idan ALLAH ya kaimu É—aurin aure.
Ƙarfe kusan sha biyu suka bar Bingo zuwa jihar Dillo a ƙaramar jukumar hutawa. Kasancewar lafiyayyar motace kuma drivern yasan aikinsa zuwa huɗu na yamma sun iso. Asabe tayi mamakin yanda aka tarbesu, ga gidan nasu data sani duk ya cinye a baya ya zama wani haɗaɗɗe yanzun. Dan harda su gate aka saka.
Kowa burinsa yaga Raudha matar shugaban ƙasa. Dan haka maƙwafta da ƴan anguwa sukaita tururuwar shigowa ganin amarya. Sai dai kuma ita amarya Raudha ta ɓoyewa ganinsu saboda zazzaɓi dake damunta har yanzu. Abu biyu ke tayar mata hankali. Zancen su Aunty Hannah da tsarin auren nasu daya sha banban dana saura. Babu wani jituwa tsakaninka da ango balle wani maganar biki ma ya shiga. To gaba daya ma sau biyu ta taɓa ganinsa a zahiri, babu kuma wanda wata maganar kirki ta shiga tsakaninsu a ciki.
Duk yanda taso cigaba da zurfafa tunanin nata dole ta haƙura saboda hayaniya da gidan ya ɗauka. Kai kace yau ne ɗaurin aure. Ga dj ya warware kiɗa tun da safe dan su Fatisa suka ɗakkosa tun daga Bingo. Tun kuma a daren jiya aka fara raƙwashewa duk da amarya bata iso ba. Shiko Mal. Dauda dama babu ruwansa, dan shi kansa yana gefe da abokansa yana ɗan rausaya ƙafa saboda yanda kiɗan ke shigarsa tsumin baya na neman motsawa.
Kowa ka gani a cikin farin ciki yake a gidan, Æ´an uwa da wandama kalan dangine duk bakuna a washe. Musamman Inna dake nuna cewar yanzu tafi son su Raudha fiye da kowa a duniya. Larai ce kawai take cikin tashin hankali, dan ta koma gidan malaminta yafi sau shurun masaÆ™i yana cemata ta dai jira ai ba’a É—aura auren ba ko. Kowace daÆ™iÆ™a ta agogo dake matso da lokcin É—aurin auren na bugawane da bugun zuciyar larai. Duk ta fita hayyacinta tsabar rashin nutsuwar zuciya. A daren jiya har faÉ—a sukai da Mal. Dauda ya shashaheÆ™a mata mari da tabbatar mata idan ta É“ata masa farin ciki a taron bikin nan zai yanka mata jan ticket É—in komawa gidansu dan bazai zauna da mai masa baÆ™in ciki ba.
Wannan shine dalilin daya sakata kama kanta sai idan ta shiga É—aki taita haÉ—iyar zuciya. Baba nafi kam babu ruwanta. ta shige cikin dangin Asabe dana mijinta anata harkokin arziÆ™i da ita. Hakama Æ´aÆ´anta na ma’auri da wanda basuyi auren ba. Yanda take É—in yasa Mal. Dauda mata Æ™yautar kuÉ—i masu tsoka wai itama ta tarbi baÆ™inta.
A daren ranar duk yanda Raudha taso maÆ™alewa taÆ™i fita Æ™ofar gidan inda su Fatisa suka tara Æ™awayensu dama wanda ba’a gayyataba hakan bai yuwu ba. Acewarsu yaune sukai taronsu na Æ™awaye. Dole aunty Hannah ta matsa mata shiryawa cikin wata haÉ—aÉ—É—iyar doguwar rigar Material a cikin akwati guda da aka kawo mata na kayan fitar biki. dan ba’a kawo lefe ba Ramadhan ya hana. Yace idan an É—aura zai bata da hanunsa. Su Bappi sun goya masa baya dan auren Amnah ma haka yayi. Shiyyasa aka kawo mata kayan fitar biki kawai da aka É—inka akwati guda da duk abinda zata buÆ™ata na ado.
Light makeup Feena da suka taho tare saboda kwalliyar amarya tai mata, aka gyara mata dogon gashinta data gada wajen Asabe tare da naÉ—a mata É—auri mai Æ™yau. Kanta ke matuÆ™ar ciwo ga zafin zazzaÉ“i amma haka ta daure ta fitan. Nanfa Æ™awaye suka shiga mata hotuna duk da dare ne harma da jama’ar gari. Burin kowa ace ga hoton matar shugaban Æ™asa a wayarsa ya samu na fafar faÉ—ama wasu yanada alaÆ™a da ita koda anan gaba idan ganinta ya musu wahala. Wasu ko a take suka shiga watsashi a media dan hannayensu na Æ™aiÆ™ayi.
Wajen ya sake ƙawatuwane lokacin da Hajiyar birni tazo ta farke ƴan ɗari biyar-biyar ta hau yima Raudha liƙi. Sai itama aunty Hannah ta farke ƴan dubu-dubu. Sai ga Mal. Dauda ma da kansa ya farke nasa dubu-dubun. Nanfa yaran dj da mutane suka shiga wawaso. Abu kamar wasa sai ya zama gasa akaita shigowa anama Raudha liƙi. Wasu ma ƴar dubu ɗaya ce suke canzowa goma-goma ko biyar-biyar suyi dan dai ace suma sunyi.
Alhmdllhi dai sai ga taron ya zama wani Æ´ar Æ™warya-Æ™waryar wasa. Amarya ce kawai zuciyarta ke a Æ™untace da damuwar data dameta. Suna mata kallon wadda zata shiga Ni’imtacciyar INUWA basu san BAƘAR INUWA bace, gara ranar da suke ciki ta fita kwanciyar hankali.
Jirin da tace tanaji yasa Hajiya mama maidata cikin gida, aka bata tea da magani tasha ta kwanta. Kasancewar maganin naÉ—an saka barci aka dace barcin yay awon gaba da ita dan dama akwai bashinsa a kanta.