Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 23

WASHE GARI

         Tunda farar safiya motocin jami’an tsaro kala-kala suka fara shigowa garin Hutawa suna masa zobe. Al’amarin tuni ya fara tsorata masu tsoro suka nutsu a gidajensu. Zuwa Æ™arfe sha biyu garin ya fara É—aukar haramar baÆ™i. Babu abinda ke danno kai cikin garin sai jibga-jibgan motoci da suka Æ™oshi. Kai harda su helicopters. Tuni gidan hakimi daya amshi É—aurin auren ya cika ya tun batsa da manyan Æ™asa dana baÆ™in Æ™etare. Dan babu kalar fatar da bazaka samu ba. Tunkan shugabanci gidansu Ramadhan babban gidane sannne, sai ya zam samun mulkin ya sake haskesu.
       Ƙarfe sha biyu da rabi dai-dai tawagar shugabn Æ™asa kuma ango Ramadhan B. Hameed Taura ta dira cikin garin hutawa. Dan tun a daren jiya nasa baÆ™in ta kowanne É“angare ke danna kai birnin Bingo, yau kuma suka É—ungumo a motoci zuwa Hutawa, duk da kuwa su Alhaji yaro glass sun so hanashi ya tabbatar musu bazaibi jirgi ba zaizo a mota saboda wani dalilinsa.
     Ta ko’ina garin ya sake harmutsewa. yayinda wasu a abokan nasa ke matuÆ™ar mamakin inda Ramadhan É—in ya Æ™waÆ™ulo matar aure a wannan garin da idan ka É—auke É—ai-É—aikun manyan gidaje da lafiyayyen titi babu komai a cikinsa sai hayaniya da tarkacen talakawa (🙄🤗ALLAH mun gode maka daka yimu a talakawa)………✍

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button