Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 52

idanun nan”. Ya faɗa da sauri ganin tana niyyar lumshesu kuwa. Yanda taji babu wasa a furucinsa ya sata dakatawa. Sai dai taƙi yarda su haɗa ido….
      “Ni bana son irin wannan gaisuwar ga matata shiyyasa ban taɓa amsa miki ba”.
     Duk yanda taso jurewa kasawa tai, sai da ta ɗago ido ta kallesa sai karaf a cikin nashi da launinsu ya canja. Ƙwayoyin cikinsu bakaƙe masu ƙyalli ya

juya mata cike da tabbatarwa. Ta risinar da nata tsigar jikinta na tashi dan ta rasa abin cewa kuma. Zuciyarta na tunanin (Banda gulma irin tashi wace

gaisuwace kuma bayan wannan da aka banbanta tsakanin mata da miji da sauran mutane? Ita dai tunda ta taso a gidansu irin wannan taga anama Abbansu).
      A bazata kawai taji saukar lips ɗinsa saman goshinta. Kafin ta dire numfashi ya saukesu kan lips nata ya bata light k.. Harya janye kuma ya sake

maidawa ya cafkesu da ƙyau yana matse hanunta dake cikin nashi tsam.
       A gwame ta dinga fidda numfashi kamar yanda nashi ke fita a harɗe, har saida yayi yanda yake so sannan ya barta dan kansa. Cikin rufewar idanu ya

lalubi kunenta.
     “Wannan itace nake buƙata a kowacce safiya idan mun tashi, da kuma idan na dawo aiki shine sannu da zuwana”.
      (Tabb ashe kuwa akwai tsallen baɗake) cewar Raudha a zuciya. A fili kam yanda yay maganar babu wasa a ciki ya sakata jinjina masa kanta kawai batare

da tace komai ba. Mikewa yay shima ya mikar da ita batare da ya sake cewa komaiba. Dolenta tabi yanda yakeso suka koma gado bayan ya cire mata hijjab ɗin ya

barta da abayarta dan shima yana son kauda kansa ga abinda zuciyarsa ke bijiro masa.
      Fargaba ta hanata barci har sai da taji yana sauke numfashi a hankali alamar shi ya fara sannan tai nata itama tunda taga ba abinda take tsoron bane

zai faru……….✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button