Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 57

Episode 57*

……….“Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un aunty Raudha jini kuma?”. Bilkisu data shigo ɗakin a birkice ta faɗa tana ƙarawo gareta. Kamata tai suka nufi

toilet, ta haɗa ruwa mai ɗumi ta taimaka mata ta wanke fuskar da hanunta, jinin dai bai tsaya ba. Sai dai sun tare da tissue. A bakin gado ta zaunar da ita,

ta ɗakko first aid box ta shiga ƙoƙarin tsaida jinin, da ƙyar aka rufe wajen da audiga da bange. Ita dai Raudha babu abinda take sai sakin ajiyar zuciya.
      “Aunty Raudha wai garin yaya? Ina Yaya kuma?”.
   Komai Raudha kasa cemata tai, sai hawaye take sharewa kawai. Hankalin bilkisu ya ƙara tashi, sai dai ta barta bata sake maganaba. Tana niyar mikewa ta

maida first aid box ɗin ma’ajiyarsa ta lura da kumbirin hanun Raudha kuma. Gaba ɗaya saita sake ruɗewa ta kamo hanun tana kallo. “Ya ALLAHU, nan ma ai ciwon

kikaji Aunty! Kinga bara na kira Yaya da mama ladi dan ta iya gyaran ƙashi”.
       Ita dai Raudha komai batace ba, babu jimawa suka dawo da mama ladi, bilkisu ta sake fita. Duk da ta fahimci akwai matsala ƙofar Ramadhan ta dingama

knocking a ɗarare. Shiru babu ko motsi, sai ta ɗan tura ƙofar ta leƙa. Gabanta ne yay masifar faɗuwa hango Yayan nasu zaune akan tum-tum ya dafe kansa. Babu

shiri ta shigo ɗakin da sassarfa. Muryarta har rawa yake ta durƙusa gabansa “Yayanmu dan ALLAH mike faruwa ne? Aunty Raudha taji ciwo sosai wlhy har a

hanunta mi’akai mata”.
        Da ƙyar ya samu damar fisgo kalmar innalillahi… A cikin zuciya. Ya ɗago jajayen idanunsa ya zuba kan Bilkisu datai matuƙar razana. Dan rabon da su

gansa a irin wannan yanayin tun rasuwar su Haseenah. Baya taɗan ja jikinta na rawa. Shima sai ya cije lips sinsa da ɗago hanunsa ya kalla. Sai kuma ya dafe

kansa dake matuƙar juya masa. Kusan minti ɗaya ya sake ɗagowa ya dubi Bilkisu da gaba ɗaya ta gama tsorata. Cikin yanayin damuwa yace, “Ina Ameenatun?”.
       “Tana ɗakinta Yaya, nabar Mama ladi zatai mata gyara a hanunta dan harya kumbura, ga goshinta ya fashe da ƙyar na iya tsaida jini….”
      Ai bama ta ƙarasa ba ya miƙe hankali tashe. Sai dai hakan bai hana bayyanar nutsuwarsa ba. Fita yay Bilkisu tabi bayansa. Kai tsaye ɗakin Raudha ya

nufa, sai dai yana ɗaura hanunsa bisa handle ɗin ƙofar ya dafe kansa da yay masifar sara masa. Da sauri ya shiga girgiza kansa yana ja da baya. Barin wajen

yay ya sake komawa hanyar ɗakinsa. Bilkisu ta bisa da sauri tana kiransa. Wata razananniyar tsawa data sakata jan birki ya daka mata, yay shigewarsa ya bugo

ƙofar da ƙarfi har Bilkisu na zabura.
          Kuka Bilkisu ta fashe da shi. dan kuwa ta fahimci lallai akwai matsala, sai da tayi mai isarta ta koma ɗakin Raudha. Ta jiƙe sharkaf da zufa kamar

ba ac a ɗin saboda gyaran da mama ladi tai mata. Mama ladi dake naɗe mata hanun da bandage ta dubi Bilkisu. “Taji ciwo sosai, dan gocewar ƙashi ta samu.

Garin yay hakan?”.
        Kafin Bilkisu ta bada amsa cikin share hawaye Raudha tace, “A toilet ne na zame”.
      Sannu Mama ladi ta shiga jera mata. Bilkisu dai wani irin tausayin Raudha ɗinne ya lulluɓeta. Dan ta tabbatar daga yayansu aka samu matsalar musamman

da taga shatin yatsu a fuskar Raudha alamar marinta akai. Magani ta sha ta kwanta bayan tayi sallar magrib da isha’i, babu jimawa kuwa barci mai nauyi yay

awon gaba da ita. Bakajin komai sai ajiyar zuciyarta.
        Tagumi Bilkisu tai zuciyarta nata kaikawo. tama rasa ina zata kama akan wannan al’amari. Kusan tara na dare sai ga kiran Basma ya shigo mata. Da

farko kamar bazata ɗaga ba sai kuma ta daure ta ɗaga wayar na gab da tsinkewa. Wani irin dummm kunen Bilkisu yayi jin abinda Basma ta faɗa. Muryarta har

rawa take wajen maimaita “Basma shi Yaya Ramadhan ɗin da kansa yace zai auri Aynah?”.
      Daga can Basma tace, “Wlhy kuwa Aunty B. A gabana Maah tai waya da shi yanzun nan sai farin ciki take tana saka masa albarka. Ni nama rasa wanda zan

tunkara da wannan abun al’ajab shine fa na kiraki naji ko wani abu ya faru anan”.
     “Nan dai babu abinda ya faru, sai dai yana ɗakinsa. Amma dai wannan lamari da ɗaure kai. Basma anya Adda Asmah bata fara cin galaba akan Maah ba?”.
        “Aunty Kamar ya?”.
Saurin dafe kai Bilkisu tai jin zata saki layi. Ta manta ita kaɗai taji abinda Adda Asmah ta taɓa faɗa akan Mahaifiyarsu kwanakin baya sanda ake tsaka da

rikicin auren Yayansu da Raudha. Kuma bata taɓa nuna ta saniba ko taɓa faɗama wani. Sai dai tana kallonta da abun kuma tun daga ranar taji bata sonta duk da

yayar Maah ce. Hasalima tafi shiri da ita fiye da kowa a ƴaƴan gidansu, dan ita takan iya zuwa ta kwana gidansu Aynah ɗin ma ba kamar su Basma ba.
          

★★★★★★

         Tabbas abubuwa sun kwaɓe a tsakanin Raudha da shugaban ƙasa Ramadhan. Ita gaba ɗaya tsoron haduwarsu ma takeyi, yayinda shi yasha gwada zuwa gareta

da zaran ya iso kofar ɗakin sai yaji wani irin mugun tsanarta mai ban mamaki, dole yake juyawa ya fasa. Babu abinda Raudha keyi sai kuka, sai dai duk da

haka tana ƙoƙarin zuwa makaranta. Bilkisu tayi-tayi ta faɗa mata ainahin abinda ya haɗasu taki. Takuma roƙota ALLAH akan karta sanarma su Anne. Rasa mi

Bilkisu zatai tayi, sai kawai ta zubama sarautar ALLAH ido tana tayasu da addu’a.
       A cikin kwanakin da basu gaza gomaba da faruwar komai Raudha duk ta fige ta rame. Sai uban haske datai ta ƙara tsayi. Kullum babu fashi zataje ta

gyara masa ɗakinsa, duk bayan kwana biyu ta wanke masa under wears ɗinsa dan tafi gane wankesu da hannu ba Worthing machine ba. Idan ta gama sai tai drying

nasu a machine ɗin. Komai dare kuma sai tayi zaman gogesu bayan ta musu turare na turaren wutarta na kaya mai daɗin ƙamshi sannan ta maida ɗakinsa ta jere

masa.
        Sam ya daina shigowa gidan da wuri, weekend kuwa har taci ta ƙare bai yarda sun gamu ba. Bata da aiki sai kuka da gayama UBANGIJI. Dan ta rasa

wanema irin tunani zatai akan sauyawar tasa. Koda zuciyarta ta nuna mata dama sabbin halayyar daya fara mata yayine dan ya samu jikinta sai tai saurin ture

tunani dayin a’uziyya. A haka suka sake cinye sati uku babu wani canji.

RAMADHAN

       A sashen Ramadhan shi kaɗai yasan tashin hankalin da yake ciki na tsananin son Ayna’u. Bashi da burin daya wuce mallakar Ayna’u matsayin matar

aurensa. Kullum cikin yima su Bappi nacin akai kuɗi yake dan abun yanzu ya wuce Maah kawai har Anne da Pa da Bappi duk sun sani. Tun suna ɗaukar abun nasa

wasa harya koma basu haushi. Dan ranar daya kai Pa ƙarshe akan lamarin ba karamin zagesa yay ciki da bai ba. Ya kuma masa dogon gargaɗi akan inya sake zuwa

masa da batun Aynah sai ya matuƙar ɓata ransa. Dama kuma itama Maah yaja mata gargaɗi akan damunsa akai kuɗi da takeyi.
       Wannan zagi da Pa yay masa ya matuƙar ƙona masa rai, dan kuwa dai a fusace ya dawo gidan. Abin tsautsayi Raudha na ɗakinsa tana gyarawa dan yau ta

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button