Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 57

fita school da wuri tama rigashi fita, shiyyasa bata gyara masa ɗakin ba sai da ta dawo tunda shi bai dawo ba. Ba karamin firgita tai da ganinsa ba, dan

rabonta da shi tun randa abin nan ya faru sai dai ta gansa a tv ko hoto. Duk ya rame mata a ido yayi duhu. Wata irin tsawa ya daka mata data nema wantsalo

zuciyarta ta baki. Tai nufi fita masa a ɗaki ya shaƙota ya jefa saman gado.

       Lallai Raudha ta tabbatar a baya wahalar da takesha a hanunsa ba wahala bace. Dan kuwa lallaɓata yake kuma cikin soyayya mai gusar da hankali. Amma a

yau ta tabbatar da waye Ramadhan. Kuka take kamar ranta zai fita tsabar yanda ya wajiga rayuwarta. Daga ƙarshe ya korota a ɗakin. Da ƙyar ta iya kai kanta

nata ɗakin, ALLAH ma ya sota Bilkisu bata gidan. Su mama ladi kuma indai ba ita ta buƙaci ganinsu ba babu mai hawo musu nan sai in zaiyi aiki. Ƙofar ta

murzawa key sai dai bai rufu da ƙyau ba ta zube jikinta tana jan numfashi da ƙyar, tsabar kukan da taci har asthma ɗinta na ƙoƙarin tashi. Rarrafe ta

dingayi hanunta rike da ƙirjinta, da ƙyar takai kanta jikin gado ta ɗauka inhaler ɗin akan bedside drawer. Tata ƙoƙarin ganin ta shaƙa hakan bai yuwuba, har

takai numfashinta na neman fara nisa ALLAH ya kawo Bilkisu.
       ALLAH ya taimaka ƙofar data rufe bata rufu ba. Da lallai zatama iya rasa ranta a wannan lokacin. Taimakon gaggawa Bilkisu ta bata, da ƙyar

numfashinta ya dai-daita. Raudha dake magana a wahale ta roƙa Bilkisu ta haɗa mata ruwa mai zafi sosai. Bilkisu batasan mike faruwa ba. A tunaninta ko duk

halin tashin Asthma ɗinne data shiga da kuma gajiyar makaranta. Bayan ta haɗa mata ta fito ta taimaka mata zuwa bayin, duk da dai yanda taga Raudha na

tafiya a bubbuɗe ya ɗaure mata kai matuƙa.
      Da ƙyar Raudha ta iya gyara jikinta, tai luff a cikin ruwan ɗumi tana hawaye da addu’ar ALLAH ya bata juriyar cinye wannan jarabawa. Amma tabbas zuwa

yau ta fara fahimtar mijinta baya cikin hayyacinsa. Akwai abinda ke faruwa da shi da su basu sani ba. Zata tayashi da addu’a koma minene ALLAH ya yaye masa

shi.
 
     Kamar wasa sai ga karamar magana ta zama babba, dan kuwa dai ciwo sosai Raudha ta kwanta washe gari ko makaranta bata iya leƙawa ba ma. Kusan kwananta

uku a halin jiyya kafin ta warware ta cigaba da harkokinta. Sai dai fa a yanzu babu wanda take tsananin tsoron haduwa da shi a duniya sama da Ramadhan. Ko

maganarsa taji a tv sai gabanta ya faɗi. A haka rayuwa ta sake turawa suka sake cinye sati huɗu, sati kusan na bakwai kenan da shiga halin da suke ciki.

Zuwa yanzu kuma har an kai kuɗin auren Aynah saboda birkicewar da Ramadhan yay musu.
       Tuni Pa ya fahimci akwai sihiri tattare da yaronsa. Amma ya zaɓi barinsa a hakan dan yanaji a ransa dole sai Adda Asmah ta shayar da gimbiya Su’adah

zumar mamaki sannan zata san ANNABI ya faku. Koda su Bappi ma suka fara irin wannan zargin Pa ɗinne ya gusar musu da zargin ta hanyar nuna musu babu wani

sihiri uwarsa ke zugasa. Yayi hakane dan baya son suce zasu tashi tsaye akan Ramadhan ɗin, yafi son sai uwarsa taji a jikinta sannan. Amma kuma bai gaza da

masa addu’ar kariya ba.
      Abinda hankalinsu kuma ya gagara kaiwa akai su duka basuyi tunanin ko abin ya shafi Raudha ba. Dan ita dai ko sau ɗaya bata kawo wa kowa ƙararsa ba.

Ta kuma hana Bilkisu faɗa duk da itama Bilkisun ba komai ta sani ba har yanzun. Kullum kuma Anne ta tambayi su Basma sukance Raudha na lafiya harma tana

gaishesu tunda kullum dai suna tare a makaranta. Hakanne ya ɗan basu nutsuwa suke ganin shi kaɗai abin ke dawainiya dashi kenan.

         ALLAH sarki Raudha, sai dai kuma abinda ba’a sani ita kaɗai tasan halin da take ciki, ga yanzu kullum da zazzaɓi take kwana. Ga kasala da batasan

kota minene ba. Komai da ƙarfin hali take yinsa hatta karatun. Ita Bilkisu tana ɗaukar yanayin natane kawai da tunanin maganar auren Ramadhan ɗin. Dan haka

ta maida hankali wajen bata shawarwari da nasiha.
      Bazatace auren Ramadhan baya damuntaba, dan tasan wacece Aynah tasan kuma burinta akanta, dan tunda Ramadhan ya fara birkice mata Aynah da Addah Asmah

suka kirata sukai mata zagin ƙare dangi saboda fahimtar ita sihirinsu bai kamataba. A tunaninsu itama bin malaman take shiyyasata ta tsira. Basu san ALLAH

ne bai ƙaddara mata shan zoɓon waccan ranar ba kawai. Ranar taci kuka matuƙa dan zagine da cin mutunci da bazai taba goguwa a zuciyaba kai tsaye. A

kalamansu kuma ta fahimci lallai akwai ƙullin dake kan mijinta da alama kuma sunada alaƙa da shi. Bata da abin faɗa, dan koba komai dai ƴan uwansa ne. Adda

Asmah ma na amsa sunan uwane a garesa tunda yayar mahaifiyarsa ce da itama zata iya kiranta da uwa. Haka ta cigaba da masa addu’a da ita kanta abun na

damunta.
      Sai dai halin da take ciki na rashin jin daɗin jiki yafi kwashe kaso mafi yawa na damuwarta. Ko mahaifiyarta batasan halin da take a ciki ba. Sai dai

a duk sanda sukai waya takance Mummy kimin addu’a. Idan asabe ta nuna damuwarta cikin tashin hankalin furicin Raudhan sai ta dinga kwantar mata da hankali

akan babu komaifa saboda karatu take cewa hakan.
     Ita dai Asabe hankalinta ba wani ya kwanta bane. Amma sai ta dage da bin ɗiyarta da addu’ar fatan alkairi. Itama kuma Raudha bata wasa. sosai take a

kan ƙafafunta tana gayama ALLAH damuwarta akowanne dare. Wani lokacin ma tana salla tana rawar sanyin zazzaɓi, haka ta dage da azumin alhamis da litinin. Ta

kuma dage da saka har Abba (M. Dauda) turama kuɗi akan ya bada sadaka yasa a mata addu’a ita da Ramadhan. Da yake shi kan babu notika ɗaurarru maimakon ya

fahimci akwai matsala sai ya kama dariya yana yana faɗin.
        “Ƴar nema taji daɗin gidan gwamnati bata son suyi shekara biyar kawai. Indai addu’a ce kin tara kin samu, yau kaf almajiran dake garin hutawa saina

bisu kowacce tsangaya na tattare da malamansu sun saka rokon ALLAH, dan nima inason ku koma hawa na biyun ai. Amma Raudha ya kamata kima mijinki magana ko

ministan bada kuɗin fansho ya bani mana. Zamannan ya isheni haka kinga wannan sarautar ba wani kuɗi ake samu ba sai uban fama da rawani da zazzare ido a

fada. Ni badan ma kar hakimi yace na raina karamcinsa ba da wlhy tuni na ajiye. Ni kuma yan kuɗina kullum kasa suke, dan ma ALLAH ya taimakeni wanda Ƴaƴan

Larai suka sata an ganosu ai da yanzu hawan jini ya shanye muku ni.
     Murmushi Raudha tayi tana share hawaye. “Karka damu Abbah insha ALLAH zan san abinyi. Amma nidai gara kayi haƙuri ka cigaba da zuwa gidan hakimin”.
     “To ai duk yanda kikace haka za’ai uwata farar haihuwa farar aniya your excellency. Insha ALLAH sai kunyi goma indai mulkin NAYA ne”.
    Dariya ta ƙyalƙyale da shi babu shiri dan ya bata dariya sosai. Da ga haka sukai sallama ta ajiye wayar. Bargo ta kara ja har kanta dan wani irin sanyi

mai ratsa ƙashi takeji. Ga ƙasusuwan ta kamar ana mata daka a kansu. Saboda zazzaɓin yau ko lecture ɗin karshe bata zaunaba ta gudo gida. Sai dai ta iske

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button