BAKAR INUWA 63-64

hannu, gaba ɗayanta ya dauka cak yay kan sofa da ita. Duk yanda take watsal-watsal da ƙafafu bai saurareta ba. Sai ma dariya da yake mata harya direta.
“Rama cuta ga macuci ai ibada ne yarinya”.
Yay maganar da kwashe hijjabinta gaba daya ya ajiye. Hannayenta dake kai masa ƙananun duka a ƙirji ya riƙe tare da kwantowa kanta, sai dai bai
sakar mata nauyinsa ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ladabtar da zille-zillenta ta nutsu tana amsar saƙonsa. Sai dai acan kasan ranta a matukar tsorace take.
Sai da ya tabbatar tayi laushi ya nema bin hanayar da take tsoro ta fara masa kuka da magiya. Dama ba zuwan zai ba. Amma ya tabbatar mata zai ƙyaleta idan
tai masa abinda yace. Ko musu babu kuwa ta amince. Dan gwara hakan ita dai da abinda takewa tsoron…….
Luf take shiru a jikinsa tana sauraren yanda yake sauke numfashi a hankali da sanya mata albarka. Yayinda hanunsa ke cikin sumar kanta yana faman wasa
da ita duk ya birkita mata ita. Murya can kasa a ɗashe tace, “Ya Ramadhan sallar isha’i fa akeyi”.
“Uhhm naji ai”.
Ya faɗa a shaƙe idanunsa rufe. Shiru tai bata sake cewa komai ba har kusan mintuna biyar sannan ya miƙe. Kai tsaye toilet ya shiga, hakan yasa Raudha lumshe
idanu da sauke ajiyar zuciya takai hanunta saman cikinta tana shafawa. Bata san yaya zaijiba idan yasan tanada ciki, ita kanta a duk sanda ta tuna akwai ɗa
mai alaka da shi tanajin tsantsar farin ciki. Badan shi shugaban kasa bane, badan shi jinin Taura family bane. Sai dai ɗunbin soyayyarta da take hangowa a
cikin idanunsa. Motsin fitowarsa a bayin ya sata dawowa hayyacinta daga dogon tunanin data lula.
Yanda ya fito yana goge sumarsa da jiki ya tabbatar mata wanka yayo, saurin ɗauke kanta tai ta maida gefe. Yay ɗan murmushi da ƙarasawa jikin
Wadrobe ɗinsa domin duba kaya. “Madam tashi kiyi wanka muyi salla”.
“Ni alwala kawai zanyi”.
Ta faɗa a shagwaɓe tana mikewa a gadon itama. Murmushi kawai yayi amma komai baiceba harta shige toilet. Sai dai kuma ashe cika bakinne kawai, dan itama dai
hummm kawai…………✍