Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 65-66

Episode 65-66

………..Fitowarta dai-dai da ƙoƙarinsa na kammala busar da sumarsa. Ya kalleta kawai ya ɗauke kansa baice komaiba. Dan rigartace dai a jikinta data shiga

da ita ala dole babu abinda tayo. Sai da ya shimfiɗa abin salla ya miƙa mata wandonsa mai taushi na adidas da farar t-shirt. “Saka muyi salla lokaci na

shigewa”.
    Kanta a kasa batare data kallesa ba tace, “Bafa abinda ya sameta”.
      “Humm Ameenatu kenan, karki manta na rigaki zuwa duniya. Bayan rigaki shekaru kusan goma sha takwas na baki, kinga a lissafi kuwa lokacin da nake a

mizanin shiga shekarun girma na ɗa namiji aka haifeki”.
      Kunya kamar ta nutse. Dan sam batai tunanin ya ganeba. Dama sotai ta masa dabara sai sun tada sallar ta gudu ɗakin Anne ta canja kayan tai salla.
        “Hallo! Ko sai na nuna miki shaida ne dan rigar kanta ta tona miki asiri tare da wannan”. Ya tura hanunsa cikin hular kanta ya jawo silin jiƙaƙƙen

gashinta a ciki. Da sauri ta kwashi kayan zata koma toilet”.
       “Hii aini ba surukinki bane canjasu anan konazo na canja miki kina ƙara makarar damu”.
     Babu yanda ta iya dole tabi umarninsa, bayan ta saka kayan suka gabatar da sallar. Suna idarwa wayarsa ta hau ruri, yasan Anne ce dan haka ya miƙe zuwa

bedside drawer ya zauna a bakin gadon yana daukar wayar….
        “Kai ka fita idona kawomin yarinya taci abinci tana fama da kanta”.
      (Mutum da matarsa ƙarfin hali kenan) ya faɗa a zuciya yana sakin murmushi. A fili kam yace, “Okay Gimbiyar Bappi yanzu kuwa maida wukar”.
     
          ★Gaba ɗaya Raudha jitake kamar ta nutse dan kunya. Kanta a kasa ta risina ta gaida Anne da Bappi. Zata zauna kusa da Bilkisu dake tare da su yaja

mata kujerar kusa da shi tare da kamo hanunta yanda su Bappi bazasu gani ba. Sai dai ya makaro sun gani ɗin. A kuma kallo ɗaya Anne ta fahimci wayo yaje

yayma Raudha, sai dai addu’arta ALLAH yasa bai aikata abinda zai cutar da itaba tunda ɗinkin jikinta bai gama warkewaba. Tunda tazo ɗaki taga babu su tai

niyyar kiransa a waya Bappi ya hanata. Acewarsa yasan Ramadhan na cikin hankalinsa bazai sake yarda ya aikata abinda zai cutar da Raudha ba. Gara su barsu

su sasanta kansu da wuri kodan su Gimbiya Su’adah ma.
        Bilkisu ce ta zuba musu abincin, dan Raudha dai ta kasa motsin kirki. Gani take kamar su Anne sun fahimci abinda duk ya faru tunda har abu yakai ga

canja kaya. Kowa nacin abincinsa hankali kwance amma banda ita. Tsakura kawai take kaɗan-kaɗan.
      “ALLAH in bakici abincin nan ba zan tonaki yanzu su Anne susan mikika aikato a ciki da hujja”.
     Wani irin ƙululu cikinta ya bada. Harta kasa daurewa saida ta ɗan dubesa. Gira ɗaya ya ɗage mata da sakin wani munafukin murmushi daya tilastata maida

kanta ƙasa da hanzari. Duk abinda suke su Anne na lure da su, sai dai kowa ya ɗauke kansa kamar bai san anaiba.
         Farfesun kan rago Ramadhan yace Bilkisu ta zuba masa. Kamar jira tana buɗe bowl ɗin Raudha tai saurin toshe hanci da rike numfashinta. Babu wanda

ya lura da hakan Bilkisu ta fara zubawa, kasancewar kusa da shi take tuni ƙamshin ya ƙara karfi a kusa da ita. Har takai amai na yunƙuro mata. Ta mike zaram

zata bar wajen ya rikota.
      “Lafiya kuwa?”.
Kanta ta shiga girgiza masa da nuna masa ya saketa amma yaƙi. Anne ce ta fahimci abinda ya ɗaga hankalin Raudhan da sauri tace, “Ramadhan saketa”. Tai

maganar tana mikewa.
       Sam ya kasa fahimta, a zatonsa wani abune daban, ina kafin ya samu damar cewa wani abu ta kasa daurewa ta fisgi hanunta da ƙarfi. Sai dai kafin takai

toilet na bayin ta saki aman a waje. Gaba ɗayansu sukayi kanta har Bappi, dama Ramadhan tunda ta fisge ya bita. Amai sosai takeyi a wahale. Shiko gaba ɗaya

ya cimimiyota jikinsa duk a ruɗe. Sai tambayarta yake mike damunta?.
          “Ramadhan ka barta taji da abinda ya dameta mana Please”.
Anne ta faɗa cike da tausayin Raudha. Sai da ya tabbatar ta gama ya ɗagata cak ya nufi sashensa da ita. Anne zata bisu Bappi ya riƙo hanunta yana girgiza

mata kai da murmushi a fuskarsa. “Barshi shi daya jawo yay aikin”.
     Murmushi kawai tai da girgiza kai tana mintsininsa da nuna masa Bilkiau da ido. Yay karamar dariya da ita kawai tajisa. Mai aikin Anne ce tazo ta gyara

wajen. Su kuma suka koma kan table suna karasa cin abincinsu kowa da tausayin Raudha a ransa

     Bayan kamar mintuna goma sha biyar Ramadhan ya fito, a lokacin sun bar dining sun koma falo.
      “Yaya jikin nata?”.
Bappi ya tambaya cike da kulawa. Cikin damuwa Ramadhan daya koma duk wani kalar tausayi yace, “Bappi na barota kwance zan sama mata wani abincin a kuma kira

Momyn Jabeer”.
          “No kiran Mommyn Jabeer ba shine mafitaba ai. Da alama kamshin naman kan canne bataso. Taci abinci saita kwanta ta huta ALLAH ya raba lafiya”.
         Wani irin yarrr yaji har saman kansa. Cikin rawar harshe yace, “Anne ban gane ba?”.
     Hannu Bappi ya mika masa da faɗin, “Ajiye goro na ganar da kai”.
    Ganin Bappi a serious sosai Ramadhan yay ƴar dariya yana shafa aljihu. Sai dai babu komai a ciki, hatta wayoyinsa na ɗaki. “Bappi na maka alƙawarin baka

koma mi kakeso faɗi dan ALLAH”.
     “Tabb ai an daina aikin banza a NAYA kai dai ajiye kasha labaru”.
         Rasa mima zaiyi yay, sai kawai ya kwanto agogon hanunsa ya ɗora a hanun Bappin. Bappi ya ɗan juya agogon, sai kuma ya taɓe baki. “Ba laifi mai

nauyine ai. Bilkisu bashi yasha”.
     Bilkisu dake dariya cike da ɗoki ta nufi Yayan nata tayi ɗan hugging nashi, sai kuma ta sakeshi. “Yaya na kusa zama Mummyne fa, Aunty nada cikin wata

biyu da kwanaki….”
       “What?!!!”.
Ai kafinma ta ƙarasa bayani ya juya da sauri ya bar wajen zuwa sashensa. “Na yafe miki sauran labarin”. Ya faɗa yana ɗago hannu sanda yake gab da shiga.
        Mi su Anne zasuyi inba dariya ba. Pa dake tsaye tun ɗazu batare da sun sani ba yay murmushi kawai yana girgiza kansa. Ɗansa kenan abin alfaharinsa.

Murɗaɗɗen mai wahalar fahimta ga wanda ke nesa da shi. Da yawan mutane akace musu Ramadhan mai sauƙin kaine a cikin gida zasu karyata. Domin shi mutumne mai

yanyin mutanen da ake kira da girman kai kai tsaye. Dan kuwa tabbas magana ma sai yaso da wanda yay niyya yakeyinta. Dariya ko mutane da yawa kance basu

taɓa gani daga garesa ba. Dan akan jima baiyi hakan ba sai a inda yaso. Sai dai ga wanda yaso kuma ya aminta shi mai sauƙin kaine da iya mu’amula matuƙa.

        Cikin ɗan barcin daya fara figarta kawai taji an rungumeta. Tare da fara bata zafafan kiss’s tako ina da ina a jikinta.
        “Ya Ramadhan lafiya?”.
Raudha ta faɗa a kasalance dan da gaske barci ya fara ɗaukarta. Bai bata amsa ba. Sai rungumeta da yay tsam a jikinsa yana jero addu’ar nan ga wanda abin

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button