JIDDATUL KHAIR

JIDDATUL KHAIR 47

Ad

_____

Lkci daya Abuturrab ya saketa ta dalilin hasken wuta da ya dawo kitchen din, ta rufe bakinta a rikice ta juya ta bude kofar kitchen din ta fice da gudu, Aneesah na tsaye parlor bayan ta kunna solan gidan, ta bi jiddah da kallon mamaki barin yanda taga ta rufe bakinta da hannu har ta wuce sama, can ta kalli kofar kitchen din, sai kuma ta tafi can da sauri ta tura kofar xata shiga suka kusa cin karo da Abuturrab xai fito, ya d’an buda ido kafin yace komai ya juya mata baya, walking toward the gas yace “Na xata kinyi bacci

ai….” Daga sama har kasa ta dinga kallonsa, yana tsaye gaban gas din bai yarda ya juyo ba tace “Me kake yi a kitchen Captain?” Yace “Gyaran kitchen din da kika bari kaca kaca” Sai a sannan ta bi kitchen din da kallo taga sai walkiya yake, ko ina yayi fess, sake kallonsa tayi tace “Who just left the kitchen now?” Ya dau lighter kamar xai kunna gas din yace “The person that helped in transforming the kitchen back to it normal sef…” Tace “To wannan juya min bayan da kake na meye haka?” Wani boyayyen ajiyar xuciya ya sauke ya daga wayarsa da ya fara ring duk da Ahmad ne ke kiransa ya kai kunne still backing her, Aneesah ta gaji da tsayuwarta ganin ba gama wayar xai yi ba gashi yayi backing dinta ta juya ta fice daga kitchen

[indeed-social-locker sm_list=’fb’ sm_template=’ism_template_9′ sm_list_align=’horizontal’ sm_display_counts=’true’ sm_display_full_name=’true’ unlock_type=2 locker_template=8 sm_d_text=’

This content is locked

Share This Page To Unlock The Content!

‘ enable_timeout_lk=1 sm_timeout_locker=1200 reset_locker=1 locker_reset_after=1 locker_reset_type=’days’ ism_overlock=’default’ ]

din, sai a snn ya d’an waiga, ya dau mug ya bude flask ya xuba ruwan xafi ya saka Lipton, sannan ya dau lime din da yake siyowa a kitchen din ya yanka uku yayi squeezing a ruwan lipton din… Hajja ce tsaye kan Jiddah dake xaune kasan dakin ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, rai bace Hajja tace “Naga abinda ya fi karfina ni Dije, yanxu baxa ki bude baki ki gaya min me aka maki ba in san ta inda xan fara, matar gidan ce ta maki wani abun koko?” Jiddah taki dagowa hawaye sai sauka idonta yake duk jikinta yayi sanyi, Hajja bata sake ce mata komai ba ta juya ta fita daga dakin ta tafi can bangaren Abuturrab, da karfi ta kwankwasa kofar, Aneesah dake xaune saman kujera a parlon tana kokarin dialing number Aunty ta kalli kofar, jin an sake kwankwasa kofar kamar xa a cire ta mike a d’an fusace tace “Wai waye wannan” Tura

Ad

kofar parlon Hajja tayi ta shigo ciki, tana huci tace “Ni dai kafin ince komai ina son sanin waye mai gidan nan tukun??” Aneesah tace “Haba dai.. ai ba girmanki bane shigowa wannan bangaren Hajja, duk abinda kike so da sai ki jira a fito…..” Wani xagi Hajja ta mulmula mata tace “Ke har kin isa ki gaya min yanda xanyi a gidan jikana? Kaji min yar banxa, Ashe dama bayan bak’ar kazanta har da rashin kunya da fitsara kika iya ban sani ba? To wllh na fasa komawa wannan gantalallen Masar din dai tunda ba uban da na hada dasu, ina nan kasata Najeriya sai na nemo ma jikana auren tsaleliyar mata me bama tsafta hakkinsa, yar

gayu me kamshi xan samar masa ba irinki kazama me wari ba, mata daga aure ko wata biyu ba ayi ba kin hallakar min gidan jika da kazanta ko ina banda tsutsa babu abinda yake fita, ko irin kamshin turaren nan na amare gidan nan bai samu gatan yi ba, to tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin mace kazama aminiyar dauda irin ki ba, amma duk ba wannan ya dameni ba, ya xan sa yarinya karama wanda kika kusa haifa ta tsaftace kitchen din da kika halaka yake fitar da tsutsa kuma ki saka min ita kuka babu gaira babu dalili??” Aneesah dai na tsaye sai kallon Hajja take baki bude with shock, Hajja tace “Ba kya kalleni kamar shashasha ba dama, wllh dole in nemar ma Aliyu mata me tsafta da son kamshi dai dai shi, ina ta kallonsa ganin ya d’an rame ashe kaxantar ki ne ke tsotse mana shi, to Allah ya isa wllh, mu kaf xuri’armu babu kazami….” A fusace Aneesah ta nufi kofa ta fice fuuuu, Hajja tace “Uwar kazaman Najeriya kawai, mata haka kazama na bugawa a jarida, dubi farin kafet din parlon nan fisabilillahi yanda ya fara fita hayyacinsa, parlon ma naji kamar karni yake wllh, ko da yake dai ba ruwana bari inyi shiru, ba abinda Usman ya aikoni inyi a gidan nan ba kenan, amma da yau kinji maganganu a kan kazantarki wllh” Aneesah na sauka downstairs ta tadda Abuturrab xaune ya gama shanye cup din Lipton da ya hada, tana shigowa parlon ta rushe masa da matsanancin kuka tace “Aliyu dama grandmum dinka xuwa tayi ta ci mun mutunci ta ci

xarafina har gidana? Dama haka kuke ban sani ba?” Kallonta ya dinga yi don bai san me ya faru ba, sai ga Hajja tana sakkowa tana cewa “Wllh kinci albarkacin ba abinda Usman yace in xo inyi a gidan nan ba kenan, amma yau da na maki bankada iri iri, kuma gida muna nan babu yanda kika iya da mu tunda ba wani ya haifo min Usman din ba har Allah ya basa Aliyun” Da mamaki Abuturrab ke kallon Hajja yace “Me ya faru Hajja?” Tace “Me kuwa baxai faru ba Aliyu, daga na tura Jiddah ta farfado da kitchen din da ta fara hallakarwa kawai sai ta saka min ita kuka na rasa abinda tayi mata, yanxu haka yarinyar na can tana rusa

kuka ta inda take shiga ba ta nan take fita ba kuma taki gaya min menene, da kyar fa Ramlah ta amince ta biyoni, yanxu in maida mata yarinya idanuwa a kumbure me kake tunanin xai biyo baya matar da ba mutunci gareta ba kowa ya san da haka…” Abuturrab ya d’an saci kallon Aneesah, lkci daya ta sake fashewa da kuka tace “Wllh baxan kwana gidanka ba yau Aliyu, ni ai bansan bayan duk hakurin xama da nake da kai a yanda kake akwai wani kalubalen dake tunkaroni ba….” Tana fadin haka ta wuce sama kamar xata tashi sama, Hajja tace “Oho dai Allah ya ishi Jiddah, kai kuma kayi ta istigifari don wnn ba karamin

Ad

_____

1 2 3 4Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button