Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 65-66

farin ciki ya sama.
       الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .
Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat.
     Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni’imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika.
اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.
Alhamdulillahi ala kulli halin
       Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali.
        Rigar dake jikinta ya ɗaga nanma yana sumbatar cikinta. Kafin ya kwantar da kansa akai wasu hawaye na tuna Haseenah na sakko masa. Ashe bayan

Haseenah yana da rabon sake haihuwar ƙanen a duniya. Ɗagowa yay ya sake sumbatar cikin, sai kuma ya fara karanto addu’ar nemawa ƴaƴa tsari (iyaye dan ALLAH

a dingayi, kai ko yaron cikine dake karanta ki shafe cikinki kafin ya fito ki ɗora dayi masa a zahiri????????. Domin kuwa MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su

tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan addu’ar: ).
             أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ.
O’eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli ‘aynin lammah.
       Ina neman muku tsari da kalmomin ALLAH cikakku daga dukkan shaiɗan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa.
        Raudha dake murmushi takai hannu ta shafa kansa. “Irin wannan security ba ɗaga ƙafa haka?”.
      Tasowa yay gareta shima fuskar tasa da murmushi, ya kwanta kusa da ita tare da tokare kansa da hanunsa ya lakace mata hanci. “Uhmm barni gara na tofe

abina tun yanzu kodan masu ƙarancin tsoron ALLAH. Yanzu nan Baby Luv kinsan da wannan abin farin cikin tun ɗazu kikaƙi sanarmin? Anya kuwa kina sona?”.
     Dariya tayi tana mai saka tafukan hanunta ta rufe fuska. “Kai Ya Ramadhan kawai kuma saina kama faɗama inada cikin ɗan fari dan banda kunya”.
        “Lallaima yarinyar nan”.
Ya faɗa shima yana dariya da son zame hanunta. Ƙin yarda tayi, sai ma juyowa datai da sauri ta sinne kanta a ƙirjinsa. Idanu ya lumshe a hankali tare da

rungumota ya kanƙame ta shima. ji yake kamar ya haɗiyeta kawai ya huta. “I love you sweetheart”.
        “I love you too Noorullah”.
“Nice name dear I love more. Na huta an daina kaƙabamin Yaya babu dangin gabas babu na yamma. Dolene yau nayi celebrations biyu kenan”.
        Siririyar dariya ta saki tana mai ɗagowa ta sumbaci lips nasa ta sake maida kanta ta kudindine a jikinsa.
      “Hummm wlhy yarinya ki bani kwana uku kacal saina maidaki mara kunya ta bugawa a jaridar duniya”. Yay maganar yana mai rungumeta sosai a jikinsa

murmushi yaki barin fuskarsa.
        Babu wanda ya karajin ɗuriyar Ramadhan da Raudha a gidan, kuma babu wanda ya nemesu. Garama ya kira Bilkisu daga baya ta kawoma Raudha sabon abinci

taci ya busar mata da gashinta daga nan sukai kwanciyarsu…………✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button