BAKAR INUWA 67-68

wataran idan kaddarar hakan ta shigo, sai dai ina fatan rayuwa dake ke ɗaya dan tun asali zama da mace ɗaya ne tsarin Ramadhan. Sai dai tsarin ALLAH yana
gaba da nawa Ameenatu. Amma a yanzu nakine ke ɗaya babu wadda aka ɗaurama Ramadhan aure da ita”.
Ƙanƙamesa tai da sake fashewa da kukan da batasan na farin ciki bane kokuwa na minene. “I love you Noorullah”. Ta faɗa da ɗagowa lokaci ɗaya ta manne
lips nata da nashi.
Tab humm, batasan kuka ta kawo gidan mutuwa ba. Dan kuwa bawan ALLAH caraf ya cafke tare da ɗaukarta cak sukai bedroom. Yako shiga yamutsata son
ransa. Yama manta da wata kwalliyar biki. Sai da labarin ya canja salo kuma ta ruɗe. Sai dai batasan dama haƙuri yake yana ɗaga kafa ba dan dole. Aiko tilas
ta bari ya rage zafi yanda ya kamata. Da ga karshe dole aka sake nemo su Basma suka kawo mai sake kwalliyar biki.
Uhhm andai ji kunya????????????????.
★Bayan sallar la’asar sai ga Aunty Hannah mata ga vice president da tawagarta sun iso gidan bikin. A ciki kuwa harda Asabe da Hajiyar Birni dasu
Fatisa. Wayyo dadi kamar zai halaka Raudha. Ta rasa inda zata saka kanta taji daɗi. Ga Anne ta saka an musu kyaƙyƙyawan karamci da tarba ta musamman ta
abinci. Su aunty Hannah anata faman ɗaga kai da hura hanci ana yatsine-yatsine kai kace itace ma firt lady ɗin tsabar yanda guards ke dogare a bayanta da
mata ƴan siyasa.
Ina Raudha bata ita takeba. Farin cikin ganin Mummynta ya rufe mata ido ruff. Ko Hajiyar Birni da Hajiya mama sai da sukai mata tsogumi ta gaishesu.
Anan suka kasance har bayan magrib. Da zasu wuce Anne ta haɗa musu shatara ta arziki musamman su Fatisa da sukaji kamar karsu rabu da ƴar uwarsu. Dan suma
dai yanzu Alhmdllhi har sun kawo mazan aure ana shirin zuwa hutawa gaida Alhaji baba Dauda mai zamani surukin Mr president na ƙasar NAYA. Yaso zuwa daurin
aure Inna ta tashi da amai da gudawa aka kwasheta asibiti a rikice tana can ana kara mata ruwa dole ya hakura. amma yasha takaici wai kallo ya wucesa daga
shi har M. Gambo amininsa da shima ya gama saye zuciyar asabe batare data san shiɗin bane har yanzun. Dan yace bazai bayyana mata kansa ba sai ta yarda ya
turo iyayensa. Itako tace su ba yaraba bata yarda da wannan ganganciba yazo gareta kawai su sasanta. To yanzu dai yace zaizo ɗin amma bai tsaida rana ba.
Bayan wucewar tasu ma zazzaɓi ne ya rufe Raudha. Koda aketa shirin tafiya dinner ita tana can duƙunkune a bargo. Dama kuma bata saka ran zuwan ba tunda
tasan Ramadhan dai bazaije ba. Kuma babu tabbas zai barta taje itama.
★Kafin a tafi dinner gimbiya Su’adah ta cigaba da neman number Fulani da Addah Asmah kamar yanda taketa fama tun bayan dawowar ƴan ɗaurin aure hakan
baiyu ba. Dan duk kashe wayoyinsu sukai. Taso su Safina su leƙa gidan suyi ALLAH ya sanya alkairi hakan bata yuwuba dan Taura house yayi matukar cika
kasancewar duka matan gidan uku sun aurar da yara.
Ta turama Ramadhan gargaɗi sosai akan ya tabbatar yaje dinner ɗin nan amma sai dai baima gani ba dan yau yayi busy da yawa. Babu wanda yasan ainahin
abinda ya faru sai fa da aka isa wajen dinner sai su Bilkisu Amare kawai da angunansu amma babu Aynah babu Ramadhan babu duk wani wanda ya shafi masarautar
Bina dake a gidan Addah Asmah dan dama biyu aka rabu. Wasu sukayo nan Taura House wasu can gidan a cewarsu duk za’a haɗe wajen dinner da walima dakai amare.
A sannan gimbiya Su’adah takejin mummunan labarin cewa ai kiɗa ya canja bada Ramadhan aka ɗaura aure ba. Ta matuƙar gigicewa a haukace ta shiga neman
number Ramadhan amma har sannan switch up. Ta nufi sashen Pa ta iskesa da baƙinsa da basu wuce ba. Tsabar yasan miya kawota kuma yay kememe yaki tasowa.
Haka ta wayance ta fito. Maida akalar kiranta tai ga Mai-martaba, shikam ta samesa. Sai dai yaja mata gargaɗi akan idan har tace wani abu yana cikin Taura
house sai ya mata hukunci mai muni, tabar koma minene za’a tattauna bayan biki.
Wannan al’amari ya matuƙar sake rikita gimbiya Su’adah, dan kuwa a daren nan jininta ba karamin hawa yayiba har sai da Safina ta taimaka mata da
maganin barci.
★Wajen dinner kam bidirinsu suka sha kamar babu gobe. Dan gaba ɗaya anan aka haɗe amare da angwayen. An raƙashe an kwalle anci ansha sai dai Bily taji
inama Raudha na wajen. Amma dai su Basma sun ɗauka komai a waya duk da anyi vedio recording. Su Ibrahim ne suka halarci wajen bisa wakilcin babban yayan
amare shugaban ƙasa Ramadhan tare da cos. Hakama manyan mutane matan gwamnoni da ministers da ƴaƴansu duk sun halarta. Dan hatta da yaran su Alhaji yaro
glass na nan anyi komai da su kamar babu wata a ƙasa. Karfe ɗaya aka tashi amare da tawagar jama’a yan biki sukayo gida. Masu gidaje a cikin Bingo suka nufi
nasu muhalli anama angwaye da amare fatan alkairi da zaman lafiya da zuri’a masu albarka………✍