BAKAR INUWA 69-70
Episode 69-70
…………Washe gari Raudha ta tashi batajin daɗi sosai. Dan har saida Dr Hauwa ta shigo ta dubata har dasu karin ruwa. Sai hankalin Ramadhan ya rabu biyu
ga meeting da za’a zauna duk da dai babu Raudha a ciki. Ga jikinta kuma.
Itako Gimbiya Su’adah tana can sun fice a sace ita da Safina zuwa gidan Addah Asmah, dan tana son tasan mike faruwa kafin a zauna zaman meeting duk da
tasan har dasu Adda Asmah ɗin za’ayi. Lokacin da motar su gimbiya Su’adah ke shiga layin su Adda Asmah a lokacine driver daya ɗakko fulani zai kai Taura
House shi kuma ke fita. Dan Addah Asmah tace fulanin tayi gaba suma zasu ƙaraso ita da mijinta da Aynah da kuma mijin Ayana ɗin da suke so ya saketa take a
yau.
Saboda yanayin hayaniyar mutane yasa Safina bata tsaya da motar ko’ina ba sai ƙofar falon baya data san su Adda Asmah nada ita. Dan kafin tai aure
idan tana son haɗuwa da Faisal mijinta tasha satar fita ta wajen taje ta dawo wani bai sani ba. Ta wajen babu kowa, sai daga ɗan bayansu ta backyard suke
jiyo ƙananun hayaniyar masu wanke-wanke. Ginbiya Su’adah takai hannu zata buɗe ƙofar wani furici mai kama da saukar aradu yay azamar taka mata birki, tai
kuma saurin damƙe hanun Safina dake shirin yin magana tana girgiza mata kai….
Su gimbiya Su’adah sun iso gidanne a dai-dai lokacin da Adda Asmah da Aynah ke tare a wannan falo, waya Adda Asmah keyi da bokanta akan abinda zasuyi
idan anje wajen taro. Shine furucin ƙarshe data maimaita kamar yanda bokan ya faɗa ya shiga kunnen gimbiya Su’adah. Kasancewar sun gama wayar Adda Asmah ta
ajiye a sanyaye tana duban Aynah data kafa mata ido.
“Mom wai yanaga jikinki kamar yayi sanyi?”.
“Tabbas dole jikina yay sanyi Aina’u. Sai dai zan iya aikata komai saboda ke. Kamar yanda malam yace na kirashi kafin muwuce wajen taron shine
na kirashi, dan wannan dalilinne ma yasa nace Ammy (fulani) tai gaba zamu biyota. Yanzu har ita ta bar sanin sirrinmu tunda bazatace batason Su’adah kamar
yanda take sona ba…..”
“Hakane Mom, amma nidai sanar dani mike faruwa kawai?”.
“Daɗina dake wutar ciki. Abinda kikaga ya girgizani da maganar malam ya tabbatarmin bincikensa na jiya ya nuna masa zasuyi taurin kai akan yarda da
buƙatar mu, amma idan muka jajirce za’a iya samun nasa ƙila. Sai dai Ramadhan ɗin shine babbar matsala yanzu, saboda akwai yarinyar dake tsaye a kansa game
da addu’a hatta azkar baya wasa yanzu safe da yamma, yace inhar tana tare da shi mawuyacine duk wani aiki namu yanzu yay tasiri a kansa dan tanada
jajircewa. Hasashena ya bani tabbas shegiyar yarinyarnan ce ƴar karuwai. Maganarsa ta ƙarshe data firgitani itace zaɓin daya bamu akan Ramadhan ɗin, kodai
akawar da shi kowa ya rasa shi da yarinyar, kokuma mu haƙur……”
“Ina bazai yuwuba Mom, wlhy bazan iya haƙura da Ramadhan ba. Idan nai haka ko to tabbaci ban cika mace ba. Har yaushe zuciyarki ta fara tausayine
Mom?.”
“Nima ba tausayi nake jiba Aynah, domin zan iya komai a kanki, ciki kuwa harda kauda duk wanda ya tare min gaba. Tunda muka taso a gidanmu kowa yafi
son Su’adah duk da kasantuwarta yarinya mai girman kai da ɗaukar kowa ba komai ba. Ba ƙyau tafini ba, amma ko kaya mukasa kafin a yabamin an yaba nata
saboda ta iya tsara ado. Kullum a makaranta takan ɗauki maki na jarabawa fiye da nawa. A gida mahaifinmu yafi sonta fiye da kowane ɗa, dan hatta da
shawararsa mai muhimmanci yakanyi da Su’adah baiyi da su Ammy ba. Mu duka ƴaƴan sarki ne amma ita kaɗai ake kira da gimbiya duk da nice babba. A koda yaushe
wannan abu nacimun rai, taya zan fita komai amma yazam kullum itace da nasara sama da tawa? Hatta a shekarufa na fita. Abinda ya ƙara baƙanta raina da
rayuwa lokacin da muke UK a school, tunda na fara ganin Basheer Hameed Taura na kamu da sonsa. Amma abin mamaki saina tsincesa tare da ƴar uwata Su’adah har
sun fara soyayya ni ina nan ina ƙulla yanda zan tunkaresa da tawa soyayyar. Na shiga tashin hankali mara misali Aynah, har takai naji bazan iya jurewaba na
tunkaresa da batun. Hummm karkiga irin korar kare da Basheer yamin tare da dogon gargaɗi, tun daga nan karatuna ya shiga hanyar taɓarɓarewa har muka dawo
gida babu komai a result ɗina. Itako ta dawo da sakamako mai ƙyau cike da nasarori. Muna dawowa babu ɓata lokaci aka fara shirin aurar damu, ita aka aura
mata wanda take so ni aka auramin mahaifinki batare da ina sonsa ba, dan iyayenmu ne suka ƙulla hakan. Watan Su’adah goma cif a Taura House ta haife ɗanta
namiji santalele. Niko a lokacin ko ɓatan wata. Naji zafin hakan matuƙa amma naita ƙoƙarin dannewa. Bayan shekara biyu da yayensa ta sake Mardiyya, har
lokacin ni babu labari. Nadai taƙaice miki sai a harhuwar Lubnah muka haihu tare, lokacin tanada yara har uku kenan niko 1 kuma mace ke. Na ƙara na biyu ma
mace. Wannan ya ƙaramin tsanarta dan koba komai ta ɗarani da namiji kuma ƴaƴanta sunfi nawa. Daɗin daɗawa ɗanta shine ɗa tilo namiji agaba ɗaya Taura
family. Nasha auna cutar da Ramadhan amma bai yuwuba saboda kakankinsa kullum nane suke da shi kamar sun san burina. Iyayi nayi Su’adah ta amshi Ramadhan a
hanunsu amma sun hanata. Dan haka nasa akai aiki akansa aka tura masa wasu hatsabiban ajanu dakan maidashi tamkar wani mahaukaci. Sai dai mahaukacin ma naso
ya koma baki ɗaya hakan bai kasance ba. Tun lokacin aurensa na farko naso ki auresa amma ya nuna baya ra’ayi, dan a yanzu babban burina shine ki auri
Ramadhan ki ƙwato mana duk wani abinda Su’adah kejin tanada shi a hannu daya fini, amma kuma sai komai ya lalace bayan mun ɗakko hanyar nasara……”
“To amma Mom duk da waɗan nan abubuwan shine kike tunanin bazamuyi abinda malam yace ba. Ramadhan nada taurin kai, na tabbatar da wahala ya yarda da
aurena, sai dai in uwarsa ce tace zata tsine masa. Idan ma tace hakan shi wannan jakin da aka auramin zai sakeni ne ta cikin sauƙi…..”
“Inko har duk abinda kika lissafo haka al’amarin zai zama to tabbas dolene Ramadhan ya mutu. Dan kawar da shine kawai zai sakama zuciyata salama
akan Su’adah. Tunda bazamu samesaba to kowa ya rasa shikenan ƙurun-ƙus!!….…”
Wani irin banko ƙofar da akai ne ya dakatar da Aynah data fara dariya, atake sukai diri-diri, gimbiya Su’adah da kanta ke wani irin juyawa tanajin
hajijiya ta shiga nuna adda Asmah da hannu sai dai abinda take son faɗa ya gagara fita. Safina datai wani tsalle ta shaƙo wuyan Adda Asmah ta buga da bango,
hakanne yasa itama Ayna yin kukan kura a kanta ta shaƙeta. Ƴan biki ne suka fara shigowa a guje saboda ihun da Addah Asmah ta buga na azaba, har goshinta ya
fashe jini na zuba……
TAURA HOUSE
Kowa ya hallara su kaɗai ake jira, mai-martaba da ransa ya gama ɓaci yana ƙoƙarin cewa a kirasu sai ga kiran daddyn Aynah ya shigo masa. Cikin
tashin hankali ya shiga ambaton kalmar innalillahi…. Har ƙarshe, kafin ya ajiye wayar ya sanarma ƴan falon da duk hankalinsu ke kansa iya abinda Daddyn
Aynah ya sanar masa. Zaram Ramadhan ya miƙe amma sai Bappi ya dakatar da shi.
“Ina zaka kuma?”.
“Bappi can gidan mana, kanajifa faɗa mizai haɗa Maah da Mom faɗa a duniyar nan?”.
“Koma miye ai zamu sani yanzu, ko kana mantawa da matsayinka a yanzune wai. Koma ka zauna Basheer yaje ya taho da su”.
Babu yanda ya iya ya koma ya zauna kamar zaiyi kuka. Zuciyarsa sai kaikawo take da tunanin mike faruwa? Miya faruwa? Mi akayi?. Hakama sauran kowa