BAKAR INUWA 79
Episode 79_*
………..BAYAN SHEKARU BIYAR
Alhmdllhi abubuwa da yawa sun faru na cigaba a cikin waɗannan shekaru daga mulkin shugaban ƙasa Ramadhan. Ciki harda haihuwa da Raudha ta ƙara har sau uku. Bayan Dawood tayi ƴammata biyu tagwaye da sukaci sunan Saleeha da Zainab. Ta kuma sake Hauwa’u, sai auta da yaci sunan mai-martaba suna kiransa Saraki.
Babu abinda ƴan ƙasa zasuce sai sambarka. Dan kafin shekarun mulkin Ramadhan su kammala ya shimfiɗa manyan ayyukan da har abada baza’a manta da shugabanci irin nasa ba. Daɗin daɗawa bai saukaba sai da ya gyara wasu da yawa a dokokin kundin tsarin mulkin kasar NAYA. Ciki harda dokar shugabanci. Duk shugaban da ya haura shekara sittin bazaiyi mulkin ƙasar NAYA ba koda kansila ne.
A kowace ma’aikata ana son kaso biyu bisa uku matasa su sami rinjayen samun aiki bawai lallai sai a manya ofisoshi ba. Kokai wanene kar’a baka aiki a gurbin da baka cancanta ba. Babu wani ɗan siyasa da zai tilasta ƴan ƙasa amsar zaɓinsa a kowace jam’iyya sai wanda takalawan kasa suka zaɓa. Duk ɗan siyasar daya tara matasa da kayan maye da makamai domin bangar siyasa bashi ba mulki har abada.
Duk shugaban daya hau mulki dolene ya tsaya akan lafiya, tsaro, ilimin ƴan ƙasa da samar da aikin yi koda ta kananun hanyoyi ne ba lallai sai manya ba. Babu wani shugaba da zai gama mulkin gwamna ya koma mulkin majalisa. Daga mulkin gwamna kanada zaɓi na neman takarar shugaban kasa ne kawai koka koma gefe ka saka ido tunda mulkin ba dole bane.
Waɗan nan dokoki sun gamasar sun kuma saka jama’ar ƙasar NAYA farin ciki matuƙa. Aka dinga masa addu’a da fatan alkairi da sambarka. Wasu harda kukansu a randa ya miƙa mulki ga sabon shugaban ƙasa da yaci zabe wanda shima shekarunsa basu wuce arba’in ba kacal.
Ramadhan da Raudha sunyi bankwana da jama’ar kasar NAYA suna kuka da neman gafarar kowa suma harda Abdull mai shekaru tara a duniya daya fara zama ɗan saurayi abinsa. Hakama kanensa ganin iyayensu na kuka da yayansu sai suka dingayi suna dagama al’ummar ƙasar naya hannu alamar bankwana garesu.
(Kai ALLAH sai naji kamar gaske nima sai da nai kuka????????????????)
Koda forma president Ramadhan B. Hameed Taura ya iso Taura house da tawagar masu rakiya talakawa da abokan mulki da iyalansa tarba suka samu mai girma daga su Anne da tsufa ya ƙara kamawa.
Hakama kanensa dake gidan aure kaf suna gidan. Ya rungume su Bappi yana mai zubda hawayen farin cikin sauke nauyi da fatan ALLAH yasa bai taho da hakkin kowa a kansa ba. Sosai mutanen wajen suma suka sake shiga matsar kwalla duk da Ramadhan ɗin ya sakasu wani acan gidan gwamnati kafin su iso nan dama.
Anyi addu’oi godiya ga UBANGIJI, Ramadhan ya sake mika godiyarsa ga su cos da wasu manyan muƙarabbansa da alkairinsu bazai iya musltuwa da baki a garesa ba. Akaci akasha aka sake addu’ar bankwana kowa ya kama gabansa.
Daga Raudha har Ramadhan zazzaɓi suka kwanta har kusan sati, dan har Ramadhan na tsokanar Raudha kodai ciki ne tace ALLAH ya kiyaye tayi kenan. Ganin alhini yaƙi sakinsu Bappi ya bashi shawarar daukar iyalan nasa suje su huta.
Haka kuwa akai, Ramadhan ya tattara ƴaƴansa da matarsa suka wuce ƙasashen duniya shakatawa. Bayan sun ɗan zazzaga suka yada zango a ƙasar America inda yafi wayo. Sun sami tarba ta musamman ga abokansa da abokan kasuwanci ciki harda Sultana datai haƙuri yanzu haka itama yaranta biyu da A.J.
Rayuwar America rayuwace da Raudha da Ramadhan bazasu taɓa mantawa da itaba. Dan kuwa ta riskesune batare da hayaniyar komai ba kasancewar a baya harkokin mulki na yawan cinye lokutansu. Yanzu ko idan yaran suka nema shiga musu hancima tuni suke tattarasu su aika gidan A.J ko Mufeed ko Sultana. Babu abinda suke sai more ƙara’in amarcinsu da basu sami damar yi a baya ba duk da yanzu kam akwai nauyi na ƴaƴa da canjawar abubuwa da yawa na rayuwa.
Dan kuwa dai da gaske Raudha ta koma yar lukuta (kamar bilyn Abdull????????????????lol). Shi kansa mai gayya da aikin ƙibar yayi harda tumbi dake tabbatar da shekarun kuruciya sun fara nisa a garesa, dan kuwa arba’in da biyar yake tunkara yanzu. Yayinda Raudhansa ke tunkarar ashirin da takwas.
Amma yanda ta buɗe ta zama babbar mace sai kace takai talatin da biyar. (Mace kenan ai, da zarar ka haihu kuma ai sai addu’a. Kai kobaka haihunba inhar akace an wuce shekarun nan na ƙuruciya sai sambarka, duk da dai akwai masu karamin jiki da zakagansu duf-duf abinsu masha ALLAH. Koma dai miye kowa da irin halittar da ALLAH ya tsara masa).
Watansu biyu kenan da baro gidan gwamnati, suna dawowa daga America suka sake dawowa Taura house dan Ramadhan baida sha’awar zama wani gida daban sai cikin family nashi, musamman da yanzu gidan ya koma iyayen sune kawai kasancewar kowa yayi aure kanensa dan Muneera ma dai ALLAH ya iyakance mata tayi auren zuwa yanzun, hakama Lubnah tayi itama.
Sai jikoki idan sunzo musu hutun weekend. Shine namiji dole ƴaƴansane zasu kasance a gidan famanet, dan haka ko a yanzu bada wani ra’ayin gina gida ko saye balle tunanin komawa. Ita kanta Raudha nan ɗin yafi mata daɗi tunda tun usil ta rayune a cikin family house.
Wasu abubuwan sun canju, wasu ko ALLAH daya halicci bayinsa akansu kawai ne ka iya canjawarsu. Dan kuwa har zuwa yanzu babu wata shaƙuwa tsakanin Raudha da Gimbiya Su’adah. Sai dai tana nuna son su Abdull kam. Hakan yasa Raudha batajin komai a ranta tunda dai su Abdull jinintane ya wadatar sonsu ya zama ƙauna tsakaninta da surukar tata mai murɗaɗɗen hali.
Sosai Bappi da Anne tsufa ya sake baibayesu, dan Yafendo ma tana fama da jiyya a yanzu. Hakama Inna ta Hutawa ALLAH yay mata rasuwa, yayinda shima M. Dauda ke fama da ciwon hanta sakamakon shaye-shaye sigarinsa. Raudha tsaye take akan maganinsa amma al’amarin nasa dai sai addu’a kawai.
A ɓangaren su Hajiyar Birni itama dai tana fama da ƙafa sosai, dan takai yanzu ko’inama bata iya zuwa. Har ƙasar indiya Raudha tasa aka fita da ita taga likita. Sai dai an samu sauki amma ba’a warke ba abinka da harda tsufa.
Hajiya Mama ma ta koma gidan mijinta na farko, hakam Asabe na zaune lafiya da mijinta da ƴaƴansa. Dan a yanzu hakama shirye-shiryen auren babban ɗan Alhaji Sageer Dogarai da Yasmin akeyi saboda sun dai-daita kansu. Babu abinda Asabe zatace da ALLAH itakam sai godiya. Ga su Fatisa na zamansu lafiya a gidan aurensu suma da yaransu abin sha’awa. Taga ribar yin tuba na gaskiya da dogaro ga ALLAH da maida dukkan lamura garesa.
Ga yan prison kam sai muce ALLAH ya cigaba da rabamu da halayya irin tasu ta masu san zuciya, wasunsu baƙin ciki yasa zukatansu bugawa tuni sun bakunci lahira, dan kuwa da ransu ga Ramadhan na mulkin kasar NAYA amma basu da ikon ko ganinsa sai dai su karanta a jarida, wanda suka kai labari kuwa yanda ya sauka cikin salama ƴan ƙasa na kuka da begensa yay mugun haddasa musu ciwon zukata a dalilin hawan jini suma sukace ga garinku nan.
Irin su Bushira Hamada da suka rage da rai rayuwar kawai ake cikin baƙin ciki dajin garama a mutu a huta da kallon wani takaicin da baƙin cikin rayuwar. dan a yanzu haka Aunty Hannah fama take da jiyya sakamakon zaftare kafa datai da fatanya wajen yin aiki cancer ta shigeta. Har prison ɗin Raudha takai mata likita na zuwa dubata lokaci-lokaci dan su Asabe kan kanje busting nata, itama Raudha ta taɓa zuwa sau ɗaya lokacin suna kan mulki.