Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 79

Bushira Hamada wai zata kashe Raudha aiko taci duka ranar hanun jami’an gidan prison ɗin. Daga lokacin Ramadhan ya hanata zuwa takuma bi maganar mijinta bata sake zuwa ba sai bayan saukarsu taje harda yara suka duba Aunty Hannah ɗin saboda jikin yayi tsanani sosai.


    
      A hutawa ma dai komai Alhmdllhi, idan ka cire ciwon M. Dauda dake fama da shi, duk da dai yana samun kulawa Alhamdulillahi. Sai dai Rasuwar Inna data gitta ce ta girgiza kowa Har Raudha da Ramadhan dama jama’ar Taura Family duka sun mata halacci sunje harda Gimbiya Su’adah a karo na farko. Hakan yama Raudha daɗi, dan bayan sadakar bakwai data dawo har ɗaki taje taima gimbiya Su’adah godiya.

     Rasuwar Inna baifi da watanni biyu ba Fulani ma ta rasu, nanma dai sun girgiza suka dunguma masautar Bina. Inda su Aynah dake zaune yanzu a masarauta itama dai tana fama da ciwo saboda abinda abokan Aminu sukai mata tun wancan lokacin yafi tabata, dan tasan dai Fulanin ce kawai ta rage gatanta kanwarta Zulfah tunda ta samu tai aure bawani zuwa takeba sosai sai hadimai ke dawainiya da ita saboda tsoron Fulani.

Yanzuko babu fulani sai abinda ALLAH yayi kuma kenan tunda Hadiman ba tsoronta sukeba kamar da da idan tazo take takasu kamar itace ta haliccesu. Babanta ko tuni yayi aurensa yana zaune lafiya da matarsa dan harta haifa masa yara biyu maza kyawawa da yaketa alfahari da abinsa. Zulfah dai na tare da shi da matarsa dan ta ɗauketa uwa ita babu ruwanta…….✍
Typing????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button