BAKAR WASIKA 17

“What? Me kake kokarin cewa Talba?”
Talba be kula Momy ba ya kara yin sama ya matsa kusa da Leila.
“I hope ba ke kika shakari yarinyar can ba, kike kokarin kasheta, saboda zafin zai zame miki biyu wahalar zata miki yawa…”
Hawaye ne ya fara saukowa Leila.
“Talba wace irin magana ce wannan? Me kake son fada?”
Juyowa yai ya kalli Momy.
“Momy kin san me nake magana a kai, I’m not a fool na fahimci komai, and i do hope Leila bata da hannu a kokarin kashe yarinyar nan…!”
Yana kawai nan ya sauka a fusace ya fice daga falon gaba daya, Momy ta bishi da kallo, Leila kam ban da hawaye babu abun da take.
“Wace yarinya yake magana akai?”
Zubewa Leila tai a gurin ta fashe da kuka.
“Momy….”
Sai kuma ta kasa karasa, Momy ta hau saman da sauri ta rika Leila suka nufi dakinta.
TALBA POV.
bangarensa ya nufa wayarsa makalle a kunnensa yana ta kiran Ali, sai dai har wayar ta gaji da ringing ta katse Ali be daga ba, zaunawa yai saman kujera ya sake kiran wayar, wannan karon ma Ali be daga ba. Hakan yasa ya dauki keys dinsa ya fito ya shiga motarsa ya fito ya ja motar da karfi, suna ganin ya kunna motar suka bude masa gate. Cikin saurin ya fice daga gidan, yana driving zuciyarsa na raya masa Leila zata iya yin yunkurin kashe yarinyar saboda ta tambayi Ali akan ta, wata kila zata iya zargin wani abu ne a tsakaninsu idan ma bata yi da kanta ba zata iya saka wani yai.
Yana isa asibitin ya faka motarsa ya fito ya mufi hanyar da zata sada shi da office din Ali, kamin ya karasa Office din Ali ya fito daga ward din, yayi mamakin ganin Talba sai dai kamin yace komai Talba ya ce.
“Ali ya yarinyar take?”
“Ba dadi, but she’s still alive”
Wani deep breath Talba yai sannan ya bude office din suka shiga.
“Ya akai abun ya faru?”
Ali ya rufe kofar yana fadin.
“Nurse Karima dai ta fada min cewar tana shiga dakin ta same ta a sume, robar a zagaye da wuyanta kuma an fisge robar hannunta jini ya zuba, yanzu haka sai da muka saka mata robar jini, daman jinin be isheta ba”
Talba ya zauna saman kujera yana dan tunani kaminnya kalli Ali daya kai hannu ya dauki wayarsa yana dubawa.
“Ali lokacin da Leila take tambayarka akan yarinyar nan ta tambaye inda take?”
“Tace dai wace yarinya ce na fada mata tana asibitin mu”
“Ka fada mata number dakin?”
Alinya dago ya kalleshi.
“No miya faru?”
“Ali Leila can do this yarinyar nan bata da zuciya mai kyau….”
“Noooooooooooooooo”
Ali yayi saurin dakatar da shi yana daga masa hannu, domin maganar ta masa nauyi sosai har sai da ya runtse ido ya bude ya kalleshi.
“Look Talba yanzu na fahimci baka son Leila, and it fine, ka ji baka son mutum normal ne amman kokarin dora mata sheri ba zai amfana maka komai ba”
“Na san dalilin daya saka na fad….”
Talba be kasara Ali ya daka masa tsawa.
“Baka da wani dalili, and karka manta Leila yar’uwarka ce ko da babu alakar kauna a tsakaninku be kamata ka jefe ta da wannan ba”
“Ali ba zaka gane ba ne, Leila can do this”
Talba ya sake maimaitawa with full confidence, abun da ya kara fusata Ali.
“Enough Talba, enough. Leila tana da damar da zata yi kishi, ta nuna bakincikinta ko bacin rai akan ka damu da wata, amman for now ka bar Leila ta ji da damuwarka karka kara mata wata”
Ali ya fada cikin tsawa jijiyar wuyansa har tashi take. Talba ya mike tsaye yana kallon Ali cikin wani irin zafin nama.
“So you’re shouting at me…?”
“Yes me ke damunka Talba? Why Leila? What if ita tai kokarin kashe kanta? What if kila ta akan wani abu dabam ake kokarin kasheta?”
Talba ya matsa kusa da shi yana kallon idonsa.
“Don’t fool me, haka nan kawai zata yi kokarin kashe kanta saboda bata son kanta? Bayan ta samu ta fito daga daji? And you already told me babu wanda ya taba zuwa ganinta how could someone know tana a nan? Ali Let me tell you this, zan bincike yarinyar nan and if i find out Leila ta aikata abun nan, sai na bata mamaki”
“And before you do this let me show you something, daga yau ba zan sake kula yarinyar nan ba, and i swear sai ta bar asibitin nan yau, ba zan zuba maka ido ka bata alakarka da matar da zaka aura ba kuma yar’uwarka saboda wata bare ba, kuma a dalilina ka san yarinyar nan and now na fahimci halin da Leila take ciki akanka”
Talba yayi murmushi irin murmushin na bacin rai da mamaki a lokaci daya.
“And remember you said yarinyar bata da kowa”
“I don’t care, idan ma mutuwa zata yi tai mutu, she’s not my responsibility…”
“And for now on she’s my responsibility har sai ta dawo hayyacinta ta fada min komai… And believe me with or without you yarinyar nan zata rayu Doctor Aliyu Muhammad Bukar…”
Talba na fadar hakan ya juya ya nufi kofa a mugun fusace, da mugun karfi yake taka kasar kamar zai fasata tsabar bacin rai, rabon da ya samu kansa cikin irin wannan bacin rai har ya manta. Har ya fito daga ward din sai kuma ya juya ya koma ciki, kai tsaye ya nufi gurin da sauran nurses din suke, mostly sun sanshi domin yana yawan zuwa asibitin gurin Ali kuma gashi sanannen mutum kuma dan babban mutum wato Alhaji Mu’azu Shimkafi, sai dai ba zai iya shadar sunansu duka ba musamman a yau da yake weekend ne ba faces din daya sani ba ne a gurin.
“Who’s Karima a nan?”
“Ni ce”
Ta amsa tana kallonsa.
“Ali ya ce ki dauko yarinyar ki saka a motana zan canja mata asibiti”
“Okay”
Ta mike tsaye ta kira mutun biyu da za su rika mata ita, a gurin ya tsaya har aka fito da ita suka turota a kujera idonta a rufe. Yana gaba suna Karima na biye da shi wata mai aikin shara da dauko files tana rike da file din Aminatu, suna isa gurin Motar Talba ya bude gidan bayan Nurse din da matar suka rikata suka sakata ciki sannan suka rufe motar. Shi kuma ya karbi file din ya bude side dinsa ya shiga ya aje file din a front seat, hakan kawai ya samu kansa da juyawa ya kalli fuskarta, sai tausayinta ya kara kama shi, abun da Ali ya fada masa akanta ya dawo masa, ga kuma wanda yake tunanin Leila na kokarin kara mata.
“Leila…”
Ya furta bayan a dauke kansa daga barin kallon Aminatu, yana jin tsanar Leila na kokarin dasuwa a ransa. Key yai ma motar yai reverse, ya kama hanyar ficewa daga asibitin.
Wata expensive private hospital ya nufa da ita, yana shiga ya nufi emergency, duk da kasancewar yau weekend ne ya samu ma’aikata da yawa a asibitin saboda private hospital ce da suka san aikinsu, sai dai ba kowa yake iya kai kansa ko wani nasa a can ba, sai ya tsaya da kafafuwansa.
Sun karbi Aminatu da gaggauwa da kuma kulawa suka shiga da ita ciki domin bata taimakon da take bukata.
Shi kuma ya tsaya daga waje ya ciro wayarsa dake aljihunsa tana ringing, ganin number Daddy yasa shi saurin picking.
“Hello Daddy”
“Mu’az kana ina? Mun ci abincin rana ba tare da kai ba?”
Ya daga jikin motarsa yana kallon harabar asibitin.
“Daddy ina asibiti”
Sometimes idan yana gurin Ali a asibitin ya kan cewa Daddy yana asibiti, hakan yasa Daddy yai zaton ko yana tare da Ali ne?
“An bata maka rai ne? Could we talk?”
“No Daddy ina wata magana ne mai muhimmanci, bata shafe ka tsakanina ne da Ali”
“Okay”
Daddy ya fada sannan ya kashe wayar, Talba ya cikawa bakinsa iska ya busar a hankali yana kallon Nurse din data doso inda yake.
“Dan Allah kai ne mijin yarinyar nan? Ko dan’uwanta?”
Tsaye Talba yai kamar an dasa shi ya kasa amsa mata.