BAKAR WASIKA

BAKAR WASIKA 18

Ad

_____

Madina ta jimmm bayan da Leila ta gama labarta mata abun da ya faru, gaba daya sai ta ji jikinta ya mutu.

“Yanzu dai ki fita ki ji abun da Ali zai fada miki”

“Zan je yanzu”

“Ki kwantar da hankalinki komai zai wuce, amman da zaki dauki shawarata da kin fadawa Talba gaskiyar komai, barin kashi a ciki baya maganin yunwa Leila, kuma yanzu zaki yi ta samun rashim fahimta a tsakaninku ne”

“Madina wannan sirina ne, Momy ma bata san na fada miki ba, amman na fada miki ne saboda na yarda da ke”

“Babu wanda zai taba jin wannan maganar daga gareni Leila, amman ina baki shawara ne akan abun da nake ganin zai zame miki masalaha”

“Yanzu dai bari na tafi Ali yana jirana”

“Okay”

Leila ta aje wayar sannan ta sauka saman gadon ta dauki wani karamin mayafi ta rufe kanta, sannan ta saka talkaminta ta nufi kofar fita idonta a kumbure saboda kukan da ta sha.
Ko da ta sauko falon babu kowa, dukansu suna bangaren Daddy, yan aikin Momy kuma Momy bata basu damar zama a falonta hakan yasa idan ba wani aikin zasu ba abu ne mai wahala ka gansu a main house din kullum suna BQ. A hankali ya bude kofar falon ta fita gabanta na faduwa, domin ji take kamar zata yi arba da Talba ne, domin a yanzu bata son ganin fuskarsa, ba dan bacin rai ba sai dan bata da amsar tambayar da zai mata. Tun kamin ta karasa gurin gate din police din ta bude mata karamar kofar ta fice, tana fitowa ta ga motar Ali fake sai ta nufi inda motar take. Ali na zaune cikin motar yana kallonta har ta karaso gaba daya sai ya ji tausayinta ya kama shi, a da can yana bata laifi kamar yadda yake bawa abokinsa sai dai a yanzu ya fahimci abokinsa ne mai matsala ba ita ba. Bude motar tai ta shiga sannan ta rufe ta kalleshi da idonta da suka kumbura.

“Ali”

Ad

Sai da ya sauke wani dogon numfashi sannan ya amsa mata.

“Na’am Leila, ya kike?”

Tambayar ya take da yai sai ta ji kamar ya tsokano mata kukanta, a take hawaye ya cika idonta.

“Ba Kalau ba Ali, ba Kalau ba”

“Na sani, abokina yayi rashin tunani, amman ban dauka zai miki magana ba, a thought ya bar abun a ransa ne kawai, sai dai faga lokacin dana kira ki na ji yanayinki, sai tausayinki ya kama ni, and now na fahimci irin halin da kike ciki”

Ya karasa yana kai hannu ya ciro tissue ya mika mata, sai ta karba ta share hawayenta.

“Sometimes ina kasa fahimtar waye Talba, abokinka yana da wahalar sha’ani Ali, taya wanda zaka aura zai zarge ka da kisa? How? And Why? Saboda na nuna kishina? Talba be dadin zama wani lokacin”

“Na sani, amman ban dauka abun zai kaishi haka ba”

Cewar Ali yana kallonta gaba daya zuciyarsa ta cika da tausayinta, domin gani yake Talba baya sonta ita ce kawai sonsa ke dawainiya da ita.

“And i respect your decision na cewar ba zaki auri Talba ba har sai ya canja”

Juyowa tai ta kalleshi da kyau.

“Dan Allah zaka fada min abun da ta faru da yarinyar?”

A takaice ya labarta mata komai na yadda aka samu yarinyar, sai dai be fada mata cewar Talba ya dauke ta daga asibitin ba, haka ma be fada mata cewar sun samu tsabani ba, domin yana ganin kamar sirrinsa ne da be kamata kowa ya ji ba.

“Amman me zai saka wani yai mata haka?”

“Ni ma ban sani ba, kuma a iya binciken da na yi wani be shigo ba, so dole dai sai ta farka zata iya fada mana yadda komai ya faru”

“Yanzu tana asibitinku?”

“No na canja mata asibiti, and i am here to apologize saboda ni na janyo komai, Talba be san yarinyar nan ba, ni na hada shi da ita da neman ya taimaka mata saboda yarinyar tana bukatar taimako, amman ban yi tunanin abun zai zama na rigima haka ba”

“Baka da laifi, na san ka yi ne da kyakkyawar niya, be kamata ka bada hakuri ba”

Yayi shiru na wani lokacin kamin ya kalleta ya ce.

“Amman Leila kin yi wani abun ne da zai saka Talba ya zargeki da taba yarinyar nan?”

“Ban yi komai ba, amman kasan a gurin abokinka kullum nice mai laifi, kawai dai na fahimci wani abu… Talba baya so na ni ce kawai na mutu da kaunarsa, wanda yake sonka ba zai maka haka ba, ko da gaske na aikata zai nemi hanyar kare ni ne, ba ya tunkare da wannan laifi mai girma ba, abun akwai ciwo”

Ta karasa wasu hawaye masu zafi na sauko mata, har cikin ranta tana fadawa Ali abunda ta fahimta ne akan zamantakewarta da Talba. Ali ya kawar dai yana jin irin tausayinta na kara kamashi.

“Ada can na dauka miskilancinsa ne ya saka yake min abun da yake min, amman a yanzu na fahimci kauna ta ce babu abunsa, kawai ya amince ne saboda ba zai iya cewa Daddy a a ba”

Ta runtse tana kokarin fashewa da kuka.

“Kabir yana da fada min gaskiya amman na kasa ganewa, saboda kaunar Talba ta cika min zuciya amman yanzu na fahimta…”

Ali yayi saurin daukar ruwan dake cikin motarsa ya mika mata.

“Please sha ruwa”

Sai kuma ya dauko tissue ya mika mata.

“Ki daina damuwa dan Allah, kukan nan yayi yawa idonki har ya kumbura, me yasa zaki damar kanki akan Namiji?”

Sai ta kalleshi hawaye na sauko mata

“Talba be taba min haka ba, na gode”

Ta fada sannan ta karba ya share hawayenta ta bude ruwan ta sha.

“Ki je ki huta, karki saka damuwar komai a ranki komai zai wuce, kin san idan ya fusata yana aikata abubuwa amman zai sauko and ina tabbatar miki zai baki hakuri”

Ad

_____

1 2 3 4Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button