BAKAR WASIKA 17

“Tana bukatar jini da gaggauwa”
“A ina zamu samu?”
“Lab amman for now za mu bincika mu ga ko za’a samu jinin da zai dace da nata”
Ya gyada mata kai a hankali cike da natsuwa, sannan ya bi bayanta suka nufi cikin ward din, ita ta nuna masa dakin da suka saka Aminatu. Ita ta fara shiga shi kuma ya bi bayanta ya tsaya jikin kofar yana kallon fuskar Aminatu dake ta bachi kana gani kasan bata san inda take ba. Nurse din ta yi abun da zata yi ta fita Talba yana tsaye jikin kofar idonta akan Aminatu, takawa yai a hankali ya karasa kusa da gadonta still ya kasa kauda idonsa akanta.
“You need to survive”
Ya furta yana jin kamar ya tashe ta ya tambaye ta waya mata haka, kuma ayi sa’a ta amsa masa cewar Leila ce. Yana tsaye akanta har na kusan mintuna talati, sai ga nurse din ta dawo tare da likitan daya karbi Aminatu a dazun.
Sake dubawa yai sannan ya kalli Talba.
“Ba mu da kalar jininta a yanzu, sai kaje babbar asibiti ko kuma ka samu wani daga familynta idan zai iya bada jinin”
Uffan Talba be ce ba har sai da Likitan ya nufi kofar fita.
“Ko zaka iya gwada nawa? O ne”
Likitan ya juyo ya kalleshi.
“Yes why not amman zamu fara maka test mu tabbatar baka dauke da kowace irin cuta gudun samun matsala”
Ya daga masa kai kamar an masa dole, sannan ya bi bayan Nurse din dake nuna masa kofa.
“Bismillah Malam”
LEILA POV.
Wani irin kuka take wanda ita kanta ba zata iya fadar dalinlinta na yin kukan a yanzu ba, na zargin da Talba yake mata ne ko kuma na laifin ne da yake kokarin dora mata? Taya zai zarge da da abun da bata san wanzuwarsa ba? Miyasa ma zai yi maganar wata yarinyar a gabanta? Ko kuma dai tana kukan ne saboda zuwan Shamsu? For now she can’t tell, all what she know is dukansu is painful, daga zargin har zuwan Shamsu har zancen yarinyar da Talba yake.
“Tun dazun kike ta kukan nan? Haka zaki yi ta yi a gaban mutane ki daure kanki?”
Momy ta fada cike da tausayin yarta.
“Wai wace yarinya ce ma yake magana akai?”
A take ta amsawa Momy hawaye ma sauko matan
“Wata ce, wata yar gudun hijira ce”
“Yar gudun hijira kuma? Shine har zai zarge ki da kashe ta? Ke kin santa ne?”
Ta daga kai tana goge hancinta.
“Na santa amman Wallahi ban ma taba ganinta balle har na yai yunkurin kasheta? Miyasa zai zarge ni?”
“Ke kika bashi fuska ai! Kina ta son bada kofar da za a zarge ki, koma dai miye ai be kamata yai wannan tunanin ba, and ko da kin aikata be kamata ya sameki kai tsaye da maganar ba!”
Momy ta fada a fusace, sannan ta mike tsaye yana wani kashe ido.
“Karki fito cin abinci, saboda Daddynku zai tambaye dalilin danuwarki, so ki zauna a nan zan fada masa kanki yana ciwo”
Leila ta daga kai, sai Momy ta juya ta fice daga dakin tana mamakin yadda Talba yake son sauyawa.
after like 40 minutes da fitar Momy wayar Leila tai ringing, hannu ta kai ta dauka tana duba number Ali dake kiranta, da kamar ba zata daga ba sai kuma ta daga wayar ta kara a kunnenta tai shiru tana sauraren abun da zai fito daga bakinsa.
“Kuka kike yi ko?”
Ta daga masa kai kamar yana gabanta, wasu hawayen na sauko mata. Be damu da yaji abun da zata fada ya sauke ajiyar zuciya daga can cikin wayar.
“I know na san abun da ya faru, can we talk? Gani a hanyar gidanku akwai maganar da nake son fada miki, please ki daure ki fito zan tsaya a gate”
“Okay”
Ta amsa masa tana jin wani sabon kuka na taso mata, sannan ta aje wayar ya lumshe ido, fuskar Baaba ce ta fara mata gizo, hakan yasa tai saurin bude idon ta mike tsaye ta nufi gurin windows din dakinta dafe kai wasu hawaye na sauko mata.
Khadeeja Candy