JIDDATUL KHAIR

JIDDATUL KHAIR 49

Ad

_____

Murmushi kawai Jiddah tayi bata ce komai ba, Ahmad bai kuma ce mata komai ba shi ma, suna isa wani babban pharmacy yayi parking yana kallonta yace “I am coming let me get u pain reliever, Umma tace kina ciwon ciki ko?” Ta gyada masa kai ya kashe motar ya sauka ya shiga cikin pharmacy din, ba a wani dau lkci sosai ba ya fito da ledan magani, ya shiga motar yana kallonta ya ajiye mata kusa da ita yace “Ko kina bukatar wani abun daban, akwai Supermarket a nan…” Ta girgixa kai tace “Aa bana bukatar komai”

Yace “Ohk” sai da suka hau saman titi ta d’an kallesa amma bata ce komai ba, ganin haka yace “Say what is in ur mind Jiddah, be free with me and take me as ur elder brother” Ta sunkuyar da kanta a hankali tace “Ni yanxu baxan iya xuwa in ga Baabarmu in gaisheta ba?” Da d’an mamaki yace “Baabarku? Me xaki yi mata idan kinje, ko kuma me xata maki ita?” Shiru tayi bata ce komai ba, yace “Babu amfanin xuwa wajenta a yanxu dai Jiddah, idan kinyi hakuri wataran babu wanda xai hanaki xuwa gareta, when the rightful time comes da kanki ma xaki je ba sai wani ya kai ki ba kin ji?” Cikin sanyin murya tace “Toh, amma kuma akwai wata tsohuwa a layinmu ana ce mata Iyah, tana da kirki sosai, ko ita ma baxan iya xuwa in gaisheta ba?” Yace “Baki tunanin xata gaya ma Baabarku kin je?” Ta girgixa kai da sauri tace “Aa baxata fada ba, ai ita ba haka take ba, ita ce fa ke taimakona lokacin da nake gun babarmu, har abinci tana bani idan tana da shi” Yace “Toh yanxu kina son a kai ki can kenan?” Ta gyada masa kai a hankali, ya d’an yi shiru yana ci gaba da driving dinsa, kallon agogon wrist dinsa dake nuna karfe hudu da wani abu yayi,

[indeed-social-locker sm_list=’fb’ sm_template=’ism_template_9′ sm_list_align=’horizontal’ sm_display_counts=’true’ sm_display_full_name=’true’ unlock_type=2 locker_template=8 sm_d_text=’

This content is locked

Share This Page To Unlock The Content!

‘ enable_timeout_lk=1 sm_timeout_locker=1200 reset_locker=1 locker_reset_after=1 locker_reset_type=’days’ ism_overlock=’default’ ]

sannan yace “Kinsan me Jiddah?” Jiddah na kallonsa ta girgixa masa kai, yace “Ki bari ko gobe da daddare in kai ki, tunda kina gidana, i think it will be more safer…” Jiddah tace “Toh nagode” Yayi mata murmushi kawai. Suna isa gidansa yayi parking a space din parking sannan ya sauka motar ita ma ta sauka, tana biye da shi suka shiga gidan, Xaunawa tayi a parlor shi kuma ya wuce bedroom dinsa sanin Ramlah na can

tana bacci, xai shiga dakin sai gata ta fito, ya d’an buda ido yace “Ashe ba bacci kike ba” Ta turo baki tace “Ina ice cream din?” Yace “Ohh kinga na mance wllh, I’m sorry anjima xan fita sai in siyo maki, fito ku gaisa da Jiddah” Ramlah tace “Da gaske?” Yace “Ehh” a tare suka dawo cikin parlon, Ramlah ta xaro ido tace “Lallai sis Jiddah ce yau a gidanmu, ashe xa ayi ruwa da kankara” Jiddah tayi murmushi tace “To ai ina

Ad

xuwa” Ramlah ta karaso ta xauna kusa da ita tace “Aa sau biyu ina ga kika taba xuwa, ina fa sane, to ya su Umma?” Jiddah na murmushi tace “Lafiya lau, ya jiki?” Ramlah tace “Naji sauki Alhmdlh” mikewa tayi ta dau jakar Jiddah tace “Mu je ciki to” Jiddah ta mike ta bi bayanta, Ramlah ta kai ta dakin visitors, sosai Ramlah taji dadin xuwa Jiddah gidanta, Ramlah tace “Gashi ni banyi girki ba wllh, ko in dafa maki indomie kafin a daura dinner?” Jiddah tace “Daga gida fa muke, ai na ci abinci” Ramlah tace “Toh bari in kawo maki ruwa” Bata jira cewar Jiddah ba ta fita dakin, sai da Ramlah ta daura ruwan shinkafa a gas snn ta dau tray ta daura Chivita drink da ruwan gora sai glass cup ta dawo daki ta ajiye tana kallon Jiddah tace “To ga

ruwa ki sha sis Jiddah” Jiddah ta d’an yi murmushi tana kallon hancinta dake shige da na Abuturrab, har idanuwansu iri daya ne, dama kuma duk a cikinsu ita tafi kama da shi, Ramlah ta xauna tana ta jan ta da hira, tun Jiddah na shiru shiru har dai ta fara biye mata, lkci daya Ramlah tace “Ohh na manta na daura ruwan shinkafa a gas, bari in xuba shinkafar in dawo” Jiddah tace “Toh bari in wanke in xuba maki” Ramlah ta nufi kofa da sauri tace “Aa wllh… Ai ba wani aiki bane” Daga haka ta fita, xaune ta tadda Abuturrab a

parlor da Ahmad, Ta d’an buda ido sai kuma ta washe baki tace “Yaushe ka xo yaya?” Karasawa tayi ta duka gefensa tace “Welcome Yaya, ina yini?” Ya kalleta yace “Lafiya lau, ya gida?” Tace “Alhmdlh, ya aiki?” Yace “Fine Alhmdlh” mikewa tayi ta wuce kitchen, Ahmad dake shafa beard dinsa yana kallon Abuturrab yace “ina jin ka great Captain” Abuturrab yace “Kana jina na me wai, kai fa idan kaga mutum na neman

abu a wajen ka ka dingi walakantasa kenan” a takaice Ahmad yace “Toh ka tafi asibiti kawai” Abuturrab ya dinga kallonsa, Ahmad yace “Yes, nasan kana da mata baxan rubuta maka wannan maganin da kace ba, ko dai Hygiene din ne bai kai yanda kayi expecting ba? Abu d’an sauki tunda kana da wadata sai ka kara aure kawai” Da dariya Ahmad ya kare maganar, Abuturrab dai ya kasa ce masa komai, Jiddah ce ta fito parlon rike da tray din lemon da Ramlah ta kai mata don xuwa kitchen ta taimaka ma Ramlah da girkin da tace xata yi, Tsaye tayi bakin corridor din dakunan ganin Abuturrab a parlon kafin ya ganta ta juya da sauri har tana tuntube ta koma ciki ta shige daki ta kulle kofar gabanta na faduwa sosai, Abuturrab ya kalli

direction din don rufe kofa kawai yaji, can ya kalli Ahmad yace “Who is there?” Ahmad yace “Bakuwa muka yi” Abuturrab yace “Ohk” Ramlah ta fito kitchen ta ajiye masa ruwa da drink tace “Amma yaya ba yau xaka koma kano ba ko, naga yamma yayi” yace “Gobe da safe in sha Allah” Yana fadin haka ya dau bottle water daya ya bude ya sha ya mayar ya ajiye sannan ya mike yace “Sai anjima….” Ahmad dai sai murmushi yake yana kallonsa, Ramlah tace “Yaya ka tsaya ka ci abinci mana pls…” Yace “What are u

Ad

_____

1 2 3 4Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button