BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 18

‘Ubanta ne kai?’

Shine reply din da yai ma Ali sannan ya aje wayar ya busar da iskar bakinsa. Kabir ya kalleshi sannan ya kalli Amal dake zaune tana kallonsu dama haka take idan ta lura da ba a zaune kalau, so that ta samu abun tseguntawa Daddy.

“Amal je ki yi bachi mana”

Kabir ya fada, sai ta make kafada.

“Bana jin bachi yanzu”

A take ya zare mata ido, hakan ke nuna ba da wasa yake ba, ya saba wasa da ita sosai sai dai a duk lokacin da yake serious magana da ita ta san yanayinsa. Mikewa tai tsaye tana kallon Talba.

“Ya sai da safe”

Ta murgudawa Kabir baki sai ya kyalkyale da dariya yai mata gwalo.

“Daddy’s noy could we talk?”

Talba ya kalleshi.

“Leila ta fada maka ne?”

“Nooo Amal dai ta shinshino ta shinshina min”

Talba ya dan yi murmushi kadan yana kallon hannunsa.

“Na bada jinina yau”

Kabir ya duba shi duba na mamaki, ba zai ce ya san dukan abun da Talba yake yi ba, amman be taba jin yace zai bada jininsa ga kowa ba.

“Something new…”

Talba yayi murmushi.

“Yeah…. I feel like….. ”

Sai kuma yai shiru kamar mai tunanin abun da zai fada.

“I feel honour.. I mean it was a great joy…. to do….something like this”

A rarrabe yai maganar and he is very excited, he can’t tell why amman yana jin yayi abu mai kyau.

“Yeah at least wani zai rayu da jininka, and mutumen nan ba zai taba manta ka idan ya sanka, idan kuma be sanka ba, kai zaka ji cewar wani yana can yana rayuwasa saboda ka taimaka masa da jininsa ko da kuwa siyarwa kai balle kuma ace kyauta ka bada, more especially ace mutumen nan yana cikin yanayi na bukatar jini tsakanin rayuwa da mutuwa…”

Talba yayi shiru yana sauraren kalaman Kabir, sai kuma ya soma tuna abun da ya faru a yau. Juyowa yai ya kalli Kabir.

“Idan mutum ya suma zai dauke ki awa nawa kamin ya dawo hayyacinsa?”

“Is depend on yanayin suman, ko kuma irin kulawar daya samu, but most wadanda tsoro yake saka su suma ko damuwa, ba su cika farkawa da wuri ba kamar wanda rashin lafiya ta saka shi suma, kuma ya danganta da kalar suman da mutum yai”

Shiru Talba yai alamar nazari sannan ya sake tambayar Kabir.

“Amman me ke saka mutum baya kuka da murya sai hawaye, kuma ba ya magana, baya cin abinci baya ma bude bakin”

Kabir ya aje spoon din da yake cin abinci da shi ya dauki ruwa ya sha.

“Depression… Damuwa tana saka wannan har fiye ma, tana saka hauka, rashin lafiya and so on, indai har ba wai mutum ya daman can haka aka haife shi ba, daga baya ne ya sauya gaskiya damuwa ce, tana tsoro tana saka mutum ya rika ganin abu yana imagination ko kuma zuciyarsa ta raya masa ya aikata ko ta saka shi hauka ko ya rika abu kamar mai aljannu, tana saka yawan mantuwa ko surutu ba akan abun da ake magana akai ba, you know komai n jikin dan’adam yana da limit din abun da yake iya dauka, so idan abun yai yawa ko yai kadan zaka tarar akwai irin illar da yake haifarwa”

Silently Talba ya sauke ajiyar zuciya.

“Idan mutum yana son yayi magana da mai irin wannan abu kamar ya tambaye shi wani abu ya zai yi?”

“Ya zai yi kuwa? Most important thing is ka yi kokarin cire wannan mutumen a damuwa, idan wani abu yake so ka sama masa, idan tsoron wani abu yake ka nuna masa babu abun da zai same shi kuma zaka bashi kula, ka sake jikim da shi kana bashi kulawa kana nuna masa far’a da walwala kana dauke masa hankali daga damuwar, kai ta kokarin ganin ka faranta masa rai, da haka da haka zaka ga ta saki jiki da kai, ka yi ta cusa kanka kana bata abinci tun bata ci har ta fara ci”

“Idan kuma ya ki fa?”

“Taki dai… Zata ma ci idan ta ji yunwa, idan ana saka mata maganine a ruwa na abinci ko kuma ana bata ta hanci a daina, as long as zata iya tashi zaune ko ta kwanta bata bukatar irin wannan maganin, a kyaleta ta wuni da yunwa idan ta ji babu komai a cikinta zata karbi abincin idan an bata, da haka zata saba ta rika ci, amman a yanzu ai an hanata jin yunwa ne, kuma ace ana son ta ci abinci?”

“But he cant walk fa”

“That one is different, maybe damuwar ce ta haifar mata da hakan ko kuma wani matsalar dabam, amman rashin lafiyarta ba zai zama da matsala a cin abincin ta ba, indai ba wai tana kan wani magani da aka dorata ba ne, shi ma kuma sai dai ace ba zata ci wani ba wani zata ci”

Talba ya yunkura da zimmar tashi sai Kabir ya kalleshi ya ce.

“Ita ce yarinyar?”

Da ido Talba yai masa alamar question mark, sai ya karansa tambayarsa.

“Yarinyar da kake zargin Leila tana kokarin kashewa?”

Talba be ce masa komai ba ya fara tafiya.

“And do you really think Leila zata iya wannan abun?”

Tsayawa Talba yai ya juyo ya kalli Kabir.

“Amal ta baka labarin Baaba?”

“No amman Momy ta fada mana yan’uwanta sun zo sun dauke ta right?”

“Yes amman dazun nan jikanta ya zo nemanta, so kai tunani akai”

A take Kabir ya cika da tsananin mamaki, Talba kuma ya juya ya fice daga falon. Bangarensa ya nufo kamin a karasa ya cire agogon hannunsa, sannan ya kai hannunsa na hagu ya bude kofar ya shiga, tafiya yake kamar baya son taka kasa ya karasa bathroom dinsa ya jefar da wayarsa saman gado, ya cire tufafin jikinsa ya daura tawul. Samun kansa yai da karasawa gaban katon madubin dake dakin wanda ke nuna iya tsayin mutun. Tsaye yai yana kallon kansa kamin ya kai hannu ya shafa kirjinsa zuwa cikinsa sai kuma ya dawo da hannun saitin inda zanen kirjinsa yake yana tabawa.
Motsin shigowar mutum da yaji ne yasa shi juyowa da sauri domin ya san ba kasafai ake shigowa bangarensa ba, Momy ba tai musu wannan tarbiyar ba, ta shiga dakin juna barkaita sai dai idan da wani dalilin. Takawa ya fara yi kamin ya isa bakin kofar Bathroom din Leila ta shigo, tsaye tai cak tana kallonsa daga kasa zuwa sama, wani irin bugawa zuciyarta tai da karfi a lokacin da idanuwanta sukai arba da faffandan kirjinsa. Tun da take a rayuwarta bata taba ganin Talba babu riga ba sai yau, duk kuwa da kasancewar a gida daya suka tashi sai dai baya bayyana mata siraicinsa kamar yadda ita bata taba nuna masa nata ba sai dai dan abun da ba a rasa ba, kamar saka damammen kaya ko wando da riga, sai dai rika hannunsa ko taba shi ba wani abu ba ne a gurinta kamar yadda shi ma be dauke shi komai ba.

“Ya akai?”

Ya tambaya yana kallonta, ba karamin jihadi tai ba na ganin ta daidaita natsuwarta, sai dai hakan be hana numfashinsa yin nisan kiwo ba na tsawon dakiku, ta dauken kai tana kokarin dawo da numfashin a hankali.

“Yarinyar ta fada maka wanda yai mata haka?”

“Kina da wata maganar ne bayan wannan?”

Juyowa tai ta kalleshi.

“Ita wannan maganar ba mai muhimmanci ba ce?”

“Mai muhimmanci ce a lokacin da ta fada min cewar ke ce ko ba ke ba ce, and kuma idan na gane gaskiyar komai a game da Baaba”

“Duka biyun ban aikata ba, miyasa baka yarda da ni ba? And me zai saka ka zarge ni da kisan yarinyar da kai ma basan san ta ba”

“She can’t walk she can’t talk, depression yana damunta, and now idan na gano da hannunki a ciki, i swear ba zan raga miki ba, you have no idea what she’s going through”

Ta kara matsowa kusa da shi tana kallon idonsa.

“I don’t care, she can’t talk or walk is not my business, ta mutu ko ta rayu be dame ni ba, ina ta fito ina zata je me ya faru da ita duka ba matsala ta ba ce, all what i care is us….we… I mean us… Just us…”

Yanayin yadda tai maganar ya bayyana bacin ran dake tare da ita, shi ma kallonta yake ido cikin ido yana kokarin hana zuciyarsa tsanarta. Sai da ta gama yawo da idanuwanta a fuskarsa sannan ta juya ta fice daga dakin a fusace. Tana dawowa dakinta ta dauki wayarta ta kira Madina ta san is late amman tana son ta yi magana da ita mai muhimmanci.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button