BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 18

“Hello Leila”

Madina ta yi picking.

“Madina fada yadda ake mantawa da mutum”

“Ban gane ba”

“So na ke na manta da Talba, na cire shi a raina gaba daya na manta da shi”

Wani irin murmushi ne ya kawata fuskar Madina, ta yi saurin aje kofin ruwan dake hannunta.

“Amman miyasa?”

“Na gaji ba zan iya ba, sai na nuna masa ni din mai tsada ce kuma na nuna masa he is nothing to me”

“Shikenan zan zo da safe, wannan maganar ba ta waya ba ce”

“Okay ina jiranki”

Leila ta katse wayar, sai Madina ta rike wayar tana kallo, rabuwar masoya ba abu ne mai kyau ko dadi ba, sai dai ita ya zo mata a dabam domin ta samu kanta cikin farincikin jin abun da Leila take kokarin aikatawa.

BATURIYA POV.

Kamar yadda Ramlee tai mata alkawarin kawo mata kayan mata da zata sha a jiya, ta kawo mata su cike kamar wanda zata sara ta kai su wani gurin, ita ma kanta ta yi mamakin tarin hakin mayen da Ramlee ta kawo mata, wanda za a hado da madara ko zuma a sha duka ta siyo mata madarar da zumar, yadda ta ware kudi ta siye mata kayan matan sai ka rantse da Allah yarta ce.
Hakan yasa ta bude wardrobe dinta ta saka su ta rufe da makulli, idan zata sha sai ta bude ta debo ta sha ta rufe, ko Sultan bata yarda ya gani ba balle kuma Faruq uban gayya.

Bayan ta gama gyara gidan yayi tsab ta dora girkinta da wuri, sannan ta shigo falonta ta dauki wayarta ta kunna data ta fara chat. Zata yi reply wani sako kiran Fahat ya shigo wayarta, da sauri tai picking ta kai wayar a kunnenta.

“Hello”

“Yan mata ya kike?”

“Lafiya kalau, sai marmarinka”

“Uhm mmn Marmari kamar gaske, ke da kin ki bari ma na zo mu gaisa, sai kwana kwana kike min”

“Ai na fada maka gidamu ba za a bar ni ba, ba a barin mu zance gaskiya”

“Amman ai kin yi girman da ya kamata ace ana barinki zance Fee’at”

Ta lumshe ido tana jindadin yadda ya kira sunanta, daman haka take so ba kamar yadda Faruq yake kiranta da Rafi’a ta yi complain har ta gaji, sai yace mata shi ba ba ta soyayya yake ba, ta neman kudi yake da abun da zasu ci.

“Ba zaka gane ba ne”

“Na gane, kuma suna da gaskiya, wasu iyayen basa barin yayansu su na kula samari barkatai, amman idan kin amince min zan iya sakawa a zo a nema min izinin magana da ke har mu fahimci juna”

“Da gaske?”

Ta tambaya tana tashi zaune daga kwance da take.

“Wallahi kuwa, Fee’at ni fa da gaske nake aurenki zan yi, ba da wasa na zo ba”

“Uhmm”

“Allah kuwa, Momyna ta dade tana min maganar aure, ansha kai ni gurin yan mata da yan’uwa amman wallahi ban taba jin wanda tai min ba, amman ke ina ganinki na ji wani abu akanki Fee’at you’re different…”

Ba karasa maganar da yake ba ta yanke wayar ta kasheta gaba daya sakamakon jin ana kwankwasar gidan. Fitowa tai ta isa gurin kofar ta bude sai tai arba da Faruq yana dauke da Sultan.

“Har kun dawo”

Sai da yai kamar kar ya amsa mata sai kuma ya amsa.

“Eh, Sultan shiga ciki”

Ya karasa yana sauke Sultan dake rike da ledar kifi kasa. Sannan ya juya ya

“Zan tafi shago”

“Allah ya tsare”

Ta fada kamar ba ita ba har sai da ya juyo ya kalleta, rabon da tai masa addu’a har ta manta.

“Ameen”

Ya amsa sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa, ita kuma ta maida kofar ta rufe taja hannun Sultan suka nufi cikin gidan tana tunanin maganar da Fahat yai mata.

‘Amman da gaske yake zai aure ni? Ko kuma dai wasa yake? Amman ai be san na taba aure ba, idan na fada masa gaskiya zai yarda ya auri bazawara?’

Ita kadai take ta haukanta ta saka wannan ta kwance wacan, gaba daya sai hankalinta ya tattara ya koma gurin Fahat tana ta ayyana irin rayuwar da zata yi, kasancewar sa mai kudi kuma dan masu kudin.

“Momy Mama tace a gaishe ki”

Sultan ya fada yana zaunawa ya bude ledar kifin.

“A hanya Dady ya siya min, yace na ci rabi na baki rabi”

Ba ta ma kula, gaba daya hankalinta yana gurin Fahat.

“Amman fa na masa karyar arziki, wata kila yana min kallon yar masu kudin ne”

Sultan ya kalleta.

“Momy waye?”

Sai a lokacin ta lura da a zahiri tai maganar ba a badini ba.

“Ba kowa ba ci kifinka, ga abinci can akan wuta idan yayi zaka ci kaji”

Ya fada mata kai ita kuma ta shiga uwar daka ta dauki wayar ta kunna, sai ga sakon Ramlee ya shigo mata.

‘Ki sha kayan nan da yawa, yace yana son ku hadu da gobe, na kira wayarki ban samu ba, idan kin gama karantawa ki goge sakon’

Dundundun ta ji gabanta yayi duka uku uku, ba dan bata saba haduwa da mazan da ba muharramanta ba, sai dai wata kila saboda wannan haduwar ta daban ce, saboda zata aikata sabo ne alhalin tana da aure da kuma da, ga kuma karamin ciki a jikinta.
Saurin goge sakon tai kamar yadda Ramlee ta bukata, sannan ta mike tsaye ta isa bakin kofar dakinta ta tsaya tana kallon Sultan dake ta aikin cin kifinsa hankali kwance, damuwa ce ta bayyana a fuskarta, duk wani dauki da take na son a bata kudi sai ta ji ya ragu, domin bata taba aikata alfasha ba, sai a wannan karon ne zata gwada. Juyawa tai ta koma cikin dakin tana busar da iskar bakinta.

Khadeeja Candy

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button