BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 20

“Madam hop kin shirya”

“Na shirya, ke kawai nake jira”

“Haka na ke so, ba wasa ganin nan nima na kusa karasowa”

“Sai kin iso”

Ta aje wayar tana murmushi, ita ma kanta ta san ta yi kyau, sai kamshi take zubawa kamar sabuwar amarya, kamin Ramlee ta iso ta shafa hoda ya kai sau shida, turare kan ba adadi irin feshin da take masa.
Tana jin sallamar Ramlee ta dauki wayarta da jakarta ta fito waje da sauri.

“Wow yanzu kika fito da sunanki n Baturiya, amman mutumen idan ya ganki sai ya rude”

Baturiya ta yi dariyar jindadi.

“Da gaske”

“Wallahi kuwa, sam sam baki dace da Faruq ba, ke din matar manya ce, amman fa karki fada masa cewar kina da aure domin na ce masa ke din bazawara ce”

“Ke ma dai da wata magana, ya za’ayi na fada, Allah dai ya sa inda zamu je ba public place ba ne, domin akwai wadanda bana son su gan ni”

“No guest house dinsa ne, muje dai kar mu bata lokaci”

“Amman kin san me? Idan na fita da kwaliyar nan haka ina kamshi mutanen unguwa za su fara saka mana ido”

“To ya zamu yi? Ke dai ina ruwanki da mutane ne wai?”

“Aa bari dai a saka hijab da nikab idan na je can sai na cire a motarki”

“Haka yayi yi sauri”

Ta juya ta koma dakinta da sauri ta dauko katon Hijab ta saka tare da niqab sannan fito ta rufe gidan.
Tun daga yanayin ginin unguwar da shuke shuken zaka san cewa unguwar manyan mutane ce, a gaban wani katon gate suka faka Ramlee tai horn Mai gadin ya leko tai magana da shi sannan ya bude mata ta shiga, a harabar gidan tai fakin ta ciro wayarta ta kira shi.

“Alhaji mun iso”

“To yayi Kyau Hajiya Ramlee a barta ta dan huta gani a hanya, garin sauri ma na kade wasu amman dai na gama komai zan iso yanzu”

“To yayi Alhaji sai ka iso”

Ta aje wayar sannan ta labartawa Rafi’a abun da ya faru da shi.

“Kuma ki sake jikinki ki kwashi arziki, domin yana son ki Wallahi na fada miki hotonki kawai ya gani amman duk yabi ya rufe balle kuma ce ya yi arba da ke”

“Inshallah ba zan baki kunya ba”

“Yayi kyau, haka nake son ji, yanzu mu shiga ciki na nuna miki falonsa sai n fito na bar ku ku sha shagalinku”

Ramlee ta fada tana murmushin jindadi. Sai Baturiya ta cire Hijab din da Niqab ta kai hannu ta bude motar wayarta tai kara.

“Allah yasa ba mijin nan naki ba ne”

Cewar Ramlee tana tabe baki, fasa fitar Baturiya ta yi ta ciro wayar daga jakarta ta duba.

“Shi ne kuwa, ban san mi zai ce min ba, ko kuma ya dawo gida ne oho”

“Karki dauka dan Allah zai wargaza mana shiri ne”

“Ai ba zan dauka ba”

Ya fada tana kallon wayar dake ta ringing har ta gaji ta tsinke, sai gashi ya sake kira sai dai wannan karon ta ji gabanta ya dan fadi.

“Kai wannan miji na ki da ci yake, gaskiya ki kashe wayarki kar ya zo yana damunki da kira ya lalata mana shiri”

“Wallahi kiran Fahat kawai nake jira, saboda yace zai kira ni anjima bana son na kashe wayar ya kira ya jita a kashe zai damu ne”

Ramlee ta mata wani kallo.

“Da alama dai shi ma dan hannu ne”

“Aa Wallahi shi ai son aure yake min da gaske, na nuna Masa ni Budurwa ce”

“Amman ke yar banza ce, ya zaki yi da Faruq?”

“Haba Ramlee kina min fatar zama da shi? Ai rabuwa zamu yi, kin ga idan ya sake ni ina zubar da cikin nan na cika idda zai na yi aurena”

“Kina ganin Faruq zai sake ki ne?”

“Dole na idan na bude masa shikashikan rashin mutunci ai dole ya sake ni”

“To dan fa ki yi yaya da shi? Ai kin san za a bincike ki musamman yayan manyan mutane basa aure zai sun zurfafa bincike”

“Ai idan na fita zan bar Sultan a gurin Faruq ne, ba da shi zan je ba, kuma shi Fahat din ai yace min a Lagos yake aiki, kin ga zamanmu a can zai kasance ba a nan ba, zan iya boye komai”

“Ki ce kema kin iya bala’i

Sai duk suka saka dariya, kiran Faruq ne ya sake shigowa wayar, wannan karon wani tsaki taja ta kashe wayar gaba daya.

TALBA POV.

Sai da yai sallah azahar sannan ya karaso gida, tun kamin yayi fakin idonsa suka sauka akan Leila dake zaune a daya daga cikin kujerun da suke balcony rike da wayarta sai cup din lemu a gaban kujerarta tana taunar cingan har wani kis kis take. Yayi kusan five minutes a motar sannan ya bude ya fito ya nufo inda take zaune ya zauna ba tare da yace da ita komai ba, hakan ya bata damar dauke kai daga gefen da yake ta maida wani gurin tana cigaba da taba wayarta.

“Can we talk?”

Ya fada ba tare da ya kalli inda take ba, sai ta juyo ta kalleshi.

“Ta fada maka ba ni ba ce ba kenan?”

Shi ma juyowa yai ya kalleta fuska ba yabo ba fallasa.

“Daddy ya damu dake ne i want us to talk”

“Da gaske?”

Sai ta mike tsaye ta dauki cup din lemun ta wuce ta bar masa gurin. Tana kokarin kai hannu ta danna door bell din kofar falon sai ga Kabir ya fito, ko kula shi bata yi ta shige, da kallo ya bita kamin ya juya ya kalli Talba dake kallon harabar gidan, har lokacin tunanin Aminatu yake. Karasa Kabir yai ya zauna a inda Leila ta tashi.

“Ya jikinta?”

“Da sauki…”

Talba ya amsa ba tare daya kalleshi ba.

“Ka yi magana da Leila ne?”

Ya girgiza masa kai.

“Wani lokacin baka sanin damuwar mutane idan baka kusantar su, you see yan gudun hijirar nan da kake gani a hanya wasu a fankon guri, suna da labaruka masu taba zuciya”

“Ita ma tana daya daga cikinsu ne?”

“Tana daya daga cikinsu ne?”

“Yeah they raped her, killed her Father, mother suka gona musu gida, suka kashe yayyunta and raped her mother in front of her, labarinta akwai tsoro da taba zuciya, yanzu haka she can’t walk saboda wahalar data sha gurin mutanen nan, and bata da kowa kuma tana bukatar kulawa sosai”

Talba ya fada cikin yanayin dake nuna zuciyarsa ta tabu sosai da labarin Aminatu.

“You know a lokacin da kake raina ni ni’imar da Allah yai maka, wasu da yawa suna can suna neman kadan, a yadda na fahimta now yanzu farinciki take bukata, saboda ya cire rai daga shi har tana neman kashe kanta, and Ali and wannan likitan sun fada min abun nan ya taba ta”

Kabir ma saurarensa yake cike da tausayin Aminatu duk da kasancewar ba taba ganinta ba, sai dai ya san waye Talba duk abun da zai saka shi a damuwa ko tunani ba abu ne kadan ba.

“Yanzu a wane matsaya take”

“Tana samun kula a asibitin, amman babu mai kwana a inda yake kuma kasan da ace tana uwa ko wata yar’uwa a raye zata fi samun kulawa, tana jin tsoro sosai har magana take idan tana bachi, and likitan ya fada mim idan tana yawan damuwa zuciyarta zata iya bugawa, yarinya ce karama kamar Amal, bata san inda zata je ba”

“Haka ne mutane suna cikin hali, sai dai idan baka shiga cikinsu baka sani”

Talba ya mike tsaye yana saka hannunsa aljihu. Ya nufi bangarensa, Kabir ya bishi da kallo yana murmushi.

LEILA POV.

Tana shiga dakin ta dauki wayarta ta kira Madina ta fada mata abun da ya faru, a ciki har da kudinta na son ta fadawa Daddy cewar ta fasa auren Talba.

“Anya idan kika yi haka baki yi kuskure ba? A Maimakon ki ta wannan haukan ba kara ki nuna masa kina son yarinyar ba ko da a munafunce ne”

“Lallai Madina baki gama sanina ba, ke a tunaninki zan iya share miji ko saurayi da wata? Har sai na nuna ina son ta bayan duk abun da yai min, ni fa na san ba sonta yake ba kawai yana amfani da ita ne ya cusa min bakinciki?”

“Idan har haka ne, ke me zai hana ki yi amfani da abokinsa ki rama abun da yai miki?”

“Waye kenan?”

“Ali mana, ta hanyarsa ma zaki iya tabbatarwa idan Talba yana sonki da gaske”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button