JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 52

Umma na shigowa dakin ta karaso kusa da gadon tana kallon Jiddah tace “Lafiya Jiddah?” Jiddah ta dago kanta da kyar hawaye na sauka idonta amma ta kasa cewa komai, Umma tace “Ciwon cikin ne?” Ta gyada mata kai kawai, Umma ta kalli agogo dake nuna karfe hudu saura, fita tayi daga dakin ta dau wayarta ta shiga kiran layin Ahmad, har ya katse ba a dauka ba, Umma ta tsaya tana ta tunanin yanda xata yi kuma, gashi ita bata driving da duhu, har ta fara tunanin kiran driver dinta sai ga Ahmad ya kira, dagawa tayi tace “Sorry i woke u up Ahmad, kana gari ne?” Ahmad yace “Aa ban shigo ba, me ya faru Umma?” Umma tace “Wllh ciwon cikin Jiddah ne ya tasar mata, ni kuma ba driving nake a duhu ba..

.” Yace “Subhanallah, bata taho da magungunanta bane?” Umma tace “Ka siya mata wasu maganin ne?” Yace “Ehh na siya mata a can gida, But Umma Captain na gari ai, ki kirasa sai ya taho ya kai ku asibitin” Umma ta sake kallon agogo, sai kuma tace “Toh shkkn” Daga haka ta katse wayar, Number Aliyu ta nemo a contact sannan tayi dialing number, Abuturrab na kwance ya samu bacci kenan kiran Umma ya shigo wayarsa, da yake baccin nasa bai wani nisa ba ya bude ido da kyar yana kallon wayar

tasa, mikewa xaune yyi ya jawo wayar da mamakin me kiransa at that time, number Umma ya gani a screen, ya daga ya kai kunne, Umma tace “Sorry na tashe ku Aliyu, idan ba damuwa ka taho gida yanxu xa ka kai mu asibiti…” Yace “Subhanallah.. waye ne ba lafiya?” Umma tace “Idan ka xo xaka gani” a hankali yace “Toh” daga haka ta katse wayarta, Mikewa Abuturrab yayi duk da idanuwansa da suka masa nauyi don throughout first hours of the night idonsa biyu ya kasa bacci, har sae kusan karfe uku da wani abu sannan ya samu sauki bacci ya daukesa, daukar wayarsa yayi ya fita daga dakin… Ya tafi

bangarensa ya bude kofar parlon a hankali sannan ya karasa bedroom dinsa nan ma he was so careful opening d door, Aneesah na kwance tayi dai dai saman gado tana baccinta, ya karasa gun kayansa ya dau kayan da xai dauka sannan ya nufi kofa xai fita kenan yaji cikin muryan bacci tace “Captain” Juyawa yayi ya kalleta, ta mike xaune tace “Ina xaka by this time, naga ka dau kaya?” Bai tanka ta ba ya fice daga dakin ta bi sa da kallo, ya koma dakin da yake yana cikin shiryawa ta shigo ta kulle kofar, bai ko kalleta ba ya ci gaba da buttoning din shirt dinsa, ta karaso kusa da shi, sai kuma ta durkushe kasa ta

[indeed-social-locker sm_list=’fb’ sm_template=’ism_template_9′ sm_list_align=’horizontal’ sm_display_counts=’true’ sm_display_full_name=’true’ unlock_type=2 locker_template=8 sm_d_text=’

This content is locked

Share This Page To Unlock The Content!

‘ enable_timeout_lk=1 sm_timeout_locker=1200 reset_locker=1 locker_reset_after=1 locker_reset_type=’days’ ism_overlock=’default’ ]

hade hannunta cikin rawan murya tace “Captain auren soyayya muka yi da kai fa ba auren kiyayya ba, wannan altitude din da ka tsiro yana sa min ciwon xuciya, don Allah idan wani laifi nayi maka kayi hakuri ka yafe min ba don halina ba” sai kuma ta fashe da kuka, ya girgixa kai yace “Ni nace kin min wani abu ne?” Cikin kuka tace “Gashi nan you are ignoring me and giving me altitude for the pass 8 days now, don Allah ba don ni ba kayi hakuri, albarkacin irin son da nake maka kayi hakuri” Shi dai bai ce mata komai ba, tana shessheka tace “Idan ma aikin gida ne da bana yi ai kaga yanxu dai na fara yi, har girki ina yi yanxu… in sha Allah kuma xan dore da haka, kawaye kuma na daina barin su xo min gida

daga yanxu, ni dai don Allah ka daina shareni haka ina shiga damuwa sosai Mijina” Ya dau makullin motarsa yace “Xan je Umma na kirana xan kai su asibiti” Tace “Subhanallah, waye babu lafiya?” Yace “I don’t know, sai naje” Tace “Toh don Allah in sa hijab mu tafi tare” Ya kalleta yace “No, it’s of no need” Ta marairaice tace “Me yasa kake yawan gwaleni a abubuwa da dama ne Captain, i just want to feel belong in ur family, har yanxu fa babu wani bond tsakanina da su, and it’s not suppose to be so, allow me to always mingle with them don Allah, kaga yanxu ai Umma xata ji dadi idan ta gan mu tare” yace

“Bayan wanda ku ke yi da Aunty? I mean the bond u are talking about” Tace “Ai Aunty daban Captain, har yanxu fa ko gidan Umman ma ban sani ba, don Allah kar kace min Aa captain, ka bari mu tafi tare, ni fa ba kowa gareni a garin nan ba sai kawaye kai ma ka sani” Bata jira cewarsa ba ta mike ta fita ta koma bangarensa ta dau hijab dinta har kasa ta saka kan doguwar rigan baccin jikinta, ta feshe duk jikinta da turare sannan ta fito, dai dai nan shi ma ya fito daga dakin da yake, ya fara sauka downstairs yana rike da makullin motarsa ta bi bayansa, Abuturrab bai ce mata komai ba ta bude daya side din

motar ta shiga, mai gadi da Abuturrab ya kwankwasa ma kofa ya fito da sauri ya bude masu gate, Mai gadin na tsaye gefe har Abuturrab ya fitar da motar sannan ya kulle gate din yana daga masa hannu, Abuturrab ya jira har masu gadin layin suka bude gate din layin sannan ya fita, yana isa layinsu Umma nan ma gate a kulle, hakan yasa ya dau wayarsa ya shiga kiran Umma, Umma na dagawa yace “Umma xa ku iya fito naga ba a bude gate na shigowa layin ba” Umma tace “Toh bari mu fito” daga haka ta katse wayar, Aneesah ta kallesa tace “Toh kayi horn mana kilan masu gadin xa su fito sae kayi masu bayani ko” Ya girgixa kai yace “No need” Idonsa na kan gate din gidansu Umma that’s not too far from

the gate leading to d street, bayan few minutes aka bude gate din gidan, Umma ce ta fara fitowa tana rike da hannun Jiddah Maimoon na biye da su, Ya dinga kallonsu kamar yanda Aneesah ke stressing idonta tana son ganin su waye suka fito, bude motar yayi ya sauka ya kulle sannan ya karasa ya shiga layin ta karamin gate din da ke a bude, Umma ta sake Jiddah da ta durkusa kusa da wani flowern wani gida xata yi amau, Ya isa har inda suke a tsaye yace “Me ya sameta Umma?” Umma dake kallon Jiddah

cike da tausayinta ta sauke ajiyar xuciya tace “Wai ciwon cikin dae…” Dukawa Abuturrab yyi yana kallonta shi ma, cikin low voice yace “Sorry…” Jiddah dai bata ce komai ba ta mike da kyar don ta kasa aman, Tun da Aneesah ta lura kamar Jiddah ce ba lafiya mood dinta ya canxa gaba daya, lkci daya ta fara da ta sanin fitowa da tayi ta biyosa… Ba don baxa ta samu abun hawa ba da kawai sauka xata yi ta

koma gida abunta, Maimoon ta daga Jiddah ganin bata yi aman ba suka ci gaba da tafiya, Abuturrab na kallon Umma yace “Tun yaushe take ciwon cikin?” Umma tace “Ban san sanda ya tasar mata ba, Maimoon ce ta shigo ta tasheni…” Abuturrab bai kuma cewa komai ba har suka isa gun motar yana kallon Jiddah, ya bude back seat Maimoon ta shiga ciki tare da Jiddah, Umma ma ta shiga bayan motar, ya xaga ya shiga driver seat, Aneesah tayi kasa da kai tace “Ya mai jikin Umma?” Umma tace “Alhmdlh,

mun taso ku ko” Tace “Aa babu komai Umma, Allah dai ya bata lafiya” Umma tace “Ameen” wani babban asibiti Abuturrab ya kai su, bayan su Umma sun sauka motar Aneesah ta kalli Abuturrab murya can kasa tace “Amma dai likita na attending masu xamu juya ko captain??” Ya kalleta yace “Amma tun farko sai da nace kar ki biyoni ko??” Ta hade rai tace “What did u mean? Asibitin xa mu xauna har a sallamesu kenan saboda Ramlah ce bata da lafiya ko Aisha?” Bai tanka ta ba ya bude motar ya sauka,

rai bace ita ma ta bude motar ta sauka tana masa wani irin kallo, kulle motarsa yayi ya bi bayansu Umma… Admitting din Jiddah aka yi a hospital din saboda karin ruwa da xa ayi mata, sosai take jin jiki wai duk a hakan ma tana da dauriya ba kadan ba, Umma na xaune bayan ta idar da sallan Asuba a ward din da aka kwantar da su wayarta ya fara ring, Maimoon ta mika mata wayar, Umma ta daga ganin Ahmad ne ke kiranta, bayan sun gaisa yace “Ya jikin nata Umma?” Umma tace “Ta samu bacci yanxu, an sa mata ruwa…” yace “Toh Allah ya sauwake, ya bata lafiya” Umma tace “Ameen” Ahmad yace “Captain ya tafi ne” Umma ta kalli Abuturrab dake xaune shima shigowarsa kenan daga masallaci tace

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button