TAYI MIN KANKANTA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAYI MIN KANKANTA 9

 ????????????????????????????????  *TAYI MIN ƘANƘANTA*

????????????????????????????????

*Zahra Surbajo*

*9*

A daren duk abinda ze mata yayi mata,iya azaba zahra tasha ta,duk wanda yaganta seya tausaya mata,haka ya gama komai,sannan ya barota kwance kamar matacciya.

Ɗakinshi ya wuce kai tsaye kan kujera ya faɗa yana maida numfashi,wayarshi tayi ƙara da sauri yakai idonsa gurin,Amininsa kuma babban likitan mata na asibitin Hammad Hospital,shi ke kiransa.

Ɗagawa yayi ya kara wayar a kunne yace “ya kake?”

Daga can ɓangaren ya amsa masa “kaganni wallahi se yanzu zan bar office,tun safe ina asibiti har na gaji,”

“munyi ɗaya kenan,nima yanzu fitowata daga wani aykin gaggawa kenan?”

“Wallahi da naso in shigo gidanku yau sabida gobe weekend,inaso in je falgore dubo ƴarfillon nan inga ko zaa dace,to se kuma ayki ya riƙeni,dama so nike in ce ko zaka rakani”

Murmushi muhammad yayi me sauti sannan yace”na gaida na ƴarfillo,Allah de ya yanke maka wannan wahalar,”

Dariya dukansu sukayi,sannan daga can ɓangaren yace “aboki bazaka gane bane,wallahi ina matuƙar tausayawa yarinyarne shiyasa”

“Na jima da fahimtar hakan,kaga in Allah yasa ka ganota kuma kaga tayi kalata kaga shikenan seka aura min ita,adena cemin gouro”muhammad yafaɗi yana dariya.Dan yasan ya tsokano abokin nasa,ilai kuwa bece komai ba ya kashe wayar.

Wata dariyar muhammad yayi sannan ya ajiye wayar ya miƙe ya shiga wanka dan jikinshi duk ciwo yake,danma mummynsa na gurin tana taimaka masa.

Tsawon watanni biyu zahra ta kwashe Muhammad ke kulawa da ita,zuwa yanzu ƙafa tasamu tana tafiya kaɗan kaɗan.

Sosai take samun kulawa agurin mummy,safe darana da yamma ita ke mata wanka,ga ruwan zafi datake yawan sata aciki ta zauna.

Zahra farinta yasoma dawowa ga wata ƙiba da tayi kamar ba mara lafiya ba,yanzu komai takeso tana samu,sede ba uhm ba uhm uhm ido kawai take binsu dashi ko wanne lokaci.

Yau zaune suke ita da hajiya a falo tana bata kankana tana sha,Muhammad ya shigo falon,bayan sun gaisa da hajiya ya dubi zahra sannan yace “hajiya jikin yarinyat nan da sauƙi,yakamata akaita asibitin mahaukata aduba lafiyar kwalwalwarta,shurun tayi yawa”

Kamar jira yana saukewa zahra cikin muryar marasa lafiya tace”lafiyata ƙalau ni ba nahaukaciya ba ce”

Ba muhammad da hajiya ba hatta daddy dake ƙoƙarin shigowa falon yayo mamakin maganarta.

Muje zuwa

Surbajo for life.

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button