Labaran Kannywood

Bincike: Mawaƙi a Kannywood ne ya ƙirƙiri labarin ƙaryar cewa Ummi Rahab ta ce ‘Ina da ciki’

WANI mawaƙi a Kannywood ne ya ƙirƙiri labarin nan da mujallar Fim ta buga a makon jiya mai taken: “Na Samu Ciki, Inji Tsohuwar Jaruma Ummi Rahab”

 

Binciken da mujallar Fim ta yi ne ya gano hakan.

 

A labarin, mun ruwaito cewa Rahama Saleh Ahmed (Ummi Rahab), wato matar mawaƙi, furodusa kuma jarumi Shu’aibu Ahmed Abbas (Lilin Baba), wadda kuma tsohuwar jarumar Kannywood ce, ta bayyana cewa ta samu ciki.

 

Mujallar Fim ta ɗauko labarin ne a ranar 9 ga Nuwamba, 2022 daga sanarwar da ta gani a wani shafin Instagram mai suna “matar_lilin_baba_official” a bisa tunanin shafin tsohuwar jarumar ne na gaske.

 

A shafin, an wallafa saƙo da Turanci da manyan baƙaƙe: “I’m pregnant”, wanda mujallar ta fassara da, “Na samu ciki”.

 

Ɗimbin masu bibiyar shafin a Instagram waɗanda ke tunanin Ummi Rahab ce sun tura saƙonnin taya ta murna tare da yi mata fatan alheri.

 

Sai dai kuma bayan mujallar Fim ta buga labarin sai wasu masu karatun ta su ka janyo hankalin mujallar da cewa shafin da aka ɗauko shi ba na Ummi ba ne, saboda haka ba gaskiya ba ne. Nan take mujallar ta tuntuɓi wani makusancin Lilin Baba a kan maganar, wanda ya ce shi ma ya ji mawaƙin na cewa ƙarya ne.

 

Don haka cikin ƙanƙanen lokaci, a safiyar Juma’a, 11 ga Nuwamba, mujallar ta goge labarin daga gidan yanar ta da dukkan shafukan ta na soshiyal midiya don kada ya ci gaba da yaɗuwa.

 

Bayan an sauke labarin daga yanar gizo, mujallar Fim ta samu labarin cewa Lilin Baba da matar sa sun nuna ba su ji daɗin buga labarin ba.

 

Wani bincike da mujallar ta yi a cikin ‘yan kwanakin nan ya gano cewa wani matashin mawaƙi mai neman suna shi ne ya ƙirƙiri shafin ƙaryar nan mai suna “matar_lilin_baba_official” inda ya ke kwafo hotuna da bidiyon Ummi Rahab ya na wallafawa a shafin da nufin cewa ita ce ke wallafa su.

 

Binciken ya nuna cewa mawaƙin ya na da kusanci da Ummi Rahab kafin ta yi aure, har ana zaton su na soyayya da juna.

.Bugu da ƙari, ya mallaki shafi a YouTube inda a can ma ya na wallafa abubuwa a kan Ummi Rahab da sauran ‘yan fim.

 

Har ma ya kan yi shigar burtu ya yi “like” na abin da ya wallafa ɗin.

 

Mujallar Fim za ta bayyana sunan mawaƙin da zarar ta kammala bincike a kan sa.

 

Yawancin jaruman Kannywood su na fama da irin wannan matsala ta yawan shafuka a soshiyal midiya, inda wasu ke buɗe shafukan ƙarya da sunan su.

 

Wasu su na yin haka ne domin su samu ɗimbin mabiya, ta yadda a gaba sai su sauya sunan shafin sannan su yi ƙoƙarin sayar da shi.

Idan a YouTube ne kuma sai su riƙa tura labaran gaskiya da na ƙanzon kurege kan ‘yan fim saboda su samu yawan mabiya don kamfanin YouTube ya riƙa biyan su kuɗin kamashon talla.

 

Wani kuma ya na buɗe shafi ne domin ƙauna kawai.

 

Da yawan jarumai su kan fito su ƙaryata shafin da ba nasu ba ne, musamman idan sun ga ya na shafa masu kashin kaji.

 

Ba halin mujallar Fim ba ne ta bayar da labarin bogi ko na cin zarafi. Ana gudanar da ita ne a bisa ƙa’idojin aikin jarida da aka yarda da su.

 

Hasali ma dai, tun da mujallar ta fara fitowa a cikin watan Maris na 1999 aka san ta da kare muradin Kannywood ba tare da tsoro ko nuna ɓangaranci ba.

 

Haka kuma ta kan karɓi gyara a duk lokacin da ta yi kuskure.

 

Don haka, hukumar gudanarwa ta mujallar Fim ta na ba Lilin Baba da matar sa Ummi haƙuri kan labarin da ta buga.

 

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button