Uncategorized

UBAYD MALEEK Page 61 to 70

Washe gari tunda safe Kamar kusan dai yanda ta Saba kitchen ta nufa aikin breakfast tayi su Fana da mum Sarah na tayata suka hada abincin safen saina maleek data hada Masa daban ta jera a tray sbd har lokacin Bai fara saukowa qasa cin abincin tareda ‘yayansa Kamar yanda ya Saba ba Ga afia har lokacin batasan yayi rashin lafiyaba ko da safen taje har sama ta gaidashi Amma bataga komaiba lafiya kalau ta gansa.

Tana gamawa tabarwa Fana aikin jera abincin a dining ita ta dauki nasa ta fito saidataga alamamun afia na daki kafin ta haye sama cikin sa’a kuwa baya palon saita ajiye ta juya ta fitowarta.

Tana saukowa dakin Farhat ta nufa Dan har lokacin bacci take itama kusan gidan yau kowa na gida tunda hutu suke.

Zaunarda farhat din tayi tana cewa”

Sweetie kitashi Haka fa ko kinmanta yau zamuje yawo.

Cikin bacci ta bude Yan idanuwanta tace”

Aunt ai ba yanzu zamuba Saida Rana kibari muyi bacci Mana.

Murmushi tayi kawai tareda kyaleta ta wuce toilet dinta anan tayi brush ta fito ta nufi dining Bata jira kowaba ta zauna taci ta koshi ta tashi ta nufi dakin padima dake zaune tana latsa wayarta ta dago suka kalli juna tasaki murmushi tace”

Ranki ya dade ta tashi kenan.

Batajin biyewa padiman Dan haka ta datse zancen da cewa”

Padima idan kinci abinci ki shirya anjima zamu fita ko.

Dan Dadi taji ta qaraso gurin NURUn tana cewa”

Inane zamuje?

Ko amsa Bata bataba ta juya ta fice tana cewa”

Ba takamaimai ko Ina aka samu zuwa za’ayi.

Qaramin tsoki padima taja tana dawowa ta zauna bakin gado tana cewa”

Duk zanyi lokacinkine daga baya indai fara Isa komai yashigo hannuna tukuna.

Dakinsu Takoma ta tararda afia zaune tana waya cikin damuwa take cewa”

Inshallah anjima zamuzo aunt Allah yabashi lafiya yasa kaffarane duk wannan.

Kashe wayar tayi tareda dagowa ta kalli NURU data tsaya tana kallonta cikin son Jin wayene baida lafiya taga duk afian tashiga damuwa.

Numfashi me zafi ta fitar kafin ta zauna bakin gado cikin sanyi tana cewa”

Jikin Imran ne yayi tsanani  tana cewa sai anyi Masa aiki,

NURU inaga duk wannan nice sanadi.

Kallonta NURU tayi jikinta amace sosai itama da tausayin Imran din sbd tabbas tasan Imran na Mata so me qarfi Amma ya suka iya Haka qaddara ta taho saidai hakuri.

Muryarta a Sanyaye tace”

Kidaina fadan haka wannan duk yin ubangiji ne haka ya tsaro dama 

Shima Inshallah zaiji sauki ahankali zai Saba ya rungumi kaddara da zaran yasamu wadda zata kula dashi.

Kallonta afia tayi da tunanin idan kulawa zatashi mantawa da komai ya dangana ya warke itace tafi kowa kamata tabashi sbd itace sanadin rabasu harya shiga wannan halin Dan haka Inshallah zatai iya kokarinta gurin sauke wannan alhakin dake kanta ko Dan haqqinsu ya sauka daga kanta.

Shiru sukayi dukkaninsu kowa da tunanin daya Dan fada musamman NURU datake ganin gwara Imran din yasan rashinta shine takamaimai matsalarsa idan yaso yaqar matsalar Yana tilastawa kansa mantawa da ita shikenan yayi maganin tasa matsalar

Amma ita haryanzu batasan matsayin kantabama bare tasan meye tata matsalar hartakai ga maganinta 

Ita kawai rayuwar take aduk yanda tazo Mata.

Qarfe biyu Sukayi wanka suka shirya

afia ta fita zuwa Taya farhat shiryawa tabar NURU na sauya wasu kayan sbd riga da wando tafara sakawa taga basuyiba ta sauya zuwa riga da skirt Suma taga basuyiba qarshe ta Sanya wasu maroon _Yves Saint Laurent_ riga da wandon Palazzo dasuka fiddo zallar yarintarta na matashiyar wayayyiya musamman kalar ta yiwa fatarta kyau ta Sanya wedges takalmin _CH/HC carolina Herrera_ black tazo gaban mirror zata fesa turarukansu dake jere saita fasa ta dauki _Lady l_ na _Acqua di parma_ ta fesa Wanda ya hadu da kamshin body mist dinta da spray na _ royalle Nina Ricci_ suna bada qamshinda sai ka kusantota sosai zakajishi

Tana daura scarf a kanta afia tashigo ta Isa gaban mirror tasake gyara fuskarta ta juyo tace”

Everyone is waiting for you fa kowa yafito.

Wayarta kawai ta dauka Banda handbag suka fito tareda afia din wadda itakuma heels ne takalmanta kusan Koda yaushe.

Suna fitowa Palo farhat tayi gurin NURU da duk ta cika musu ido musamman padima datake Mata kallon qyashi kafin ta dauke Kai tana sakin boyayyan tsokin da NURUn taji Amma ta qyale kaman bataji komaiba suka fito dukkaninsu afia ke driving sai ita NURUn a gaba sai padima da farhat sai jekadi a bayan.

Mr Omar yaso NURU tabi motar driver sbd ganin kaman sunyi yawa a motar Amma tace tafi buqatan cikinsu din suka fice Yana musu adawo lafiya.

Gurin wasan farhat suka fara zuwa sukayi kusan 2 hours agurin kafin suka fito suka tafi wani qaton mall

acan suka Bata lokaci sosai Dan sai yamma sbd irin kayan da padima tayita dauka Babu Wanda yace tabari

Dan kanta dataga kayan sunmata nauyi tabari suka fito aka aika duka siyayyan kayan dasukai direct zuwa gida da motar mall din.

Har zasu fito afia ta nufa bakery dinsu akai Mata packaging cupcakes guda shida masu icing na chocolate kadan ta biya ta karbo ta nufosu NURU ta kalleta tana cewa”

Mezakiyi da cupcakes?

Zamu biya dubiyan Imran a hospital so nayi tunanin abinda zamu Kai bansaniba kila wannan zaiyi.

Mum manta duka amma da a gida za’ayo Masa wannan din Amma ko hakan ma inaga yayi.

Mota suka shiga suka nufi hanyar asibitin farhat se murna takeyi zataga Uncle Imran sbd akwai shaquwa da sabo tsakaninta dashi Dan Kam acikin dangin mahaifiyarsu shikadai tasani duk da shima bawai tasan asalin asalin alaqarta dashiba kawai abinda tasani uncle Imran kaman family dinsu ne.

Suna Isa harabar asibitin sukai parking dukkaninsu suka fito NURU da afia ne agaba sauran na biye dasu NURU na riqeda hannun farhat wadda sai tsalle tsalle take tana cewa”

Aunt NURU mu bamu siyawa uncle imran komaiba kaman afia.

Murmushi tayi tana cewa”

Munkawo Masa addua ai muma.

Receptionist suka tambaya room number din Imran jalal tafada musu a third floor room 10.

Suna zuwa kuwa dakin na farko farko afia ce tafara knocking tareda bude kofar ta tura tashiga ahankali da sallama abakinta saidai ganin wadda ke dakinta yasa dukkanin bakinta qafewa saidai gudun wani tashe tashen bacin Rai da bazasu qari kowa da dadiba yasa ta danne ta qarasa shigowa dakin NURU da afia suka shigo hannun farhat har lokacin yana riqe acikin hannun NURU.

Kallo daya NURU tayiwa Matar dake zaune ta dauke wuta zuciyarta na harbawa da qarfi ta dauke Kai ahankali tana kallon afia da yanayinta ya sauya gabaki daya ta maida kallonta kan dad din Imran din dake tsaye da Alama fita zaiyi duk saitaji tana neman shiga wani mummunan hali ta samo nutsuwa daqyar cikin kannewa ta saki fuska ahankali tacewa dad din Imran din”

Ina wuni,ya me jikin?

Alhmdlh Mrs MALEEK 

Ya gida?ya maleek?and fmly?

Alhmdlh sir”tafada tana waiwayowa gefen LAILAH dake zaune dukkanin qamshinta na turaren _Calvin klein boss lady_ yacika dakin tana sanye cikin wasu set na byredo ash kala komai nata kana gani kasan manyan kudadene suka siyesa musamman makeup din dake fuskarta Wanda akoda yaushe LAILAH Bata rabuwa da ita.

Wani abune ya wucewa NURU da kayar tasamu numfashinta ya saki ta bude Baki daqyar tace”

Barka da yini miss.

Wani irin murmushin tausayinsu su duka yaran tasaki sbd sai yau Allah yayi zataga matarda maleek yake aure yanzu,

1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button