JIDDATUL KHAIR

JIDDATUL KHAIR 2

Ad

_____

Abuturrab ya xaro ido yana kallon ikon Allah, Hansai ta juya garesa da sauri tana dukawa tace “Don Allah kayi hakuri Alhaji, kayi hakuri Alhaji…. wllh akwai na nawa kake so?” Kasa ce mata komai yyi, ya kalli Jiddah da ta mike tsaye tana shessheka ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta, Yace “Toh har ya kai ki mareta haka??” Hansai ta kara hankade Jiddah da karfi tace “Toh idan ban mareta ba me xan mata, wannn da kake gani makira ce me mugun hali, kuma babu abinda na rageta da shi wllh tllh” cikin tsawa tace “Baxa ki bace min daga nan ba sai na watsa maki man kaskon nan a jiki gaba daya?” Matsawa tayi daga wajen tana kuka sosai, Hansai ta kara turata tace “Muguwa bar min awarata xan karasa suyan, ki je wannan tulin wankin na tsakar gida ban son in xo in ga ko hankici a kasa, duk in samesu kan igiya da lema” Tafiya kawai Jiddah take bata ce komai ba tana kuka, Abuturrab dai dauke kansa yyi, Hansai ta marairaice murya tace “Kayi hakuri Alhaji nasan ta 6ata maka rai sosai, na nawa kake son awaran?” Yace “Dubu daya” da sauri ta shiga saka masa har ta gama sannan ta mike ta kai masa ya bata kudin ta risina ta amsa tana murmushi hade da godiya, bai ko kalleta ba ya ja motarsa ya bar wajen. Washegari Saturday Abuturrab da yamma ya shirya ya fito daga dakinsa, Umminsa ce xaune parlor da Stepmum dinsa, duk ‘yan matan gidan sun tafi makaranta, Ummi ce ke magana Aunty na ta kallonta absentmindedly lkci lkci tana duba wayar hannunta, Ummi tace “Ai mu ma ba sonmu Allah ya fi yi a kansu ba, toh meye a ciki don ta shigo nan ta xauna?” Aunty tace “Haka dai kike ga babu komai a ciki, amma kina da labarin kudin cixo na makalewa jikin kaya kuwa?” Ummi tace “Gashi ai naji a bakin ki yau” Aunty na kallon Abuturrab tace “Kai ka ji fa Aliyu…. Musa me gyaran fulawa ne ya xo da matarsa da yara uku wai sun xo gaishemu daga kauye ina laifin parlan can na boys quarter da har sai sun xo nan don Allah, baka gansu ba wllh abun ba acewa komai, ni yanda kake da kyankyami ma nasan da kyar idan baka yi throw up ba, sai fa da nasa turaren wuta a parlorn ynxu….” Abuturrab ya d’an yi shiru, can kasan xuciyarsa yace for peace to reign…. Sai kuma ya dago kai a bayyana yace “To ai can din ya kamata suje dama ba nan ba Aunty” Wani kallo Ummi ta jefa masa, yayi murmushi yace “That’s the fact mum, ita Aunty tsoron bedbugs take….” Aunty tace “Toh ita cewa tayi wai ba a kyauta ba, haka kawai a bada mana kudin cixo a parlor a cuce mu?” Ummi tace “Toh Allah ya baku sa’a, idan walakanta d’an Adam abun yi ne, ku ci gaba” Abuturrab ya shafa kansa ya nufi kofa, Aunty tace “Ina xa ka Captain?” Yace “Xanje wajen wani abokina he just arrived from New york….” Har ya fita parlon Ummi bata ce masa komai ba, yyi murmushi bayan ya shiga motarsa, ko ina ruwansa da ‘yan kauye da suka xo da Aunty xata yi involving dinsa at d first place, girgixa kai yyi ya tada motar ya bar gidan, tafiyar kusan minti talatin yyi tunani iri iri na yawo a ransa, ba kasafai yake kwana da abu a ransa ba, infact it’s very rare hakan ya same sa, amma jiya ya kwana da yarinya me awara a ransa, dalili kuwa he lead to her been maltreated, she was slapped severally because of him, he felt guilty shi ne ma yasa ya kasa samun nutsuwa a ransa, yana isa dai dai gun da take awaran ya tarar bbu kowa, alamar ba ayi awaran yau ba, yyi ta bin dirty

unkept layin da kallo wanda ko mota ba lallai ya iya bi ba sbda gutters dake kwance ta ko ina, ji yyi kamar yyi amai, hankalinsa ya tashi sosai Bibalo ce ta xo wucewa fuskarta yau ma dai kamar warce tayi dambe da powder ga bakinta ya sha jan janbaki, lkci daya ya ganeta, ya sauka motarsa da sauri yana yamutse fuska yana kallonta yace “Yau babu abinda ku ke siyarwa ne?” Tayi fari da ido tana kallonsa tace “Ehh wllh, mijin kanwar babaarmu ne ya rasu yau da safe, tana can gidan mutuwar tace yau baxa ayi awaran ba” Yace “Ohk, ita warce take soyawan tana ina??” Ta wani yatsine fuska tace “Ohh wai Jiddah, tana can gida xata daura sanwan tuwon dawa, nima yanxu gidan mutuwar xa ni Baabarmu tace inje” yace “Ohkk, sai anjima” Tana murmushi tace “Toh sunana Bibalo kai fa?” Wayarsa ya ciro ya kara kunne snn ya koma cikin motarsa ya kulle, ta bi sa da ido sai bayan da yaga ta wuce snn ya bude motar ya tsirtar da yawu yana yamutsa fuska, ita kanta tsami take yi ga uwa uba warin gutter din anguwar, yaji gaba daya cikinsa ya fara hautsinewa, ya fi minti biyar xaune motar bayan ya cika Ac, har yaji ya dawo dai dai, wani yaro ya hango yana tafiya ya sauke glass ya kirasa, yaron ya xo, yana kallonsa yace “Wani gida ne ake awara a layin nan?” Yaron yace “Gidansu Bibalo ne” Ya sauko motar ya kulle sannan yace “Toh kai ni gidan” Nose mask ya sa a hanci bayan glass dake idonsa yana biye da yaron har suka isa kofar wani kuturun gida wanda shi dai ko dabbobi yake kiwo baxai sa su gidan nan ba don kilan Allah sai yayi ma dabbobin sakayya a kan ajiyesu da yyi a nan, gaba daya tsigar jikinsa tashi yake ga cikinsa da ya fara hautsinewa again, he have never been uncomfortable all his life kamar wannan moment din, yana kallon yaron da kyar yace “Shiga ka kira min me awaran” Ba musu yaron ya shiga, can sai gashi ya fito yace tana xuwa, ba a dau lkci ba sai gata ta fito, Hijab ne ta saka iya cinya sai xanin jikinta, gefen farin fuskarta duk bakin gawayi don wuta take rurawa, kallonsa kawai take alamar bata ganesa ba, ya sauke nose mask dinsa, ya cire glasses din idonsa, lkci daya gabanta ya fadi sosai bayan ta ganesa, hakan kuma bai hanata hade rai tana kallonsa ba duk da a tsorace take, shi ma dai cike da karfin hali yace “A xaton ki an mareki jiya sbda ni?” Kauda kai tayi, ya hade rai yace “Ki juyo ki kalleni ina maki magana” Ba tare da ta juyo ba tace “Ni dai ka rufa min asiri bance an mareni sbda kai ba, me ya sake kawo ka nan, in dai awara ne yau babu bamu yi ba” kallon yanda take maganan yake wanda komai ta fada sai dimples dinta ya lotsa, ta kallesa jin bai ce komai ba tace “Nace maka babu awara yau” Yace “Ohk dama sai kuna awara kenan kike wanka ki xauna bakin titi?” Ta wani xare ido tace “Ni nace maka banyi wanka ba??” Tana fadin haka ta kalli Hijab din jikinta wanda shima duk bakin gawayi ne hade da xaninta, slippers din kafarta ma duk ya tsufa, haka kawai ta ji kunya ya rufeta, ta 6ata rai tace “Ni sai kace nace ma banyi wanka ba, bayan girki nake yanxu” Bai tankata ba ya mayar da nose mask dinsa da glasses dinsa ya juya ya bar wajen ta bi sa da ido kamar me shirin kuka har ya kusa bakin titi snn ta juya a hankali ta koma cikin gidan nasu.

Ad

_____

Previous page 1 2 3Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button