JIDDATUL KHAIR

JIDDATUL KHAIR 2

2…..

KAbuturrab na kwance saman gadon dakinsa yana rike da wayarsa, kunnensa sakale da earpiece, video call yake da wani matashin da baxai wuce sa ba, matashin na xaune cikin wani ubansun parlor yana cin apple, Abuturrab ya girgixa kai yana kallonsa yace “Look… I don’t want to say anything about that…. idan Mummy na kusa ka bata mu gaisa” Matashin na taunar apple yace “It’s already late, tayi bacci…” Abuturrab yace “It’s late tunda baka son fita, so when are u coming to kd?” El-Basheer yace “Xa mu shigo kano tare da Mai martaba next week in sha Allah, probably ni xan karaso, amma sai kana nan” Abuturrab yace “In dai Friday ne ina nan in sha Allah” El-Basheer ya daga kafada yace “Ohk then” Abuturrab yace “Let me pick a call, sai da safe” El-Basheer ya gyara xamansa yana murmushi yace “The lady u don’t want to talk about?” Katse call din Abuturrab yyi ya dau daya wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne hade da cewa “How u babe?”
Abuturrab ne xaune parlonsa a gidansa dake Abuja shigowarsa gidan kenan ko awa daya bai yi ba, kasancewar weather babu kyau yasa suka yi landing flight da suka yi piloting daga Lagos a Abuja a maimakon kano…. Grapes ne gabansa yana ci a hankali yana kallon wani action movie da ake yi a tv, bude kofar parlon aka yi, lkci daya ya daga kai, he was expecting no one other than Ahmad da ya sanar ma yana Abuja… Tsayinta matsakaici ne…. ita ba siririya ba ita ba mai jiki ba, ta karasa shigowa parlon ta kulle kofan tana kallonsa ta cire Nikab din fuskarta, fara ce sosai, kallonta shi ma yake, she looks so orderly from head to toe, tuni kamshinta ya baxa parlon, shi dai kallonta kawai yake ta nufesa da damuwa ta xauna gefensa tace “Why ain’t you picking my call Captain?” Ya gyara xamansa yace “It wasn’t long da muka sauka ai, na sa wayar a caji a can daki, how are you doing?” A hankali tace “I’m fine, ya gajiya?” Yace “Alhmdllh, where are u coming from?” Ta buda manyan idanuwanta tace “Home… kace min xaka sauka Abuja shi sa na samu na fito” ya shafa beard dinsa yace “Ahmad na hanya, bana son ya xo ya sameki nan, u know how he thinks” Ta langwabar da kai tace “Ohk, amma nace maka ina son muyi magana, ina ta bin ka yau kusan sati biyu kenan sai kace min you will be piloting today, u will be piloting tomorrow….” Da damuwa ta kare maganar, Ya kalli agogo yace “To ina jin ki yanxu, I’m sorry i forgot about that” Shiru tayi, ya kafeta da idanuwansa, sai kuma yyi murmushi ya kamo hannunta yace “Ina jin ki Aneesah” Tayi kasa da murya tace “Aliyu a gidanmu an takurani in fito da miji, kwanaki kuma na gaya maka baka ce komai ba, idan har da gaske kake kana sona what is hindering you pls?” Ya dauke idonsa daga kallonta, bayan few seconds yace “To a jira ki gama karatun mana ko? Ina ce saura kadan” Ta girgixa kai tace “Aa last week Abbana ya kara min magana, and he is very serious about it this time, don’t u love me ne Aliyu?” Abuturrab ya xaro ido yace “Not at all Aneesah, kema kinsan ina sonki…. kar ki damu xa mu yi magana, yanxu ki tashi ki tafi kafin Ahmad ya xo…” Ta gyada masa kai sannan ta mike, mikewa yyi shi ma ya wuce daki ya dauko kudi ya mika mata kafin yace komai tace “Aa ni da motana na fito don’t worry” Bai ce komai ba ya rakata har balcony snn ya amshi jakarta ya sa mata kudin yace “I know da mota kika xo, Chocolate din da ban kai maki ba last week sai ki siya, ba kudi ne me wani yawa ba” Murmushinta me kyau tayi, tayi kasa da muryarta tace “Thank you my Captain” ya kashe mata ido yace “C’mon babe…. Nikab din kuma na meye yau kika sa?” Tace “I just felt like” ya daga kafada yace

[indeed-social-locker sm_list=’fb,tw,li’ sm_template=’ism_template_1′ sm_list_align=’horizontal’ sm_display_counts=’false’ sm_display_full_name=’true’ unlock_type=1 locker_template=2 sm_d_text=’

This content is locked

Share This Page To Unlock The Content!

‘ ism_overlock=’default’ ]

“Alright sai mun yi waya” ta gyada masa kai ta nufi gate ya juya ya koma parlor, her neatness melt his heart always nd make him fall for her deeply. Wata dattijuwa ce xaune dakinta tare da yan mata biyu, aka bude kofar dakin duk suka daga kai, Dattijuwar na murmushi tace “Aa Abuturrab sannu da xuwa” ya karasa ciki yana murmushi shi ma, ya xauna sannan ya gaisheta da ladabi, tace “Ka dawo weekend kenan” yace “Ehh daxu muka sauka, ya karfin jikin Umma?” Tace “Alhmdllh na ji sauki yanxu” yace “Allah ya kara lfya” tace “Ameen” ledan hannunsa ya ajiye yace “Ahmad yace in taho maki da wannan” Tace “Kun hadu a Abujan kenan” Yace “Ehh kwana na biyu a can, weather babu kyau sai yau na samu muka bar Abujan xuwa kano, daga kano na biyo private jet” Umma tace “Toh Allah ubangiji ya tsare mana ku dai, Allah ya rabaka da sharrin kayan bature, haka kai kuma Allah yayi hanyar cin abincin ka” Amira tayi ‘yar dariya tace “Kabu kabun jirgi Ya Abuturrab yake fa” Ta gefen ido ya kalleta bai ce komai ba, amma ya hade rai sosai, Umma tace “Ni dai Allah ya tsare min shi” a hankali yana kallon kanwar mahaifiyar tasa yace “Ameen Umma” Tace “Mun yi waya da Ahmad daxu nace masa wani awara da yake kawo min nake son ci wllh, gaba daya bani da appetite, yace kuma a hayi ake yi ko” Abuturrab ya d’an buda ido, sae kuma da sauri yace “Allah sarki, baxa a iya maki a gida ba Umma? Ae kamar yafi tsafta ayi a gida kawai” Tace “Aa da wahala, beside babu ma waken suyan a kasa, Hurairan da xata yi ma ta tafi garinsu daxu, kanninka kuma babu abinda suka iya gasu nan dai xaune, gwara kawai a siya a wajen ya fi, naga me kyau ne sosai ran da ya siyo ae” Abuturrab dai bai sake cewa komai ba, tace “Kuma yace ka san wajen, tare ma ku ke xuwa” Da sauri

Abuturrab ya xaro ido yana kallon ikon Allah, Hansai ta juya garesa da sauri tana dukawa tace “Don Allah kayi hakuri Alhaji, kayi hakuri Alhaji…. wllh akwai na nawa kake so?” Kasa ce mata komai yyi, ya kalli Jiddah da ta mike tsaye tana shessheka ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta, Yace “Toh har ya kai ki mareta haka??” Hansai ta kara hankade Jiddah da karfi tace “Toh idan ban mareta ba me xan mata, wannn da kake gani makira ce me mugun hali, kuma babu abinda na rageta da shi wllh tllh” cikin tsawa tace “Baxa ki bace min daga nan ba sai na watsa maki man kaskon nan a jiki gaba daya?” Matsawa tayi daga wajen tana kuka sosai, Hansai ta kara turata tace “Muguwa bar min awarata xan karasa suyan, ki je wannan tulin wankin na tsakar gida ban son in xo in ga ko hankici a kasa, duk in samesu kan igiya da lema” Tafiya kawai Jiddah take bata ce komai ba tana kuka, Abuturrab dai dauke kansa yyi, Hansai ta marairaice murya tace “Kayi hakuri Alhaji nasan ta 6ata maka rai sosai, na nawa kake son awaran?” Yace “Dubu daya” da sauri ta shiga saka masa har ta gama sannan ta mike ta kai masa ya bata kudin ta risina ta amsa tana murmushi hade da godiya, bai ko kalleta ba ya ja motarsa ya bar wajen. Washegari Saturday Abuturrab da yamma ya shirya ya fito daga dakinsa, Umminsa ce xaune parlor da Stepmum dinsa, duk ‘yan matan gidan sun tafi makaranta, Ummi ce ke magana Aunty na ta kallonta absentmindedly lkci lkci tana duba wayar hannunta, Ummi tace “Ai mu ma ba sonmu Allah ya fi yi a kansu ba, toh meye a ciki don ta shigo nan ta xauna?” Aunty tace “Haka dai kike ga babu komai a ciki, amma kina da labarin kudin cixo na makalewa jikin kaya kuwa?” Ummi tace “Gashi ai naji a bakin ki yau” Aunty na kallon Abuturrab tace “Kai ka ji fa Aliyu…. Musa me gyaran fulawa ne ya xo da matarsa da yara uku wai sun xo gaishemu daga kauye ina laifin parlan can na boys quarter da har sai sun xo nan don Allah, baka gansu ba wllh abun ba acewa komai, ni yanda kake da kyankyami ma nasan da kyar idan baka yi throw up ba, sai fa da nasa turaren wuta a parlorn ynxu….” Abuturrab ya d’an yi shiru, can kasan xuciyarsa yace for peace to reign…. Sai kuma ya dago kai a bayyana yace “To ai can din ya kamata suje dama ba nan ba Aunty” Wani kallo Ummi ta jefa masa, yayi murmushi yace “That’s the fact mum, ita Aunty tsoron bedbugs take….” Aunty tace “Toh ita cewa tayi wai ba a kyauta ba, haka kawai a bada mana kudin cixo a parlor a cuce mu?” Ummi tace “Toh Allah ya baku sa’a, idan walakanta d’an Adam abun yi ne, ku ci gaba” Abuturrab ya shafa kansa ya nufi kofa, Aunty tace “Ina xa ka Captain?” Yace “Xanje wajen wani abokina he just arrived from New york….” Har ya fita parlon Ummi bata ce masa komai ba, yyi murmushi bayan ya shiga motarsa, ko ina ruwansa da ‘yan kauye da suka xo da Aunty xata yi involving dinsa at d first place, girgixa kai yyi ya tada motar ya bar gidan, tafiyar kusan minti talatin yyi tunani iri iri na yawo a ransa, ba kasafai yake kwana da abu a ransa ba, infact it’s very rare hakan ya same sa, amma jiya ya kwana da yarinya me awara a ransa, dalili kuwa he lead to her been maltreated, she was slapped severally because of him, he felt guilty shi ne ma yasa ya kasa samun nutsuwa a ransa, yana isa dai dai gun da take awaran ya tarar bbu kowa, alamar ba ayi awaran yau ba, yyi ta bin dirty

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button