CIWON SO COMPLETE NOVEL

Lokaci yana tafiya kwanaki sunaja saffeya yau kingi 1 week sufara exam Abu yahadema safeeya biyu.
Kowa ya ga safeeya sai yatausayamata tarame sosai sai fari kawai,
Shima Dr Ahmed kowayaganshi baya tare da walwalla tare dashi Abinka dama da miskili sai yakara kurma karfi dayaji.
Komai yayi farko zaiyi karshe yauga su safeeya sungama Exam yau lafiya sunata pic din bakwana da yan makarantasu.
Domin wani saikadade bakaganshi ba wani ma har karshe rayuwa bazaka sake ganinshinba.
Amma kowa yaga safeeya bata cikin walwala Meenat ketajawo kota Saki jikinta Amma murmushin karfin hali kawai take,
Wayarta tayi Kara tana dubuwa taga Dr Ahmed kekiranta tafita Daga cikin hayaniya domin tadaga tace, hello, yace kisameni nan bayan wajen office din Dr mukhtar,
Tace OK, ganinan takatse wayan bata koma wajen su Meenat ba kawai inda yace tanufa, tanufi bayan tana zuwa
Ta iskeshi tsaye yaharde hannuwa.
31
Tanazuwa Dr Ahmed yabita da kallo itama kuramasa Kallo tayi,
Sunfi minti 15 suna kallon junansu babu kyaftwa,
Dr Ahmed ya kauda idonsa yaja Numfashi mai karfi yace safeeya yanzu rabamu zaayi ko ki Auri wani bani ba,
Safeeya Ina Kaunarki sondaban tava iyima watashiba, aryuwata,
Idan narasaki Bansan Halin dazan shigaba Aruyuwata,
Safeeya wallahi idan narasaki bazan taba aure Arayuwataba zanta rayuwata haka har lokacin mutuwa ta yayi.
Saiga Dr Ahmed yana hawaye Tofa ciwon so Maisaa kuka Dr Ahmed yamike.
Yace safeeya zantafi sai wata Rana, saffeya tamike tace sai wata Rana????
Yace Eh, sai wata Rana domin rabuwa dake yazama dole safeeya saboda maihaifinki, yazabamiki miji
Safeeya tazo gabansa ta tsaya kokasan zuciyata bakuwar zuciya ce dakai tasoma soyaya,
Yazakazoma jaririyar zuciya dabatu irin wannan,
KO kasan zuciyata kamar kwalba ne sonka Kamar ruwane dayasshiga ya daskare inda zaa cire saidai Afasa kwalbar,
Dr Ahmed yajuyo wajen safeeya ya muka iya
Safeeya muyi hakuri da juna,
Safeeya nabarki lafiya inayimiki fatan Alkairi
Yajuya yatafi saffeya tabi bayanshi tana kiranshi Amma inah bai juyowaba,
Domin hawaye ke tsiyaya yake safeeya tazauna kasa rarashe rashe tana rufzar kuka .
Allah sarki so
Allah karabamu da ciwon so.
Ina godiya masoyana
masu kirana DA masu iyiman text
nagode Allah bar kauna????????????
[1/24, 6:49 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): ????CIWON SO????
Na
Hafsat ( Hapsy baby)
32
Meenat ce keta joyo Joye inda zata ga hango saffeya Amma bata gantaba Meenat tace to inatashiga ne.
Nan tafito Daga cikin taron mutane tana dubuwa cantahango safeeya tana goge fuska da gyaletnta
Dasauri Meenat ta isa wajenta,
Safeeya tana hango Meenat ta isa wajenta dagudu tafada jikin sai wani sabon kuka yazomata,
Tace sister Dr Ahmed yabarni wayyo Allah na yanayiman fatan Alkairi,
Inayimasa magana betsaya saurerenaba,
Sister inason Dr Ahmed Abba zai hadani da yaya Haidar.
Banason yaya Haidar Meenat tace don Allah kiyi shiru sister kibarma Allah komai,
Shikeda iko Akan komai,
Nanta rarrrsheta tayi shiru suka dawo cikin mutane har akagama komai da komai. Kowa yawatse.
Shikam Dr Ahmed yana barin wajen safeeya mota kawai yaja yafita Daga school,
Allah kadai yakaishi gida domin Gudu kawai yake,
Yanazuwa kodaidata parking beyiba yafito dakinsa kawai fadawa yayi Bisa gado ko talkama be cireba,
Wasu hawaye masu zafi suka zubomasa yace narasa safeeya Arayuwata .
Basai lokacin daya dauka yana tunane tunane,
Wayarsa tayi Kara yanadubawa yaga my best Friend,
Yadauka yace Hafeez dagacan bangaren yace Abokina,
Yanaji muryarka wani kalah,
Dr Ahmed yace babu komai bacci ne nafara,
Hafeez yace dama zanfadamaka nanda 2weeks zanshigo katsina daddy zaifara ginin company. Nan sukayi magana ya datse wayar.
33
Safeeya ce kwance daki ta rame sosai saikace ba saffeyya kukan yau daban na gobe dabam
Batacin Abinchi tarame sai kuka hartakai data kuka zuci
Umma tunbata shiga Al’ amarinta hartakai data bata tausayi,
Tana rarrrshinta Abba yace komai zatayi baza fasa Aurenta da haidar ba.
Yanzuma kwance take tunanin wai yanxunan vazata Auri Dr Ahmed masoyintaba,
Meenat, ce tatoro kofar daki tashigo tazauna wajen da safeeya take tazauna,
Tace sister don Allah kirage damuwarnan,
Kibarma Allah, kamar ba musulmaba,
Kidauki kaddara, mai kyau, ko marar kyau,
Jiyadda kika koma kinrame yanzu tashi muje falo domin idan tafadamata Haidar ke kiranta bazata jeba,
Saffeya ta tashi suka nufi falo. Suna shiga kawai taga Haidar zaune falo kawai buge hannuta tayi Daga hannun Meenat ta buga tsoki tashige ciki,
Meenat tawaiwaya wajen Haidar, tace kayi hakuri yaya Haidar,
Yace babu komai Meenat kyaleta,
Dama nazo naji shirye shiryen Ku, Meenat tace insun shirya zasuyimasa magana,
Yace babu damuwa, yatashi yatafi,
Meenat tashiga cikin dakin cikin Fushi tace sister wai yakike haka ne don Allah meyasa bazaki hakura, da Dr Ahmed kisa yaya Haidar,
Saffeya tawurgo ma Meenat harara kinga malama ya isheki tsoki taja kawai tabar dakin ,
Tanufi waje tana try, din number Dr Ahmed domin tuneanar dasuka rabu school, haryanxu batasake samunshiba,
Harda hakan yakarasata damuwa,
Shikam Dr Ahmed yacire Sim din dasuke waya da saffeya kowa yaji saukin wani Abu, domin. Inyanajin muryarta zai shiga matsala, babba,
34
Lokaci yana tafiya kwanaki suna Kara yawa, yau bikin saffeya da Haidar kingi kwana goma, Amma babu ruwanta dawani hidima biki Meenat ce kadai keta hidima umma datayimata maganar bikin sai kuka.
Hajiya saudat ce zaune falo tana duba husnul Muslim,
Taji sallama tabada izinin shigowa saitaga Hafeez ne ahahaha, Hafeez kaine yace Eh,hajiya,
Yadurkusa yagaidata cikin ladabi suka gaisa
Tace shiga yana cikin daki kullum kwance, tindashi bedaukar kaddara mai kyau KO marar kyau intazo mishi,
Hafeez yatashi yashiga dakin yanashiga ya iske Dr Ahmed kwance daki duk ya yamutse,
Gashi Dr Ahmed duk yatara suma, ga kasumba tayimashi yawa, Haffez cikin mamaki yace Ahmed meke damunka,
Ka kuma haka kana kallan kanka Kuwa,
Dr Ahmed yatashi zaune cikin yanayi namar lafiya
Yace Hafeez yaushe kazo ne Hafeez yace bawaanan ta tambayeka ba meke damunka haka,
Dr Ahmed yace rashin saffeya, munrasa junanmu,
Hafeez yace. Mutuwa tayine,
Dr Ahmed yace A,a Abbanta zaimata Aure da dan kanenshi,
Nan yagayamashi komai yanagama gayamashi tari yasarkskeshi, Haffez cemasa yake sannu Amma tari yaki lafawa dasauri Haffez yanufi wajen firjin daki yadauko masa, ruwa Amma yanashan ruwa, suka dawo yana Kara wani kakin sai jini,
Hafeez ya firgita yace Ahmed!!! Jini kezuba
Amma Ina Dr Ahmed yasuma,
Haffez dagudu yafita. Yakira hajiya,
35
Hajiya tanashigowa taga halin da Ahmed yake ciki fashewa tayi da kuka tace Haffez dauko mota, mutafi Asibiti dasauri ya fiddo mota,
Ya ciccibi Ahmed hajiya tashiga suka nufi Asibiti,
Suna shiga Asibiti Aka turo keken marar lafiya Aka dauki Dr Ahmed Akashiga dashi
Hajiya da Hafeez sai zagaye suke hankalinsu tashe,
Kamar wajen minti 30
Doctor yafito Daga dakin daaksa Dr Ahmed yace su same shi office,
Bayan sun shiga sun zauna doctor yace ma hajiya Saudat kice mahaifiyar sa tace Eh,
Shikadai gareni doctor yakalli Hafeez, Kai kuma fa Hafeez yace Amininsa ne,
36
Doctor yaja Numfashi yace gaskiya yana cikin damuwa sosai daf take ta taba zuciyarsa Akwai. abinda yakeso, taredashi Asamomasa koma meye inbahakaba zai taba zuciyar sa Daganan kuma zuciyar na iya buguwa Ku rasashi,