CIWON SO COMPLETE NOVEL

Na
Hafsat ( Hafsy baby)
06
Wannan page din naki ne
Nana A Usman bisa kaunar book din nan dakike Allah yabar kauna.
Meenat taja wani numfashi tace kinaga hakan zai yiyu kuwa sister safeeya tace hakan shine mafita sister domin nagaji dahakan dayakeman kamar ni kadai A fadi school. Meenat ta mike tace ke bari naje dakin umma batasan nadawo ba domin nan kawai nayo domin hankalina yatashi wallahi. Daban ganki cikin school ba tana shirin fita sai ga umma tashigo tace Ahh,Ahh, yaushe kikadawo ne ke tace yanzu nashigo umma da Ina niyyar shiga dakin ki sai gaki kinshigo umma tace nashigo ne dama naduba jikin safeeya naga yajikin karfe Safeeya tace umma da sauki sosaima yanzu zantashi nayi sallah ne. Umma tace to kitashi kiyi ga dan gidanki can nayi miki dan’ wake kiyi sallah sai kici Nizan deka gidan Kawunku naji Alhaji nafadi dazu hajiya murja ta tazame da tayils ta goce da kafa Anjima kinkara jin sauki sai Ku leka kuganota. Safeeya tace sai kindawo umma. Umma tajuya tafita.
Bayan sallar Magariba safeeya da Meenat suka nufi gidan kawunsu domin ga gida ga gida suke suna shiga suka iske. Haidar zai fita( dan kawunsu ne) haidar yace yafara washe hakora kamar me tallar close up, safeeya takara daure fuska Meenat ce kawai tadan Saki fuska tace yaya haidar Ina yini yace bazan Amsa ba Ku baa ganinku sai da dalili ko yanzu ma don mamy tagoce dab aza gankuba ko Meenat tace wallahi karatu yadau zafi ne shi yasa . Haidr ya juya bangaren da safeeya take yace ke kurma ce dabazakiyi ma mutane magana ba safeeya inayini bata jira ya Amsa ba tashigewar wata ciki bata jira Meenat ba Haidar ya kada Kai domin CIWON SO Safeeya nadumshi tun lokacin da yafada Mata ta canza mishi. Bayan sun shiga ganin marar lafiya ne sun dan jima suka fito suka nufi gida bayan sallar Isha’ ne suna zaune A falo bayan sun gama cin Abinci dare kamar yadda suka saba wajen karfe 10: 00 pm kowa ya nufi makwancin sa. Amma safeeya babu Abinda take sai juye juye bisa gado domin wani fitanenen ciwon so Dr ke tasomata kuma koda zai kasheta bazata iyah tunkarsa tace tana sonsa. Kuma gobe tayi Alkawarin tunkaranshi taji meta iyimishi ya tsaneta haka. Nan tana juye juye har bacci yasadodo ya saceta.Asuba ta gari yan biyun umma.
[1/10, 12:14 AM] Hafsat ( Hafsy Baby): ????CIWON SO????
Na
Hafsat ( Hafsy baby)
Jiya wajen rubata number 5 narubata number 6 sorry????????????????????????
06
Washe. Gari kamar yadda suka saba tashi suka gama Abinda suke suka nufi school. Suna fitowa safeeya tace zataje gun Dr Ahmed. Meenat ta dakatar da itah tace tabari sufito daga lecture sai taje office dinshi . Meenat suna tafiya zuwa class take cewa nidama kin kyaleshi wallahi sister duka kingi one year mu ida school din fa, basai yakara ganniki ba sannan zai miki. Nan gaban safeeya yafadi ta tuna kingi shekara daya fa su ida school tadaina ganin muradin ranta(Allah sarki So duk irinda Abinda yakemata bata gani zuciyarta taki fushi dashi) Meenat tace sis yanaji kinyi shiru ne. Takakaro wani nurmushi tace Ahhh,, babu komai sis tunani nake wai kingi shekara daya mu ida school. Daganan firar su tazo karshe domin su iso class, Bayan sun fito daga lecture ne Meenat batasan zamewar safeeya tanufi office din Dr Ahmed. Tana isa ta iske yana kokarin rufe. Office din tayi sallama yajuyo yaga waye yanaga safeeya yace yakara daure fuska. Yacemata mekawoki wajena ba tunjiya mukayi magana dake ba nakuma baki Amsa. Ya bita ta gabanta zai wuce. Safeeya tayi saurin shan gabanshi. Tace sir bawannan yakawoni cikin fada take magana yayi mamakin haka daga bakin safeeya Amma benunamata ba yace mekawoki domin ina da Abinyi Ina sauri ne nabaki 5 minutes kifadi Abinda yakawoki. Tace bazan wuce hakan ba domin banga Abin tsayawa wajenka ( Karfin hali)
Sir naga duk cikin school babu wadda katsana kamanta. Mekake takama dashi, Kudi, mulki, kyau, komai daza kadinga wulakanta mutane yadda kakadama kasani babu Abinda yakai mutum daraja Amma Kaine Abin wulakacika, Kullum duk Abinda kake takama dashi fa Akwai wadda yafika. Ina sanar dakai kabi duniya A sannu ba matabbbata. Ba wurine dazamaba nar har Abadaba. Wulakanta mutane kuma kacigaba. Banyi maka wannan Maganar daka daina tsanata ba Ahhh, na tunatar dakaine. Nabarka lafiya. Safeeya tajuyo. Tatafi kawai tabar Dr Ahmed tsaye kamar butun butun butumi domin tunda tafara Maganar ya kuramata Ido nan yaji wani Abu yanayimasa yawo Akai ( tofa meye wannnan) A bangaren safeeya Kuma ba nufi wajen Meenat can baya takoma inda babu mutane tasha kukanta ta koshi har inda ta yacanza Allah sarki safeeya ciwon so Dr Ahmed na Amma tadaure tayimasa magana. Haka .
[1/10, 6:04 PM] Hafsat ( Hafsy Baby): ????CIWON SO????
Na
Hafsat ( Hafsy baby)
07
Safeeya nan wajen Tasha. Kuka tagaji taji kanta na ciwo. Tana niyyar mikewa taji wayanta na ringin taduba taga Meenat ce. Tace hello, Meenat cikin fada tace Ina kika shigane Ina nemakin tundazu tace sorry sis ganinan zuwa. Bayan sun idar da lecture din suka nufi gida. Kamar yadda bayan sun idar da Abinda suke sukayi ma iyayensu bakwana kowa yanufi makwancinsa safeeya tafara tunanin datasaba kullum dare. Takasa bacci ma baki daya tatashi tayo Alwalla tayi sallah ra’ ka biyu. Ta roki Allah yayemata son Dr Ahmed inba Alkairi bane. Tare da itah. Bayan tagama tatashi tahau gado ta kwanta can sama sama bacci yafara daukar ta taji wani zafi A kirjinta tun tana daurewa har takai datafara numfashi sama sama. Can. Meenat taji kamar A mafarki taji numfashi firgice tatashi ta kunna lantarki taga safeeya ce cikin wannan halin A firgice tace sister! Sister!!! Amma taga numfashinta sama sama kawai yake A firgice ta Doro. Daga bisa Gado ta nufi Hanyar waje domin kiran Umma da Abba tazuwa tashiga knocking din kyauren Daki Abba. Da karfi A firgice umma da Abba suka farka sukaji buga kyaure ba kaukautawa Abba yazo ya bude kyauren yaga Meenat yace meyafaru Amina( domin haka yake kiranta) cikin kuka tafara magana Abba.. Safeeya bata lafiya gayanacan numfashi ta ….bebari ta ida yanufi dakinsu da sauri saidai umma tabi bayansa itada Meenat suna shiga suka iske safeeya tana ta numfashi sama- sama da sauri Abba yace mikar da ita kafinan na fiddo mota cikin sauri Abba yafito don fiddo mota domin tafita Asibiti yana fiddota su umma suka fiddo da safeeya tallabe baya Meenat suka shiga Alheri clinic suka nufa domin can suke da file suna isa suka fiddo da safeyya wadda takejin su sama sama. Suna shiga Akabata gado. Sunyi sa’ a kuwa sun iske doctor dinsu wadda kedubasu. Nan danan yashiga duba Safeeya yaga Abinda kedamunta yayi mamakin dayaga ciwon zuciya kedamunta har yana nema yimata illah. Cikin zuciyarta. Yasan dai ba su rasa ci ba balle kayan sawa tomeke damunta ne nan yafito yacemusu suje gida sai dasafe sudawo domin yanzu zasu ajeta dakin Hutu bata bukatar hayaniya Abba yace doctor bazan barta ko yar uwata bace yace karku damu Alhaji daki dazamu ajeta bata bukatar kowa. Abba yace doctor jikin dai sauki yace da sauki mumata wasu Allurai yanzu. Tana bacci zuwa gobe insha Allah zata warware Abba yace toh Allah yasan haka. Doctor yace Ameen.
Abangaren Dr Ahmed kuwa tunda Safeeya tama gayamasa magana tajuya tatafi yakusan Minute 10 goma tsaye yana tunanin sannan yatuuka motar yabar makarantar babu inda ya nufa sai gida yanashiga ya iske mahaifiyarshi A falo tana kallo yayi sallama yace Hajiya tace naa’ m Babana meyafaru naga yanayinka ya canza ne. Yace babu komai tace Anya babana babu komai inbaka fadaman waza kafadamawa ne yayi murmushi babu komai hajiya. Yatashi zai shiga ciki tacemasa Ga Abincika can kitchen naajemaka fa. Yace yanzu dai bari nashiga ciki nayi wanka. Nadan kwanta Ina fitowa zuwa Anjima naci hajiya taceshikenan sai kafito yajuya ya shiga ciki hajiya tabisa da ido har yashige ciki tace nasan Akwai Abinda kedamun yaron zurfin cikinsa da miskilanci bazai Bari yafadaman ba tagirgiza Allah sawakka karya jama kansa wani ciwo Dr Ahmed nashiga babu inda yazarce sai dakin sa yashiga toilet yawtsa ruwa yana fitowa jallabiya kawai ya zura yahau gado domin yasamu bacci Amma inah babu bacci magaganun Safeeya kemasa yawo. Nan yafara tunanin komai yacazama masa tsanar kowace mace cikin Ranshi