TAKUN SAAKA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAKUN SAAKA 5

 

*_Typing????_*            *_????TAKUN SAAƘA!!????_*

                *_Bilyn Abdull ce????????_*

_ZAFAFA BIYAR 2K22_

????????????????????

*_LAST BONANZA_*

*KARO NA QARSHE!*

*_farincinku shine namu,ZAFAFAN DAI,sun sake amsa kokenku,sun sake rage muku kaso 20 cikin 100_*

*_Daga yau 29 ga wata,har zuwa 31 ga watan nan,xaku iya biyan 800 a amadadin 1000 na kudin litattafai biyar_*

*_za’a fara posting in sha Allah 3st January da yardar Allah_*

*HANZARTA KI BIYA NAKI KAFIN RANAKUN SU QARE*

*XAKI BIYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

SAIKU TURA SHAIDAR BIYA

08184017082

GA MASU TURA KATIN WAYA KO KUMA VTU,SAIKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYANKU

09134848107

_________________________

*_Chapter Five_*

…………Wani irin rawa jikin Ummi ya fara saboda azaba. Ya ƙyalƙyale da dariya yana wani fici-fici da ƙananun idanunsa jajaye. “Asiya idan kin manta bara na tuna miki. Daga ke har ƴaƴanki da kikeji girmansu ya kai yanzu a tafin hannuna kuke wlhy. Zan kuma iya binku ɗaya bayan ɗaya na salwantar da rayuwarku batare da wani mahaluki ya iya gane hakan ba ko zargina. Kamar yanda na gagareki a baya da kikeji da ƙuruciya a yanzunma hakan take. Dan haka ki cigaba da buɗemin ido da tsagerancin nan naki kiga idan ban kai rayukanku ƙasa ba cikin ƙanƙanin lokaci”.

    Ya ƙare mganar da hankaɗa kanta ta bigi fuskar gadon. Wata siririyar ƙara ta saki ta zaba. Cike da juriyar zaluncin data saba sha daga garesa ta dubesa da idanunta da suka kaɗa zuwa ja tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallar dake taruwa a cikinsu. “Insha ALLAHU Haƙilu bazaka taɓa cin nasara akan zuri’ata ba bayan nasarar aure na da kayi a baya, bazan gaji da faɗa makaba ko yanzu kana samun nasarane a kaina saboda wasu dalilai na lizzamin zaren ƙaddara, amma ka jira lokaci, dan kaɗan ya rage azo dai-dai wajen da zakasha mamaki…….”

     Sake buga kanta yay a fusace kafin takai ƙarshen zancenta saboda sukar zuciyarsa da kalamanta sukeyi a duk sanda ta maimaita masa su, ya saka hannunsa ya danne mata baki yana ƙyalƙyalewa da dariya. “Iyakarki kauɗin banza da cika baki Asiya, amma ki sani ni Haƙilu nafi ƙarfinki, dan baki da maraba da wulaƙantacciyar dabba a gareni, amfaninki a wajena kawai samun abinda nai kwaɗayi a gareki tun farko kika hanani, yanda kika wulaƙantani a kansa a baya haka zan cigaba da samunsa a gareki cikin wulaƙantarwa da ƙasƙantar dake a ƙasan takalmana.”

     Da iya ƙarfinta tai yunƙurin turesa amma ta gaza hakan, sai ma ƙara jigata da wahaluwa da takeyi a hannunsa. Yayinda shikuma yake ƙyalƙyala dariyar shaƙiyanci a gareta da izgili, cikin tsantsar zalunci da wulaƙantarwa ya shiga ƙoƙarin yin tarayya da ita kamar wanda ke tare da ƙasƙantacciyar karuwarsa. Yanayi yana kai mata mari saboda ƙoƙarin ƙwatar kanta da takeyi a garesa.

         Kamar kullum sai da ya galabaitar da Ummi son ransa sannan ya barta yana faman tuntsurar dariyar rashin imani. Yaja kayansa ya saka bayan ya goge ƙazantar jikinsa da gashin kanta tare da tofa mata yawu ya fice yana cigaba da ƙyalƙyala dariyar.

         Wani irin siririn kuka Ummi ta saki mai cin rai a wajen. Takai kusan awa ɗaya tanayinsa kafin ta miƙe zuwa toilet da ƙyar saboda azaba. Dukkan dabarun data sabayi domin gyara jikinta a duk lokacin da hakan ta faru tsakaninsu su ta gudanar, koda ta fito doguwar riga ta saka tahau saman abin salla ta fara gayama ALLAH kukanta akan zaluncin Alhaji Haƙilu ƙanin mijinta ada, sannan kuma mijinta a yanzu. 

         Bayan tayi nafilfilinta tai zaman karatun AL-QUR’ANI. Sai da taji zuciyarta tayi mata sanyi, nutsuwarta ta dawo jikinta sannan tai addu’a ta ɗan kwanta, cikin lokaci ƙanƙani barci mai daɗi yay gaba da ita tamkar bata da wata damuwa.

        Kamar yanda ta horar da yaranta tun suna ƙanana yau ma tun kiran sallar farko na asuba suka tashi. Sai da duk sukai alwala sanann suka firfito daga ɗakunansu su biyar abin sha’awa, dan a daren duk suka dawo ba kamar yanda ta tsammaci zasu kwana a wajen ba, a tunaninsu tayi barci ita da auta shiyyasa basu shigo ba. Ammar ne ya nufi ƙofar ɗakin Hibbah ya shiga mata knocking da kiran sunanta har sai da yaji ta amsa. “Tashi kiyi salla, saura kuma idan kin idar ki sake kwanciya tunda kinsan dai yau kinada text ɗin safe”.

          Bai jira amsartaba yabar wajen dan yayunsa na jiransa. Basu damu da tada Ummi ba, dan sunsan ita bata makara saboda mace ce mai tsantseni da yawan kula da ibada, bata da wasa sam akan bautar ALLAH. Hakama koda suka fito daga sashen nasu basuyi gigin tada sauran jama’ar gidan ba suka fice abinsu zuwa massallacin anguwar.

        Daƙyar Hibbah ta tashi zuwa toilet saboda barcin dake cikin idonta. Cikin layi da rangaji irin na wadda ta tashi a barci ta shige bayin. Kusan mintuna ashirin sai gata ta fito ɗaure da towel tana tsane gashinta da wani alamun ta samu tsarki. Zani ta ɗaura ta saka hijjab har ƙasa ta tada salla.

*_7:34am_*

           A gurguje take shiri tana yawan kallon agogon ɗakin nata saboda kiran da Ummi keta faman ƙwalamata daga falo.

       Cikin kumbura fuska da ƙunƙuni take faɗin, ‘Kai Ummi wannan kira kamar makauniya, ai ba kowa ne ya jamin wannan makararba sai Yah Ammar, duk da yasan zanje makaranta harda min gargaɗin karna koma barci sai gashi bayan dawowarsu massallaci ya tsareni sai na haɗa masa indomie wai nafi kowa iya dafawa……..’

      “Tanee! Tanee!!”. 

     Ummi ta sake ƙwalama Hibbah kira again. Ƙoƙari amsawa take cikin zazzaƙar muryata tana tattare tarkacen abinda zata buƙata a cikin bag ɗinta mai zubin school bag. Daga can ta sake faɗin, “Auta kina kallon agogo kuwa?!”.

        Saurin ɗaukar bag ɗin tayi da gyalenta tayo waje da hanzari. Tun kafin ta ƙaraso tsakkiyar falon Yah Umar ya wullomata harara cikin faɗa. “Wai ke kullum sai kin makara kin makarar da mutane hankalinki ke kwanciya a gidan nan ko? Tun kina zuwa secondary halinki kenan, yanzu kin fara jami’ar ma baki canjaba”.

       Fuska ta kumbura tana tura baki, ta ajiye bag ɗinta da gyalen a saman kujera tana ƙarasawa dining ɗin inda duk suke zaune har Ummi, dan haka suke cin abinci a tare duk safiya da dare. Cikin shagwaɓar data saba da tsiwar da bata barin bakinta tace, “Kai Yaya Umar naga dai Yah Ammar ne ya sakani makara, sakanifa yayi na dafa masa noodles”.

        Yah Ammar dake kujerar gefenta yana ƙoƙarin fara cin indomie ɗin data dafa masan ya zubomata uwar harara shima yana faɗin, “Dama can kin saba makararki yarinya zaki wani jingina dani”.

       Baki ta sake buɗewa zatayi magana Yah Usman dake duba wasu takardu dake gabansa a dining ɗin shima ya watso musu harara ita da Ammar ɗin, “Dalla malamai karku cika mana kunne kuma ko”.

     Ummi dake turama Hibbah kofin kunu data zuba mata tace, “Ai inda sabo sun saba, Ammar da Tanee basa taɓa zama waje guda basu isheka ba, sai kace suna ganin hanjin junansu. Nikam babu mai barina da ciwon kai kowa yayi ya gama ya kama gabansa”.

       Baki Hibbah ta kuma cikawa da iska tana duban Yah Muhammad da Yah Abubakar masu kareta. Yaya Abubakar dake hidimar haɗama kansa shayi yayi murmushi, “Auta yada kallona kuma? Nimafa yau gashi kina neman makarar dani bayan nace da wuri zan fita”.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button