NOVELSUncategorized

DIYAM 20

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Twenty: The Two Corpses

Tunda muka koma school nake lissafin kwanaki ina jiran zuwan Sadauki dan nasan wata daya yake yi yazo ya ganni, kuma nasan bashi da karya alkawari sam. Lissafi na yana cika
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); kuwa na fara saka ran ganinsa. Ina zaune kuwa a class sai ga baba mai kiran alkhairi yazo kirana. Na tashi na bishi da sauri jidda tana tsokana ta dan tasan lissafin zuwan wanda nakeyi. Muna fita daga class din na tsaya na kara gyara fuskata ta glass din window, ina lura da yadda sabon kitson da na saka akayi min jiya ya kara fitowa wa da kyawun fuskata. A gefen staffroom na hango shi a kasan bishiyoyi kamar kullum in yazo. Sai dai amma dama matsa kusa sai naga kamar ba shiba, kamar Sadauki na baikai wannan girma da iya daukar wanka ba. Sai na tsaya daga dan nesa nayi sallama. Ya juyo kyakykyawar fuskarsa dauke da murmushinsa mai kyau, na rufe baki ina dariyar murnar ganinsa nace “ashe da gaske kaine, sai naga kamar ba kai ba” ya harde hannayensa a kirjinsa yana kallona yace “lallai Diyam girma yazo, yau ke ce da yi min sallama bayan da tahowa kike da gudu ki wuce kirjina?” Na dan jawo hijab dina na rufe fuskata ina jin kunyarsa, ya saka hannu ya bude fuskar yace “yanzu in taho gari ya gari dan inga fuskarki kuma sai kiyi min rowarta ki rufe? Kinyi min adalci kenan?” Na danyi murmushin jin kunya sannan na kalle shi daga sama zuwa kasa. Ya zama cikakken saurayi sosai, hatta sajen sa ma ya zama complete kuma yayi masa kyau sosai. Gani nake duk samarin duniya babu wanda ya kaishi kyau a lokacin. 

Sai kuma na rike baki nace “wai!! Sadauki ina zaka kai girma ne? Sai wani jin karfi kake kamar zaka dauki duniya” yace “ya kika ji sunan? Aliyu fa aka ce miki. Kin manta shi asalin mai sunan duniya kaf ta shaida karfinsa da jarumtakarsa? Sannan kuma akayi min lakani da Sadauki, kin san kuwa ko a cikin mayaka to duk wanda aka kira da Sadauki ina nufin jarumi ne shi a cikin jarumai. Ingarman namiji kenan” nayi dariya ina rufe baki, yace “what’s funny?” Nace “wai ingarma, sai kace wani doki” shima sai ya tayani dariyar.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Na sunkuyar da idanuna ina wasa da fingers dina, mukayi shiru na wani lokaci sannan na dago kai na muka hada ido, na turo baki na buga kafa a kasa nace “ni ka daina kallona haka” yace “fada min menene shirrin, sai wani kara kyau kike yi kullum” na bata rai nace “bayan bana girma. Kuma wallahi ina cin abinci sosai” yayi dariya yace “girman zaizo ne Diyam. You won’t know sanda zaki girma kawai sai dai ki ganki kin zama katuwa” nace “ni tsoro nake ji?” Ya bata rai yace “tsoron me? Nace “kai gashi nan ka zama kato, gashi kuma zaka tafi jami’a, kar kaje kaga manyan yammata kace ka fasa dani” ya jingina da jikin bishiya yana kallona, yace “Diyam” na dago muka ido yace “you have no idea how much I love you, do you? Ke din fa zuciyata ce, sonki kuma jinin da zuciyata take bugawa ne yana zagaye ilahirin jikina. Ta yaya mutum zai iya rayuwa babu zuciyarsa. Idan kinga Sadauki ya daina sonki to numfashin sa ne ya bar jikinsa. Idan kinga na rabu dake Diyam to kirjina aka tsaga aka cire zuciyata daga ciki. Nine ya kamata in kasance cikin tsoron watarana zaki rabu dani, ina tsoron idan innarki ta ki amincewa dani Baffa zai hanani aurenki, ina tsoron in kin girma zaki samu wani wanda ya fini kudi wanda ya fini asali kice kin fasa dani” na girgiza kai na nace “never, ba dai Diyam ba, Diyam ai kai take so tun kafin ta san menene so, da kai ta saba da kai kuma za tayi rayuwa insha Allah. Rayuwa babu kai will not be only unbearable but also unimaginable. I can’t imagine Diyam without Sadauki” sai ido na ya kawo kwalla, yace “zaki fara kukan ko? I am here and I am going no where”

Muka zauna akan bench ya fara bani labarin gida, ana yake gaya min Baffa ya siya masa fili, yace “filin fa babba ne sosai, wai ashe for years yana tara min kudin aikin da nakeyi masa a garage shine yakara akai yasiya min. Yace duk sanda natashi yi mana ginin gidan mu sai inyi akai. Sannan kuma ya fara bani salary a garage kamar sauran ma’aikata” nayi murmushi nace “inye, kaga masu albashi” ya daga gira yace “ya kika gani?” Nace “Baffa ya kyauta. Allah ya saka mishi” yace “ameen. Problem din da nake fuskanta daga Ummah ne, tun ba yau ba kinsan nake fama da ita akan ta kaini dangin babana taki, ni kuma yanzu ina ganin kamar har da rashin su a tare dani ne yake kara kiyayyata a zuciyar Inna, ina so su shiga rayuwata Inna ta gansu tun yanzu amma kullum Ummah tana ce min wai ba yanzu ba, wai lokaci bai yi ba. I just hope ba zai zama too late ba” nace “it won’t be, ni nasan Ummah kuma na tabbatar tana da dalilinta”.

Ya sunkuyar da kai yana kallon kafarsa fuskarsa da alamun damuwa, naji nima zuciyata babu dadi sai nayi niyyar saka shi dariya nace “Sadauki kaga wani kwaro zai shigar maka ido rufe idonka inga ni” sai kuwa ya biye min ya rufe idonsa, sai kuma na shagalta da kallon fuskartasa. Fuskarsa bata cika tsaho ba kuma ba za’a kirata da zagayayyiya ba. Gashin girarsa mai cika ne da laushi kamar yadda gashin kansa yake, dogon hancinsa da kofofin suke budewa da sauri da sauri a yanzu alamun bugun zuciyarsa ya karu, madaidaicin bakinsa mai dauke da lips a slightly lighter than his dark skin color kuma suke zagaye da kyakykyawan sajensa mai laushi da kyalli, abinda yafi ɗaukan hankalina a fuskarsa sune zarazaran gashin idonsa da suka yi kama da irin wanda yammata suke sakawa a gidan kwalliya. 

Sai kuma nayi dariya, ya bude idonsa yana kallona yace “what? Ya fita?” Nace “wallahi gashin idonka irin na yammata ne” ya bata rai yace “Diyam kin raina ni Wallahi, dan kinga gurin kwana na ko?” 

Sanda aka zo min general visiting sai naga anxo har da Ummah wannan karon, abinda ba’a taba yi ba. Naji dadi sosai muka zauna mukayi ta hira, muka ci abinci har da Baffa. Da zasu tafi kawai sai na fara kuka, abinda na dade banyi ba. Baffa yace min “ki zama yarinyar kirki Diyam, ki rike addinin ki kuma ki dage da addu’a akan komai ya same ki. Allah yayi miki albarka” sai na rungume shi ina kuka, yana dariya yace “yau kuma shagwabar kaina tazo?” Ya cire hannu na daga jikinsa, Ummah tace “zo ni ki rungume ni tunda shi baya so” na sake shi kuwa na tafi na rungume ta, sannan na juya na rungume inna itama. Ina kallo suka shiga mota suka tafi, sai naki kamar wani part nawa ya tafi tare dasu.

Kafin muyi hutu Sadauki ya sake dawowa. Wannan karon shida wani abokinsa suka zo kuma shine karo na farko da Sadauki ya fara introducing dina a gurin abokinsa, Ahmad Muhammad, na rike sunan ne saboda a ranar mun jima muna musu akan Ahmad da Muhammad duk suna daya ne. Sai kuma mukayi hirar carrier, shi Ahmad yace babu abinda yake so ya zama inya girma irin dan sanda, yace “duk ranar da na zama commissioner of police duk wadannan yan iskan da suke yawo a gari sai na rufe su” Sadauki kuma yace “ni kam whatever zan zama nan gaba a rayuwa will have to do with cars. Ni ina da wani passion sosai akan motoci” sai suka tambayeni ni kuma fa? Na girgiza kai na nace “I don’t know gaskiya” Ahmad yace “with time zaki yi finding your place in the society kema”.

Tunda hutu ya kusa nake jin babu dadi kamar wadda zanyi rashin lafiya amma kuma ciwon yaki zuwa, haka nayi exams din duk babu dadi. Ko kitson hutu banyi ba. Ranar hutun kuwa sai jidda ce ta hada mana kayan mu ta kai mana bakin gate. Har ta dawo ina kwance akan gado kawai naki hawaye yana bin fuskata, tazo ta tsaya tana kallona tace “kuka kuma Halima? Wani abun ne yake miki ciwo?” Nace “zuciya ta ce babu dadi jidda, ji nake kamar bani da lafiya amma kuma lafiya ta kalau, gaba na sai faduwa yake yi jidda” tazo ta rike ni tace “to ai addu’a zaki ke yi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun , ba wai kuka ba” na fara yi kuwa sai naji naji dadi. Muka fito tare akayi assembly aka sallame mu kowa yana murna bandani. 

A ka’ida duk ranar hutu kafin a bude gate su Baffa suke zuwa, amma yau sai naga an bude ana ta daukan sauran dalibai bandani. Na samu kofar wani class na zauna idona akan gate din makarantar amma ko motar da tayi kama da tamu ban gani ba. Har aka zo daukan jidda tazo tayi min sallama ta tafi. Har akayi sallar azahar shiru. A lokacin I was beyond crying kawai dai a zaune nake kamar mutum mutumi. Can sai ga wani malamin mu yazo inda nake yace “Halima? Ki zo anzo daukanki” na mike jiki ba kwari na bishi ina ta baza idon ganin Baffana ko Sadauki. Muna shiga staffroom sai naga Abba, baban su Rumaisa. Na tsaya kawai ina kallonsa yace “Diyam babu gaisuwa?” Sai na durkusa na gaishe shi malaman gurin suna ta kallona. Ya tashi da kansa ya zuba min kayana a motarsa sannan yace min inzo mu tafi, sai da muka shiga mota sannan nace “Abba ina Baffa yake?” Ya dauke kansa yace “sun taho motar su ta samu matsala, shine yayi min waya ni kuma na taho daga gumel yace dan Allah in biyo in taho dake” na gyada kaina kawai ina forcing zuciyata ta yarda da maganar sa.

Har muka shiga Kano bamu kara magana ba, na kwantar da kaina na rufe ido na kamar bacci nake yi amma ido na biyu. Na bude ido na kallon inda muke naga ba hanyar gida bane ba nace “Abba ba gida zamu tafi ba?” Yace “zan karbi wani sakona ne anan akth” na koma na kwanta. Ina ji muka shiga asibitin har mukayi packing, na daga kaina kadan ina kallon inda muka tsaya “Accidents and Emergencies” sai kuma ido na ya hango min wata kamar Aunty Fatima a tsaye a kofar gurin, sai na bude kofa na fita idanuna suna kara tabbatar min ita din ce amma zuciyata ta kasa yarda. Ina zuwa kusa da ita na lura kuka take yi, na bude baki zanyi mata magana sai na hango Inna a cikin hall din, Mama ta rike ta tana ta rusa kuka kamar ranta zai fita. Kamar mutum mutumi haka nake tafiya har nazo kusa dasu, sai naji muryar Ummah daga gefena tace “Diyam!!” Na juyo na zube idanuna a kanta, she looked old, ban taba ganinta a irin wannan yanayin ba amma kuma babu hawaye ko digo a idonta, “Diyam” ta sake fada sanda ta karaso kusa dani ta miko hannu da niyyar rungume ni amma sai ta sulale ta fadi kasa ta suma akan kafafuwana. 
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Tsayawa nayi kawai ina kallonta yayinda jama’a da ma’aikatan asibitin sukayi kanta. “Addah” naji muryar Asma’u a bayana, na juyo lokacin data karaso da gudu ta rungume ni 

“addah mun shiga uku, Baffa da Sadauki sunyi accident kuma duk sun mutu”

Na cire hannunta daga jikina na dan tura ta kadan ina kallon fuskartada take cike da hawaye, sai kuma naji wani abu yana fusgata zuwa wani daki da naga wani doctor ya fito daga ciki yanzu. Na tura kofar dakin ina kallon gadaje guda biyu da suke a cikin dakin, sannan na kalli wadanda suke kan gadajen. Gadon farko wanda yake kai an lullube shi har fuskarsa. Gado na biyu kuma an rufe shi zuwa kirjinsa. Sadauki. Daga inda nake ina iya hango jinin daya jika sumar kansa ya bata katifar da yake kai.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button