NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 13

      *_Bilyn Abdull ce_*????????

*_NO. 13_*

……….Gidane da komai za’ace Alhmdllh, dan saika rantse da mace aciki, komai tsaf kuma ƙal, ga ƙamshi mai daɗi yana tashi.

        Zama Ummukulsoom da Dad sukayi, yayinda Amaan yanufi wata ƙofa Attahir na binsa abaya.
     Mintuna kaɗan suka fito suma suka zauna suna sake gaida Dad cikin girmamawa.
   Shima cike da kulawa yake amsa musu da tambayar aikinsu.
     Bayan kammala gaishe-gaishe Amaan ya sake miƙewa yana faɗin “Dad bara na saka maka ruwan wanka kai salla, kafin Su Abbas sukawo abinci”.
     “A dai akai ɗiyata ɗakinta tasami nutsuwa, ni ba baƙo baneba, Attahir ma ya rakani”.
       Ɗan yatsa yasa ya ɗan shafi girarsa kawai, bai iya sake cewa komaiba har Dad da Attahir suka nufi wata ƙofa dakecan gefen falon.
     Ummu dai na zaune duk tana saurarensu kanta a ƙasa, ya ɗan kalleta yay gaba batareda yace mata komaiba, itako dukda tana kallonsa ta ƙasan ido ƙin motsawa tayi, yayi wajen taku biyar ya tsaya cak jin bata biyoshiba, ya kasa ɗaga baki yace mata ta taso, yakuma ƙi juyowa ya kalleta.
      Karo na farko da abinsa yabama Ummu haushi, ta miƙe tana kumbura fuska batare da itama ta tanka masa balle ya samu amsa.
    Gaba yay tabisa a baya saikace wata munafuka, yanzu kam ta fara fahimtar dolene su Aneesa sukejin tsoronsa, mutum babu fara’a babu walwala, magana ma wahala take masa, ita kam dai takula yamafi Dad tsauri da tsare gida.
       Ɗakine Babba, wanda da alama ma sabbin kayan gado aka saka masa, dan sai ƙamshin sabon fenti ke tashi, gadonma babu zanen gado, sai katifar da ko leda ba’a cirewa ba, hakama bedsheets ɗin yana cikin ledarsa ba’a fiddashiba.
       Da ƙyar ya iya buɗe baki yace, “Nan ne ɗakinki”.
   Kai kawai ta ɗaga masa, amma bata amsa da bakiba.
   Hakan sai ya sakashi waigowa ya kalleta, dai dai ta ɗago ido zata saci kallonsa. Karaf idonsu suka shige cikin na juna, da hanzari ta janye tai ƙasa da kai.
    Idanu ya ɗan lumshe ya buɗe yana taɓe baki, kafin ya raɓa ta gefenta yafice abinsa.
     Cikin dabara tabi bayansa da kallo harya fice, ta sauke ajiyar zuciya tana taɓe baki itama da bin ko ina na ɗakin da kallo.
   Komai Ash color ne a ɗakin, idonta ya sauka akan akwatuna pink dake gefe guda shida sabbi fil, mamaki ya ɗan kamata, ta taka zuwa gabansu jikinta har rawa yake ta ajiye handbag ɗin hannunta a gefen gadon tabuɗe ɗan ƙaramin saman akwatunan. Littatafaine na addini, sai Qur’an da abin sallah mai ƙyau.
    Jikinta a sanyaye ta maida ta rufe tana mamakin akwatunan minene kuma?…..
    Batada mai bata wannan amsar, dan haka tanufi ƙofar data gani a ɗakin wadda take kƴautata zaton toilet ne.   
         Sosai Toilet ɗin yamata ƙyau shima, sai dai ba a ajiye komai ba na amfani a ciki, alwala kawai tayi ta fito tai sallar Isha’i.
       Idar da sallarta babu daɗewa saiga matar Attahir, itama bawata babba baceba, dan yaronsu ɗaya Ahmad, Ummu ta tarbeta da fara’a tana karɓar tiren hannunta data haɗoma Ummun abinci.
      Hafsat wayayyar macece mai yawan fara’a, gata ƙyakykyawa masha ALLAH, tun Ummu na sissine kai harta fara sakin jikinta da Hafsat saboda janta da hira da take tayi, cikin mintuna ƙalilan sabo yashiga tsakaninta da Ummu.
      Ahmad kam ai yana jikin Ummu. Hafsa itace tabuɗe bedsheets ɗin ta shimfiɗa a gadon, tareda buɗe akwatunan ta fiddo mata duk abinda zata buƙata kamar su sabulan wanka mai turare da kayan barci dadai sauransu.
    Ta ɗaga wata rigar barci mai azabar ƙyau pink tana kallon Ummu da murmushi, “Amaryarmu gaskiya wannan ya kamata yau asama angonmu, dan dakansa yaɗau rigar barcinnan dukda dai bai buɗe ya ganiba lokacin”.
     Ummukulsoom tai ƙasa da kai tana murmushi da mamakin maganar Hafsat na cewa da kansa ya ɗauki rigar barcin, dan ƴar ɗigilace, gata shara-shara.
    Fahimtar hakan da Hafsat taine yasata dariya, “Karkiji wasa wlhy, dashi mukaje muka haɗo lefennan, duk abinda ya tare masa gaba ya ringa kwasowa, ni dariya ma ya bani, sai da naima Abban Ahmad magana sannan ya dakatar dashi nafara nuna abinda za’a ɗauka. Ai wannan miji naki kam saikin dage kin maido manashi mai fara’a amarya, dan ALLAH ya kukeyi idan yaje wajanki hira? Dan ni tunda mukai aure da Abban Ahmad kusan shekara biyu kenan zan iya rantse miki ban taɓa ganin haƙoransa da sunan dariya ba”.
     Rasa abinda Ummu zatace tayi, dan ta fahimci itama maman Ahmad ɗin batasan auren ɗori ɗafini akai mata da shiba, sai kawai tai murmushi tanama Ahmad wasa”.
      “Nifa kibarjin kunyata, danni ƙawarkice ehe”. ‘Cewar maman Ahmad tana rufe akwatunan da miƙewa’.
     Toilet tashiga ta aje mata komai na amfani inda ya dace, tasake dawowa bedroom ta shirya kayan kwalliyar da turarirrika akan mirror.
    Ummukulsoom dai nata wasa da Ahmad abinta tanacin abincin da maman Ahmad ta kawo.
      Bayan Maman Ahmad ta kammala itama ta dawo ta zauna kusada Ummukulsoom suna ɗan hirarsu a nutse. Bata sake jin ɗuriyar su Amaan ba sai kusan sha ɗaya na dare, lokacin hadari yafara tasowa gadan-gadan.
     Amaan yay sallama a ƙofar ɗakin batareda ya shigoba, amsawa sukai yaɗan leƙi kansa yana faɗin, “Maman Ahmad Attahir na jiranki”.
     Baima jira ta amsa ba yabar wajen.
      Ummukulsoom ta ɗakko mata Ahmad dayay barci ta rakota, sun iske har harsun fice dan haka suma sai suka fito inda Amaan da Attahir ke tsaye iskar hadari na kaɗasu.
     “A’a amarya dakanki kika fito cikin wannan iskar? Kamata yay ai kar’a sake ganin idonki a waje sai nan da wata biyu haka”.
     Murmushi Ummukulsoom tayi tana miƙama Maman Ahmad dake bama Attahir amsa Ahmad ɗin, shi dai Amaan uffan bai ceba, dukda kuwa yana tsaye a wajen yana jinsu dama kallonsu, dan ƙasa-ƙasa yaketa bin duk wani motsin Ummukulsoom da ido, so yake yaga mi Dad yagani a tattare da yarinyar da har yaga dacewarsu takai suzama miji da mata……
    Yayyafi aka fara, dan haka su Attahir sukai musu sallama suka nufi gidansu dake gabansu Ummu kaɗan, dan gida baifi goma bane a tsakaninsu.
        Daga shi har ita babu wanda ya motsa a wajen bayan wucewar su Attahir, ƙarfi ruwan ya farayi yana jiƙasu, ganin bashida niyyar motsawa sai Ummu tawuce sim-sim ta barshi a wajen tsaye.
      Da kallo ya bita harta shige, kafin ya lumshe idonsa ya buɗe yana shafar girarsa da ɗanyatsa.
      Koda Ummukulsoom ta shiga saita laɓe a jikin Window tana kallon ikon ALLAH, zai taho kokuwa sai ruwan yagama sauka a kansa?. A mamakinta sai taga ya cigaba da tsaiwa a wajen ruwa na jiƙashi, tsawon mintuna kusan goma ruwan yayi ƙarfi sosai yay masa jalaf, dan farar rigar jikinsa dukta manne masa, ganin yanufo hanyar shigowa yasa Ummu kwasa da gudu tanufi ɗakinta, sai da ta zauna sai gudun nata yasata yima kanta dariya ita kaɗai.
      Tundaga nan bata sakejin motsin kowa ba, ga ruwa ana shekawa sosai, ALLAH ɗaya gari banban kenan, a gida arewa dai sanyi ake zubawa, sai gashi yau tazo lagos kuma ana ruwa, lallai baka sanin mi duniya take ciki saika baro yankinka, tunani taitayi kala-kala, harta kwanta, can ƙasan zuciyarta kuma cike da kewar babanta da ahalinta na ɗilau tareda Baseer daya faɗo mata a rai. Daga ƙarshe dai saida tai kuka zuciyarta ta rage nauyi kafin barci ɓarawo yasamu damar saceta.

  ⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

        Kwanan su Suhailat goma cif a dubai suka dawo Nigeria da kaya niƙi-niƙi, dan tunkan su taho da kwana huɗu suka turo kayansu.
      A washe garin dawowarsune ta kira Baseer dake ɗilau a waya tana sanar masa sun dawo, sakin jikinsa yay sukasha hira, da mata alƙawarin gobe zaizo kaduna wajenta.
    Murna tayi sosai tareda masa addu’ar zuwa lafiya.
   
      Duk wayar da yake da Suhailat agaban inna dake bakacen geron fura data surfa yakeyi, amma tai biris dashi tamkar batajiba, saida ya aje wayarne daga inda yake a kishingiɗe a tabarma yace, “Inna kinji Suhailat sun dawo jiya”.
      A lalace Inna tace, “ALLAH sarki, to sannunta da zuwa”. Daga haka taja bakinta ta tsuƙe taci gaba da bakacenta. Shima bai sake magana ba yakoma chart dasu Abdull. Kamar an tsikareshi ya ɗago ido ya sake kallon Inna,
    “Inna wai miyasa naga an dawo da waɗancan akwatinan?”.
       Kamar bazata tanka masaba sai kuma tai murmushin takaici tana miƙewa da harhaɗe kwanukan datai aikin, “Tunda kace bazaka auri ƴarsuba mizasu yi da kayanmu, sun kuma aurar da ita gamai bukatarta, idan sun ajiye kayan wazai saka?”.
     Mamaki shinfiɗe a fuskarsa yace, “Wai Inna kina nufin Ummukulsoom tayi aure?”.
     Cikin gatse Inna tace, “A’a sun ajeta sai bayan kayi naka tukunna”.
       “ALLAH yabaki haƙuri  inna ba baƙar magana na nemaba, amm to yaushe ma akai hakan ban saniba? Ko wani ƙaton ƙauyen suka samu?”.
       “Kaje ka bincika mana”.
    Shiru yay bai sake maganaba, saima baki daya taɓe alamar su suka sani yacigaba da chart ɗinsa.

*_Washe gari_*

      Da hantsi ya shirinsa tsaf ya nufi kaduna wajen Suhailat. Tarba yasamu mai ƙyau agareta, yini guda suna a tare, ta kwaso masa akwatuna yagani, sai santi yake da yaba ƙyansu. Suhailat na fita kawo masa abinci yay sauri ya ɗauki hotunan komai tare da kansa cikin style kala-kala, atake ya turama Su Abdull cewa gafa kayan lefe Mom nashi ta haɗo a dubai, jiya ta dawo.
     Rikicewa sukai sunata santi, Areef yace, “Bas gaskiya wannan karon kazo ka kaimu mu gaida Mom, bai dace ace muna tare kusan 3years ba amma kaƙi kaimu gidanku, bayan kuma mu duk kasan namu gidajen”.
      Tashi yay zaune da sauri saboda ganin maganar Areef ɗin, jikinsa har rawa yake ya rubuta musu, “Karku damu guys zakuje gidanmu, kunsan dai anan wajen ƙanwar Mom ɗina nake, gashi masifaffene mijinta da ita kanta, amma zakuje Abuja tushena insha ALLAH”.
     Nan take suka shiga maida masa reply ɗin “ALLAH ya kaimu lokacin”.
    Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya rufe data ɗin, kansa ya dafe da takaicin Areef, duk cikin abokansa shine ya cika nacin akan saiya kaisu gidasu, shikuma ya zula musu ƙarya cewa a abuja iyayensa suke, anan zariya gidan ƙanwar Mom nashi yake, sun taɓa zuwa gidan Innarsa anan zaria, dayake gidansu mai ɗan ƙyaune dan mijinta nada hali dai-dai gwargwado sai bai damuba, amma saida ya zinliƙa musu karyar wai Dad nashine ya sayama su Innar tashi gidan ma. Suko duk sun yarda dashi saboda ƙyawunsa da tinkaho kesakasu ɗaukarsa ɗan manya, kuma sun haɗu da shine a time ɗin yana tare da Suhailat tafara sakar masa ƴaƴan banki.
      Suhailat bata san miya faruba tadawo suka cigaba da hirarsu hankali kwance.

★★★★★★

        Tun daga ranar shirye-shiryen biki suka cigaba da gudana, sai dai a gidan su Suhailat kawai hakan ke faruwa, dan a ɗilau hankalin Baba da Inna kwance yake, sun dai san ɗansu zai aure, amma tunda ba’a buƙatar komansu an raina miye nasu kuma, sai su zuba ido suga yaya wasan zai ƙare.
       Tun bikin na sauran sati ɗaya Baseer ya tattara kayansa ya koma Kaduna ya tare a hotel da  Suhailat ta kama masa ɗaki da kanta, dan haka suma su Najeeb sai suka dawo nan suka tare kawai.
    Hidimar biki aka shiga sosai, sai dai kuma babu ahalin Baseer na gaskiya a ciki, dan yanajin kunyar nunasu saboda ƴan ƙauyene. Amma gudun kar suji kunya suka samo wata hajiya Hamida ghana amatsayin sojan haya mai amsa sunan mom ɗin Baseer, itace ta samo musu dangin da zasu dinga wakiltar kowane taro matsayin dangin Baseer kuma.
   Hakan kuwace ta faru, tun aranar kamu dasu hajiyar Dubai akayi amatsayin dangin Baseer, ko lefe ma ana saura kwana hudu biki su aka kaimawa suka kuma kawowa gidansu Suhailat amatsayin lefe harda key ɗin mota.
      An cigaba da biki har ranar da aka ɗaura auren Suhailat da angonta Baseer, wanda yay shar cikin shadda fara tas. Ɗaurin aure dai su Baba sunzo hardama baban Ummu ma ya halarci ɗaurin auren, sai daifa su ƴan kallo suka zama, dan wani Daddyn Suhailat yasa a matsayin wakilin Baseer, dan haka ƴan ɗaurin aurema suka ɗauka shine mahaifin Baseer ɗin.
     Abin yay matuƙar ƙona ran baba, amma saiya danne bai nunaba, sai idon mutane ya faka ya share hawayensa da babbar riga, ƴaƴa biyu kawai suka mallaka a duniya, daga Talatu sai Basiru, sun saka basiru yay makaranta bisa shawarar mijin innarsa ta zaria, sai kuma danya zama mai taimakon kansa da ƙauyensu, amma sai abin yazama ba hakaba, dama wannan shine dalilin da su mutanen ƙauye ke gudu wajen barin ƴaƴansu suyi zurfi akaratu, kowa na tsoron ɗansa ya aro baƙon halayya da sukan kira na yahudu da nasara. Da wannan takaicin baba yakoma dilau, ko inna baiba labarin yanda akaiba ya bar abinsa a zuciya. 

Ango da amarya ansha kyau an gaji, musamman a wajen dina, ƙawayen Suhailat duk sun rikice da ganin handsome ɗin data samu na kerewa tsara da zagayen ƙasashen duniya, ga nera kamar yanda ta sanar musu, ansha shagali kam yanda ya kamata, dan nera ta koka iya kokawa, daga karshe aka miƙa amarya Suhailat ɗakinta dake a ƙaton gidan da mahaifinta ya bama Baseer. Wanda shikuma baseer ya mannama abokansa ƙaryar Dad ɗinsane ya saya masa anan kd saboda yanason zama anan fiye da Abuja.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
      
           Barcin da Ummukulsoom bata samu bane yasata makara, sai wajen 7 ta tashi, salla tayi cikin taraddadin yinta a makare, bayan ta kammala ta gyara ɗakin dukda babu wani dattima, wanka tayi ta shafa mai, sai dai kuma babu kayan sakawa, tsaye tayi cikin jimamin yanda zata samu kaya, dan ta lura su isa basukai ga isowaba ƙila, dabarar buɗe akwatunan lefen nata da maman Ahmad tace tayi, cikin amincin ALLAH saita samu dogayen riguna a ciki, wata jaa ta ɗauka ta saka, rigar tamata ƙyau sosai, gashi tai mata ɗas tamkar an gwadata, dan Ummu ba siririya baceba, hargitsin bikinnan ma ne dai yaɗan sakata ramewa, motsin dataji ya yawaita a falone da maganganu yasata leƙowa.
      Mamakine ya kamata ganin Dad dasu isa direban dayayo gaba da kayanta, sai kuma wadda aka haɗosu tare da zata ringa taya Ummu ƴan ayyuka kamar yanda Dad yace.
       Fitowa ta idayi, tazo gaban Dad ta durƙusa ta gaidashi. 
     Da kulawa ya amsa mata dukda dai fuskar babu walwala, tariga ta saba zuwa yanzu da wannan yanayin nasa. Gaidata su Isa ma daketa shigo da kayan sukayi, ta amsa tana musu sannu da zuwa da tambayar hanya.
       “Hanya Alhmdllh auntynmu, ai tunma jiya muka iso, sai dai lokacin ruwa ya sakko dole muka nemi mafaka”.
    Ummu tace, “ALLAH sarki, sannunku da zuwa”.
        
         Dad ya kalli agogon dake falo sannan ya kalli Ummukulsoom, “Ɗiyata tadomin mijinki, danni nagama shirina jirgin ƙarfe goma zanbi”.
       Gaban Ummu ne ya faɗi, tuni damuwa ta mamaye fuskarta, sai dai kuma ta kasa cewa komai ta miƙe zuciyarta na ɗar-ɗar ɗin tsoro, itafa koma ɗakin nashi bata saniba.
    Corridor ɗin dataga yashiga jiya shida Attahir ta nufa zuciyarta nata bugawa da sauri-sauri. Ƙofar ɗaya ta iske cikin Corridor ɗin, tai tsaye takasa koda ƙwanƙwasawa,  taja kusan seconds 10 kafin ta fara ƙwanƙwasawar a hankali, saida tai haka har sau uku amma ko motsi batajiba, ɗora hannunta tai a handle ɗin ƙofar tana rimtse ido, tamkar wadda tazo sata haka ta leƙa kanta bayan ta tura ƙofar, ALLAH ma yasota bata da ƙara.
     Kwance ta hangosa saman ƙaton gadonsa ruwan hanta a rigin gine ya rungume filo dogo, gadonma farin bedsheets ne a shinfiɗe, yana sanye da wandone 3queater fari tas shima a jikinsa da best itama fara, fuskarnan fayau da annurin da ko idonsa biyu bazaka sameta a sake hakaba. Rasama abinda ya kamata tayi tai, sai kawai ta zaɓi juyawa ta sanarma Dad bai tashiba….
      “Mikike buƙata?”.
Muryarsa ta daki kunnenta babu zato. A matukar firgice ta juyo ta kalli gadon, a mamakinta saitaga yana a yanda tashigo ta iskeshi, saurin janye idonta tayi da matuƙar mamakinsa, kenan duk abinda take yana kallo, muryarta na rawa tace, “Dad ne yace dama na maka magana ya shirya zai wuce”.
     Manyan Idanunsa da suka ƙara girma saboda barci ya buɗe ahankali yana kallonta, batareda ya tankaba ya tashi zaune ya zuro ƙafafunsa alamar zai sauka.
    Fita Ummu tayi tana kuma jaddada mamakinta akan halin wannam mutumin.

      Kodama ta dawo falon saita iske Attahir yazo harda Ahmad, ga kulolin abinci alamar breakfast yakawo musu.
     Saida ta sanarma Dad yana zuwa sannan suka gaisa da Attahir ta ɗauki Ahmad daya baro jikin Dad ya nufota tamkar ya ganeta, dan yaron akwai wayon tsiya masha ALLAH.
      Bayan Ummukulsoom ta ɗauki Ahmad saita nufi komawa ɗakinta, da sauri taɗanja baya saboda karo da suka kusanyi dashi, ya sako blue ɗin t-sheat a saman 3queater ɗin wandonsa. Ganinsa yasaka Ahmad fara zamewa daga wajenta yana miƙa masa hannu.
      Gani tai kawai ya miƙo masa hannu alamar ɗaukarsa shima, babu yanda ta iya dole ta miƙa masa shi, wajen ƙoƙarin ɗaukarsa hannunsa ya gogi ƙirjinta.
    Saurin matsawa tayi saboda jin abinda batai zatoba, shi kansa saida zuciyarsa tai wata irin harbawa, amma a fili saiya kuma tamke fusaka yana barin wajen tamkar ba ayi komaiba.
      Tunda ta shige bata sake fitowa ba har Maman Ahmad tazo, itacema tabiyota da breakfast ɗin.
         Sai da Attahir ya kira wayar maman Ahmad akan Ummukulsoom tazo sannan tataso ta fito.
     Dad da Yaa Amaan kaɗai ta iske a falon zaune, kansa a ƙasa alamar nasiha ake masa.
     Guri Ummukulsoom tasamu ɗan nesa dasu zata zauna, amma sai Dad yay mata nuni da kusa da Amaan dake zaune a kujera 2seat.
       Bata zauna a kujerarba dai ta zauna a ƙasa kusa dashi sai dai  akwai tazara a tsakaninsu.
        Dad yay gyaran murya yana gyara zamansa idonsa a kansu. “To Alhmdllh da ALLAH ya nunamin wannan rana, Fodio ga Ummukulsoom nan matarka dana ɗaura muki aure, bakuma komai yaja hankalina dayin hakanba sai ƙyawawan halayya dana lura tana dasu, ina mai ƙyautata maka zaton samunta fiyema da yanda kake zato, ina fatan zaɓina bazai zama abin wulaƙantarwa daga gareka ba, idan kayi haka kuma ka tabbata ni kaimawa, dan na yarda da tarbiyyar daka samu ɗari bisa ɗari”.
       Da ƙyar ya iya dai-daita kansa yace, “Insha ALLAHU Dad, ina godiya, ALLAH yaƙara nisan kwana”.
       “Amin” Dad ya amsa yana maida kallonsa kan Ummu da kanta ke a ƙasa tana share hawayen da batasan dalilin yinsuba.
     “Ummukhoolsum!”.
“Na’a Baba”. ‘Ummu tafaɗa muryarta na rawa’.
        “Ga mijinki nan Fodio, ina fatan zaki kwantar da hankalinki kimasa biyayya, karnaji wata matsala kinji, ALLAH ya baku zaman lafiya da da zuria ɗayyiba mumina”.
      kai Ummu ta ɗaga tana hawaye, bakinta yagaza furta komai. Dad ya kara musu nasiha sannan ya miƙe yana kallon agogon hannunsa. 
      “Kunga bara na wuce naga ina neman makara, ALLAH yabada zaman lafiya”.
    Mikewa Fodio yay shima, sai yanzu Ummukulsoom ta lura ya canja kaya ashe.
     Ummu naji na gani Dad da sukazo tare ya tafi ya barta, ɗaki takoma tana kuka, maman Ahmad taita lallashinta da mata nasiha. Harsu Amaan suka dawo daga rakkiyar Dad bata gama sakin jikintaba.
     Wajen sha biyu maman Ahmad ma tai mata sallama ta koma gida ɗora girkin rana……….✍????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button