NOVELSUncategorized

DIYAM 37

DIYAM Chapter 37
Tareda Naja’atu Lawal Rijau
Abatcha Motors

Da assuba na tashi kamar kullum, na cire hannayensa
daga kaina na mike ina kallonsa yana ta sharar baccinsa,

ban tashe shi ba tunda ni dai dama ban taba jinsa ya fita
masallaci ba, na tafi dakina na shiga toilet na kunna wa
kaina shower wai ko zata sanyaya min zuciya, inna wanke
jiki na sai in sake wanke wa in sake wanke gani nake
kamar duk Saghir dinne a mammanne a jikina, ji nake ina
ma ace zan iya cire fatar jikina in sake wata wadda Saghir
bai taba ba? Nayo wanka na na fito na saka doguwar riga
ta hijab nayi sallah ina addu’a Allah ya kawo min karshen
auren nan, sai kuma na chanja nace idan auren shine mafi
alkhairi a gare ni Allah ya cire min Sadauki daga zuciyata
ya shiryar da Saghir ya saka min sonsa a raina. Ko da
banso shi ba at least in rage tsanarsa hakan zai dan rage
min zafin da nake ji a zuciyata.
Ina nan kan sallayata har gari yayi haske rana ta fito, sai
naji an bude kofar dakin da nake, na juya ina kallon Saghir
daya dau wanka yasa gayunsa kamar kullum sai kamshi
yake, ya tako har tsakiyar dakin da takalmin sa a kafarsa
yace min “ki zo ki bani breakfast zan fita” na dauke kaina
gefe saboda wani takaici da ganinsa ya saka min nace “ka
kawo abin breakfast din ne?” Yace “ki duba dakina akwai
kayan tea sai ki hada min tea, akwai kuma kwai a kitchen
sai ki soya min” daga haka ya fita, na tashi nayi abinda
yace na kawo masa palon sama yana zaune yana kallo,
na zauna ina kallonsa har ya gama ya karkade jikinsa zai
tashi nace “mu kuma fa? Me zamu ci” ya tsaya yana
kallona yace “babu abinci a store?” Nace “ka ajiye ne?”
Yace “bana son maganar banza in babu kawai kice min
babu” nace “ai ka fini sanin babun” yace “ku sha tean
mana to, kafin lokacin abincin rana ai zan dawo” yayi
hanyar waje nace “in baka dawo ba nima zanyi Allah ya
isa” sai kawai ya juyo ya kalleni yayi murmushi ya fita.
Bai dawo ba din kuwa. Haka na samu wata guntuwar
shinkafa a store muka dafa fara dama uwani tayo guzurin
yaji muka ci da mai da yaji. Bai dawo ba sai dare, daren
ma sai bayan mun kwanta kuma nasan maybe yayi hakan
ne dan kar inyi masa mitar bai ciyar dani ba. Da safe ina
kasa muna gyaran gida sai gashi ya sauko, ya leka wajeya
kira mai gadi sai naga sun hau sama tare ya bashi akwati
ya sauko dashi kuma daga ganin akwatin nasan da kaya a
ciki, akwatin cikin kayan lefe nane. Nabi mai gadin da
kallo har ya fita sannan na hau saman muka hadu dashi
yana kokarin saukowa nace “wancan kamar kayana naga
an fita dasu, ko dai ido na ne?” Bai kalle ni ba yace “aro
na dauka, zan siya miki wasu idan wadansu kudina da
nake jira sun zo” nace “ko aron ne ai ana tambayar
mutum kafin a dauki aron kayansa, kuma ni ban bayar da
aron ba a dawo min da abi na” yace “ta yaya zamu zauna
da kaya cikin akwati alhalin store din abincin mu babu
komai? Ai ba kyauta nace ki bani ba aro ne kuma zan biya
ki kin dai san ni ba talaka ba ne ba ko?” Kafin in bashi
amsa ya fice. Na shiga dakina na tarar duk ya hargitsa
min kaya, kusan duk kayan lefe na masu tsadar ya dauke.
Bakin ciki ya kama ni kawai sai na zauna ina kuka, sai na
tambayi kaina, wai yaushe ne zanyi farin ciki ni kam,
yaushe ne zanyi murmushi, irin geniun smile din nan mai
zuwa har zuci.
Ya siyo mana kayan abinci sosai, ya kuma bani 10k ya ce
kudin cefane “saura kuma a karar dasu da wuri ace min
babu” sauran kudin kuma bansan me yayi dasu ba.
Kwana biyu bayan nan, tunda rana naga yana tayi min
fara’a sai nasha jinin jikina, da dare ina kwance a daki sai
gashi ya bude kofa ya shigo nayi sauri na rufe idona dama
fitila a kashe take, yace “Diyam, Diyam” nayi banza na
rabu dashi. Sai ya hawo kan gado na sai nayi juyi na fara
munsharin karya, irin wannan munsharin mai kamar kakin
majina, sai yayi tsaki ya tashi ya fita. Na gyara kwanciya ta
a raina nace “sai dai kaje ka rungumi pillow bani ba” and
that got me thinking, this is his second attempt a kaina a
cikin sati daya da dawowa ta, amma wancan karon wata
na bakwai a gidan sa tun randa yayi raping dina bai kuma
kallata da wannan maganar ba, menene ya chanza yanzu?
Sai nayi realising cewa da yana da kudi yanzu bashi dasu,
meaning da yana iya siya a waje yanzu ba zai iya siya ba,
wato wannan shine dalilinsa na yarda da dawowa ta irin
ga banza ta fadi dinnan ko? Ni kuma indai haka ne bazan
yarda ba sai nasan yadda nayi na karbar wa kaina yanci.
Sai kuma nayi mamakin kaina yadda nayi realizing Saghir
yana neman mata amma ko a jikina wai an tsikari
kakkausa, ko kadan banji raina ya baci ba alhalin ko a
yanzu da nake matar wani in nayi imagining Sadauki da
budurwa ba karamin baci raina yake yi ba ballantana inyi
imagining dinsa yayi aure. I can only imagine yadda
Sadauki yake ji a ransa a yanzu da make matar wani, har
na haihu dawani. Ko ya yake ji? Ko ya yake coping?
Washegari ya tashi yana ta fushi, ni ko kallo bai ishe ni ba.
Zai fita yace “zanyi baki anjima, abokaina ne manyan
mutane ne sun takura wai sai sunzo sun ganki. Please
don’t embarrass me, kiyi musu abinci kuma kiyi shiga mai
kyau kisa kayan da zasu kara miki girma”. Bai jima da
tafiya ba dai sai gashi ya dawo da kaji wai duk ayi musu.
Mukayi abinci ni da uwani muka jera a dining, muka gyara
gida tsaf yana ta kamshi na tafi sama nayi wanka na saka
wata doguwar riga ta atamfa, dama ba kwalliya nake yi
ba, na saka hijab nayi sallah ina zaune akan sallaya ya
shigo yace “gasu sunzo, kuma please ki cire wannan
dogon abin” ya juya ya koma, na tsaya ina tunanin
menene dogon abin, doguwar rigar ko kuma hijab din?
Na tashi na gyara hijab dina na bishi, suna zaune a palon
kasa kusan su biyar duk irin sa, yayan masu kudi masu ji
da kansu. Na zauna a hannun kujera na gaishe su suka
amsa, suna tsokana ta wai amaryar da ake boyewa, ina
kallon Saghir yana ta harara ta nayi kamar ban ganshi ba
sai cewa yayi “kin zo kin zauna kin saka mutane a gaba,
ba zaki tashi ki kawo musu ruwa ba?” Na fahimci lallai so
yake ya dizga ni a gaban abokan sa ya nuna musu ba
sona yake yi ba, ni kuwa bai san yadda nake jin haushinsa
yafi yadda yake jin nawa ba. Na mike sai cewa yayi “au
ina miki magana ba zaki tsaya ki gama ji ba sai ki wani
tashi ko?” Na dawo da baya na tsaya a gabansa nace
“wanne daga ciki kake so Saghir? In tsaya kayi min fadan
ne sai in kawo musu ruwan ko kuma in tafi in kawo musu
ruwan sai kayi min fadan which one will you like first”.
Kusan gaba-daya suka kwashe da dariya. Ya kasa cewa
komai ya tsaya yana kallona, sai na daga kafada nace
“abinci yana kan dining, you can serve them in ka gama
fadan” na juya nayi hayewata sama. Ni kaina nasan na
gama da Saghir, amma kuma shi ya jawo wa kansa, me
yasa zaiyi tunanin bara ya wulakanta ni a gaban abokan
sa? Ko yana ganin hakan zai kara masa class ne a cikin
su.
Ina nan zaune naji fitarsu a motoci sai kuma naji yana
hawowa, nasan zuwa zaiyi mu yita amma sai naji bana jin
tsoronsa, ya shigo har dakina ya karaso gabana ya tsaya,
kawai sai jin saukar mari nayi a fuskata, saboda karfin
marin har saida na daina gani for some seconds sannan
ya sauke min a daya side din. Sai da naji taste din jini a
bakina. Ya nuna ni da dan yatsa “ke har kin isa ki ce zaki
gaya min magana a gaban abokaina, me kika dauki kanki
ne? Wallahi ki bini a hankali Diyam in ba haka ba
watarana sai na kai gawarki gida” Ya juya ya fita.
Na rike fuskata na zauna a bakin gado, bazan iya tuna
sanda aka taba marina ba, to ni waye ma mai dukana in
banda inna itama kuma mostly a kafa take dukana.
Hawaye ya fara bin kuncina ina lissafa irin abinda zai faru
da ace da ne wani yayi min wannan marin a gaban
Sadauki. Nice kuka har magrib ina tayi, daga yin Sallah
kuma sai zazzaɓi mai zafi ya rufe ni. Uwani ta hawo taji ni
shiru sai ta tarar bana jin dadi sai ta zauna a waje na har
saida Saghir ya dawo sannan ta sauka.
Tun daga ranar ban kuma lafiya ba, yau zazzaɓi gobe
amai jibi ciwon ciki. Saghir kam fushi yake yi dani sosai ni
kuwa ta kaina nakeyi, bai ma kula cewa bani da lafiya ba
ballantana yayi tunanin kaini asibiti. Bayan nayi kusan sati
ina jinya rannan uwani tace min “Diyam anya kuwa ba zaki
yiwa Saghir magana ya kaiki asibiti a gwada ki ba? Ni fa
ina ganin kamar juna biyu ne dake” sai naji wani amai ya
taso min, naje nayi na gama na dawo nace “ciki fa uwani?
Wanne irin ciki kuma?” Tace “ni dai na fada miki, kuma
kije a gwada ki gani” sai na hau sama da sauri ina jin
kamar labarin mutuwa ta uwani ta fada min, na fada kan
gado na kama kuka, na shiga uku ni Diyam, sai na fara
addu’a “Allah ka dube ni Allah, Allah kasa kar maganar
uwani ta zama gaskiya” amma kuma nasan rabo na da
period tun ina gidan mu, ga kuma abinda ya faru ranar
dana dawo.
Ina nan kwance Saghir ya hawo yana kwalla min kira, na
tashi na same shi a tsaye a kofar dakinsa yace “ki shiga ki
gyara min dakina” na wuce shi na shiga na fara harhada
uban lodin kayansa duk daya barbaza a dakin, ga zazzaɓi
gashi jikina babu kwari saboda amai. Shi kuma ya tsaya a
kofar dakin ya harde hannayensa yana kallona. Na daga
wata riga kenan naji kamshin turarensa ya doke ni sai
amai, da kyar na karasa toilet na fara karara wa sai ya biyo
ni ya tsaya a bakin toilet din yana kallona har na gama
sannan yace “baki da lafiya?” Bance masa komai ba yace
“me yake damunki?” Nace “zazzaɓi” yace “da amai?” Na
girgiza kaina da sauri nace “warin turarenka ne ya saka ni
aman” yace “amma ai kullum shi naje sakawa baki taba
aman ba sai yanzu. Are you pregnant?” Nayi shiru bance
masa komai ba sai yayi tsaki “ke bansan wacce irin mace
ba ce ke, daga an taba ki kadan sai ciki” naji wani abu ya
tsaya min a kirji na wuce shi na dawo daki ina cewa
“tunda dai bani na hau kan kaina nayi wa kaina cikin ba ai
da sauki. If you hate me that much ka sallameni mana in
tafi” ya biyo ni yana cewa “and who says I hate you?” Na
tsaya ina masa kallon kar ka raina min hankali, sai yace
“idan da bana sonki Diyam da tuni kina gidan ku wallahi ko
dan wannan rashin kunyar taki. Kuma yanzu ko dan
wannan samun cikin da ake yi ai ya kamata ki fahimci
cewa we are meant to be together. Ki kwantar da hankalin
ki muyi rayuwar aure kinki, kin ki cire that Sadauki of a
person daga zuriyar ki kuma… ” Ban karasa jin abinda zai
fada ba na fito daga dakin na koma nawa.
Washegari shi ya tashe ni da safe wai in shirya muje
asibiti, muna zuwa ya samu doctorn dana lura kamar sun
san juna yace “PT zaka mata Please” sai doctorn yayi
dariya ya kira wata nurse ya hadamu muka je tayi min.
And it came back positive. A ranar nayi kuka kamar idona
zai fita.
Tunda muka koma gida ya tare a dakina yana jinya ta,
shine bani magani shine yi min sannu da su hada min tea,
ni duk na dauka jinyar Allah da annabi ce sai daya sauke
bukatunsa a kaina sannan na fahimci inda jinyar ta dosa.
Kayan lefe dai mun cinye su, babu biya babu ranar biya.
Sai kuma yazo ya dauki set din kayan kallo na palon sama
ya siyar, daga nan sai set din gadon extra dakin da bama
amfani dashi a sama, sai deep freezer. Duk abinda aka
siyar daga an dan siyo kayan abinci an dan bani kudin
cefane bana kuma sanin inda sauran kudin sukayi. A haka
har cikina ya tasa yayi wata biyar.
Ranar nan na shiga kitchen na rasa me zan dafa mana na
hawo sama na same shi akwance a gado yana daddanna
waya. Nace “babu fa abinda za’a ci a gidan nan” sai ya
saka hannu a aljihu ya zaro min yadin aljihun na karkade
min ya cigaba da danna wayarsa. Sai na samu kaina da
tambayar kaina menene role din Saghir a auren mu? Shi
aikinsa kawai shine yayi min ciki? Na shigo ciki na zauna
a kan bedside nace “Saghir idan ni da kai da uwani mun
zauna da yunwa wannan” na nuna cikina, “bai san babu
ba” ya kalli cikin nawa sai ya ajiye wayar yace “to wai me
kike so inyi? Ni fa ko kudin man da zan zuba a mota in
fita bani dashi, ko so kike a ganni a daidaita sahu ake
nuna ni a gari? Ko kuma so kike in ke bin gidajen masu
kudi ina cewa allazi wahidi? Ko kuma dako kike so in
dauka ko lebura ko kuma aikin mechanic? Na fahimci
abinda yasa ya fadi mechanic din, so yaje muyi fada inyi
zuciya in rabu dashi amma sai nace “eh, so nake kayi duk
abinda ka fada indai zaka samu halak dinka. Wai kai ba
kayi karatu bane ba? Ina takardun ka, ka karkade su ka fita
kane gurin abokan Alhaji su hada ka da connections din
da zama samu aiki. At least if you can’t be a good
husband try to be a good father”.
Bansan ya akayi ba kuma ina daki sai gashi da folder din
takardu yace zai je gida ya kaiwa Alhaji, sai kuma yace “in
na samo kudi a hannun Hajiya sai in taho mana da wani
abun a hanya”. Ni dai na rabu dashi a raina ina cewa lallai
gata mugun abu. Na tuno Sadauki da rashin zamansa a
guri daya, tun yana dan karamin sa Baffa ya nuna masa
neman kudi. Sai nayi murmushi ina lissafin irin kudin da
Sadauki zai tara in dai ya samu hanya.
Ban kuma tabbatar wa cewa Alhaji Babba ya fada kwata
ba sai da muka je gidan few days after that. Mota daya ce
a compound din, ita ma kuma daga ganin ta nasan an
dade ba’a hau ta ba, komai babu, ni sai naga gidan kamar
har wani duhu yayi. Shi kansa ya rame, kayan jikinsa sun
tsufa, na gaishe shi ya amsa yana ta yake baki. Muka
shiga cikin gida suna ta kallon cikina, Hajiya Babba har da
yar min da magana wai da Inna ta hanani komawa bayan
ni ina son mijina, ni dai bance mata komai ba. Itama naga
dakinta yar aiki daya ce kawai kuma itama na tabbatar
yan uwanta ne suka dauko mata. Hajiya Yalwati kam Allah
ya taimake ta ƴaƴanta manya su uku sunyi nce sun fara
teaching dan haka su suke daukan nauyinta da kannen su.
Da zamu tafi su murja suka ce zasu bi mu amma Saghir
ya rufe idonsa yace babu wadda zai dauka. Sai da muka
dauki hanya ne yake cewa wai nauyi zasu dora masa in
suka zo. Sai na tambayi kaina ‘ba shine namiji ba, babban
wa uba? Bashi ya kamata ya dauki nauyin kannensa ba
amma shine mai gudun ciyar dasu na kwana biyu?”
Bayan munje gida yake gaya min “Alhaji ya hada ni da
wani abokin sa shi kuma ya hada ni da wani mutum daya
bude kamfanin siyar da motoci kwanan nan. Gobe zanje
interview kiyi mana addu’a. Idan aikin nan ya fada ko?
Hmmmm, ba karamin kudi suke dashi ba a gurin nan
kuma kinsan accounting na karanta harkar kudin” ni dai
nayi addu’a amma bansa ka rai ba saboda bansa ran zai
samu aiki irin haka da wuri ba.
And to me surprise, sai gashi washegari da offer. “I nailed
it. Diyam, I got it. Wato managern ne da kansa ya ganni,
karamin yaro ne mai babbar harka. Kawai few personal
questions yayi min shikenan yace ‘you are hired’ just like
that fa, Diyam you are talking to the financial secretary of
Abatcha Motors”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button