NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 4

???? *WA ZAI FURTA?*????
              0⃣4⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Kinfi Alawiyya farin jini unex ta hannun damata ( Hussaina Nasir )* Allah yabar kauna. *Alawiyya*????????????

*Federal University dutsinma*

Tun lokacin da Bilkisu ta siya ma Anwar break abun ya mishi tsaye cikin Rai saboda karon farko daya taba karbar kyauta daga hannun wani ko wata bayan iyayen sa.
  Wasu mutanen basa raina alheri ko kadan hakan yasa Anwar yaji Bilkisu ta shiga ransa farat daya ba don Yana sonta ba ko makamancin hakan sai dai lura da yanayin takun yarinyar, Bata da Jaye Jaye kuma baya tunanin zatayi yawan surutu.
  Ita kuwa tuni ta fitar da abun a ranta saboda bata dauki hakan da tayi da wani girma ba, kawai she feel like making him happy kamar yanda ita ma ta kasance cikin Jin dadin bayar da lokacin sa gareta ya koya mata karatu .
 Ya kasa sukuni ganin lokacin yakeyi baya gudu duk wadanda keson Karin bayani ya Basu hakuri sai zuwa dare, yanayi Yana duba agogo da Kuma wayar sa Koda zata Kira, me yasa ni ban karbi wayar tata ba? Mtsew yaja guntun tsaki, uku na bugawa ya kasa hakura kawai yayi wanka ya shirya cikin kananan Kaya gayu yayi sosai, uku da ashirin ya Isa makaranta, anata Kiran sallar la’asar hakan yasa Shi wucewa masallaci. Lokacin da aka fito sallah uku da hamsin, ya kura ma wayar sa ido kamar ya rotsata da kasa, shin Wai bazata kirani ba? 
  Bummmmm……ta fada daga bayansa alamar tana son bashi tsoro.
  Ya tuntsure da dariya lokaci guda Kuma zuciyar sa ta mishi sanyi, Ni Zaki ba tsoro? Ko kin dauka kowa irin ki ne matsoraciya?
 Tayi murmushi kawai, Yanzu na fito masallaci Ina Shirin kiranka na hango ka…….. Ba wani baki da niyyar kirana tun yaushe Kika karbi wayar ba sai ki yi mun ko flashing bane don Nima nayi saving taki?
  Suka jera suna tafiya, 
No need….kawai na barta ne sai lokacin da Zan Kira.
 Bana daukar wayar da bansan no. Ba so better call me to save yeye.
 Ta kyalkyace da dariya yabi fararen hakoranta da kallo…….Ni ce yeye?
 Ya mata banza kawai.
Karo sukayi da Dr Dan Musa akan hanya, ta gaida Shi Anwar kuwa ko kallo ya wuce abinsa, ya bishi da kallo cikin bacin Rai laifi biyu gashi suna tare da Bilkisu sannan Kuma gashi baya gaida Shi kusan sau hudu kenan suna haduwa Anwar din na watsin kasa kasa dashi, don akwai lokacin ma da suka hasu banki Anwar din ya kalleshi ya watsar ba tare da ya gaida Shi ba. Ya kuta cikin Rai zaka ci ubanka, ya kalli Bilkisu sai Ina Kuma haka kuna da evening lecture ne?
 A’a zamuje karatu ne Anwar zai mun bayani. Wanene Anwar?
Ya bukata, Hamza Yusuf wancen ta nuna Shi da yatsa Yana tsaye gaba kadan Yana ta faman latsa waya da alama ita yake jira, Au wancen Dan iskan yaron Mai girman Kai Wanda ya Raina mutane?
Ta zaro ido……raini Kuma sir?
Ya harareta kawai ya wuce abinsa yabarta tsaye. Ta bishi da kallo tana mamakin me ya hada Shi da Anwar din domin tasan Shi mugu ne ana kuka dashi a department.
Me ya hada ka da Dr Dan Musa? Ta karasa inda yake tsaye da sauri.
Ya kalleta cike da mamaki. What the hell are you talking about. Meye zai hadani dashi kuwa inba Yanzu da ya ganmu tare ba…….kada ka mishi fassara, yace ka Raina mutane and this is the second time I hard about something like this a bakin lecturer.
Me yasa baka gaida Shi ba Yanzu Kuma kaji na gaida……saboda baya gaba na.
Malama stop interrogating me about those idiots…… idiot? Anwar kanka lafiya kuwa?
Bai tanka mata ba har suka zauna wani class.
Ki fiddo littafin da zamuyi.
Bazan fiddo ba ….me yasa malamai ke cewa ka Raina mutane Kai kowa ma daukar ka yakeyi ka Raina kowa……Amma ai ke kinsan ban Raina ki ba ko? Hasali ma tsoron ki nakeyi to meye zai dameki? Ya karasa maganar Yana Yar dariya .
Ba wani… ai su malaman ka…..
Bilkisu me yasa kike kirkiro unnecessary problem ki dorawa kanki?
Meye abin dagewa anan Wai? Sun Dade basu kirani da Dan rainin hankali ba so what?…….sai suyi maka mugunta a result, 
Basa iyawa ki daina damuwa……
An Gaya ma na damu ne?
Kai ba a Isa a fada ma kana kuskure ba ka gyara.? Ta dunga balbala mishi masifa.
Hannunsa duka biyu ya goya a kirji tare da tsareta da ido Yana mamakin.
Meye abin hakikancewa anan? Ita meye nata aciki? Wai me yasa take kokarin shiga harkarsa ne ma?
Ya sha mur Yanzu kin kirani anan ne don ki nemi rigima ko kuwa karatu zamuyi? Cos I’m tired of it already.
Ya janyo littafin dake gabanta bari mu Fara ………..
Gab da magariba suka gama, tare suka taho yana ta binta, har suka karaso kwanar gidan ta, lokacin ne ta kalleshi zaka bini ne?
Ashe kin gane , ya fada Yana murmushi…. 
Tabbb da ka ci na jaki kuwa muyi maka ihu Kato.
Wannan karon dariya yakeyi sosai nine katon?
Eh Mana namiji a gidan mata.
 Kin San ma’anar katoa hausa kuwa? Ta kalleshi eh Mana gashi na fada kato namiji kamar Kai……barawo ake ce ma Kato fa ni barawo ne?
Kai Ni dai bance ba kada kamun fassara. 
Test din gobe ina bayanka please.
Da gaske kike?
Allah kuwa……
Okay ba damuwa.
Kiyi man flashing nayi saving no. Ki Mana.
Zan kiraka anjima kada ka damu ai na ce Zan karanta abinda mukayi inda na manta Zan maka waya ka tuna?
Ke ban yarda ba kirani Yanzu.
Allah Zan kiraka kaji na rantse.
Sai da safe gashi can an Fara Kiran sallah.
Kina korata ne? Me yasa like zaune a off campus bakya son hostel? Hakanan Ina da kyankyamin toilet maganar gaskiya Kuma Ina son privacy in ma life.
Kai me yasa kake son zaman hostel?
Kar na Zama Dan iska Shi yasa a off campus mata zasu dameni Yanzu ma Yana iya……harara ta balla mishi sannan ta buga tsoki kaji dasu can, sai da safe………….. Bilkisu…. Bilkisu… Bilkisu….. Amma inaaaa tayi shigewar ta gida ta kyalesa.
Yayi murmushi yarinyar rigimammiya ce wallahi. Kut! 
 Wai ni Anwar yau mace tayi wa tsoki banji haushi ba shin Wai wanna yarinyar wacece ita?
        **************
*KADUNA RIGASA*

Tunda suka Fara raba kwana matsaloli suka Fara kunno Kai daga bangaren Ummi, duk ranar girkin ta sai ta Mila tasha iska take data abinci wani lokacin sai dai Amirar ta dafa ma Yara indomie ko su Sha oat ko wani simple food, tun abun baya damun Amira har ta Fara Jin Yan aikin gidan kansu sun Fara korafi.
Gashi baya nan yayi tafiya.
Ranar da ya dawo kuwa akayi sa’a dakin amaryar yake.
Bayan sallar isha’i Yara sunyi barci ta sameshi acan. Yana kishingide bisa kujera ita Kuma tana saman kafet tana chatting……dukkan su ta kalla sannan ta watsar.
Ya Dan zabura Amira yau kece anan? Lafiya dai ko?
Domin bai taba ganin ta sashen ba idan Yana nan wata kila ko tana zuwa sai idan baya nan ne.
Zuwa nayi in tambayeshi ka, Kaine ka Sanya matar ka ta ringa yin abinda taga dama gidan nan?
Ya zaro ido Ni? Me tayi?
Ta zaburo Au karata…..ya daka mata tsawa idan Kika Kara magana bakin auren ki wallahi kada ki dauki mutane Yan iska ke gidan ku ba manya ne?
Abinda kikeyin mun daga ni sai ke Ina shanyewa idan Kika ce zakiyi gaban jama’a kece Masha wuya.
Amira me ya faru? Zo ki zauna….. Ba Zama ya kawo ni ba.
Ina so in sani cewa Kaine ka ce matar ka ta ringa Mana horon yunwa a gidan nan? Daman ka sanya doka ne na Mai miji tayi girki don ka fifita daya?
Tun zuwan Ummi gidannan a duk lokacin da aka ce kasa kafa kayi tafiya to mu da abinci sai taga dama Yara har sai sun Fara kuka sai dai a nema masu wani abun.
Bata ganin kowa da mutunci ban Isa in nuna mata kuskure ko shawara ba shine na ke son gani a gabanta ka fada mun idan Kaine ka daure mata…… Wallahi bani da masaniya.
Kuma me yasa tun farko Baki fada min ba ……saboda Ina tunanin ko hada bakunta ne Shi yasa Amma na lura galari ne da daurin gindi….wurin wa? Na rantse da Allah ban sani ba.
Ke Ummi kinji abinda ta ce haka ne?
Ta yatsina fuska, eh saboda Ni ko a gidan mu ba saba dafa abincin gandu da……what?
Nan gidan ku ne?
Da sauri ta kalleshi.
Ya zaburo na ce Nan gidan ku ne?
To bari kiji in fada Miki Nan gidana ne matukar kina son Zama Dani wallahi sai kinbi abinda nake so da abinda na tsara.
Waye zakiyi ma gadara kice gidan ku? Idan gidan naku kike so sai a maida ki kije kiyi abinda kike so Amma anan matukar kina son Zama to ya Zama wajibi kibi abinda nake so. Bazan taba daukar raini da wulakanci ba ai nasan halinki na ga take taken ki na rashin tarbiyya da tsageranci idan nayi la’akari da yanda kike datsa mun magana many times.
Ya nuna ta da yatsa wallahi ki taka a sannu……Amira dai juyawa tayi abinta.
Ya kirata Amira tana juyowa tace abinda ya kawo ni kenan idan itama tana da nata korafin Ina jiranta…..tayi ficewarta.
Amma ke wallahi Baki da wayau Ummi. Da kin San Hali irin na Amira da kin lallabata Kun zauna lafiya. Kin Aure mata miji Kuma kin dawo kina wani hauka…… Gori zaka mun? Ai ba ni na kawo kaina ba……. An Miki gorin.
Wallahi matukar kina son Zama Dani cikin Jin dadi sai kinbi Amira Kun zauna lafiya…..fuuuuu ya tashi ya shige daki ji kake gammmmm.
Kwalla suka zubo mata, zuciyarta tayi mata kunci wanna masifa dame tayi Kama?

       ******************
*Federal University dutsinma*

Sun fito lecture 9-11 kenan aka aiko registration officer dinsu na kiranta.
   Babban mutum ne ana yawan Kira mishi kirki da mutunci.
Tana ta faman tunani ko lafiya?
Bayan sun gaisa ya mata fatan alkhairi sannan yace yaji dadin gajin result dinta da Kuma yanda ta Sami shaida a department na tare mutunci amatsayin ta na budurwa Kuma ita kadai mace musulma a ajin.
Sannan idan har tana da wata matsala kada tayi kasa da guiwa ta je ta sanar dashi in shaa Allah zai taimaka.
Tayi godiya sosai, ta koma aji dayake suna da wata lecture ta 11-1 sannan suyi test 2-4.
Sadeeq babban abokin Anwar, Wanda kowa yasansu tare tun aji daya, ya hangota yace mutumen ga fa bilky can .
Yayi kamar baiji Shi ba miskilin……..


*Zainab wowo*..????✍????ayi hakuri da kadan pls

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button