NOVELSUncategorized

DIYAM 38

❤ DIYAM ❤

By

Maman Maama

Episode Thirty Eight : Subay’a

Na rike baki ina dariya, ko ba dan Saghir ba ko dan ni kaina da abinda yake cikina nayi murnar wannan aikin. Nace “Masha Allah.
Alhamdulillah. Amma fa kayi sa’a, abinda mutane sai su dade suna neman aiki basu samu ba amma kai kaga lokaci daya ka samu” yayi dariya yana zama akan kujera yace “maybe mutanen da kike magana akan su basu san inda ya kamata su nemi aikin ba ko kuma basu dace da aikin ba. Kinsan appearance matters alot a gurin neman aiki, yanzu misali ni, kowa ya ganni yasan na chanchanta da post din dana samu” na zauna ina mamakin bragging irin na Saghir, nace “komai fa a rayuwa yana da lokaci, wadanda basu samu aiki ba lokacin samun su ne baiyi ba, kai kuma daka samu lokacin kane yayi, ita rayuwa…..” Ya daga min hannu “don’t spoil my mood please. Je ki kawo min ruwa” nayi ajjiyar zuciya na tashi.

Ranar daya fara zuwa office ne bayan ya dawo na tambaye shi “to an baka office? Da fatan sun fara baka aiki kanayi” yace “wanne irin aiki kuma?” Nace “rubuce rubuce mana, ba shine aikin secretaries ba?” Yayi tsaki yace “fin sec fa aka ce miki, ni harkar shiga da fitar kudi a companyn ne kawai part dina, besides, ina da mataimaki so shi zaike handling duk aiyuka” nace “so? Kai menene naka aikin?” Yace “who cares about aiki ne wai, what I care about is the salary kuma zasu ke bani mai kyau shikenan”.

Tunda aiki ya samu kuma shikenan Saghir ya koma tsohuwar rayuwar sa, inya fita tun sassafe baya dawowa gida wani lokacin ma har sai nayi bacci. Baya zuwa gida a bige, amma hakan bawai yana nufin ya daina bane ba dan sau da yawa in ina gyaran kayansa nakan ji wannan warin a jiki, sai dai bani da wani kwakwkwaran hujja. Yana ciyar damu, duk da dai considering yadda yake kashewa jikinsa kudi baya yi mana yadda ya kamata amma dai muna cin abinci. Shi kuwa kullum cikin sababbin dinkuna yake yakance “gwara mutum yayi dressing sosai kar a raina masa hankali”.

Cikina yana ta girma abinsa, ni kuwa babu komai a raina sai fargaba dan kuwa har yau ban manta da wahalar da nasha a waccan haihuwar ba, gashi wannan cikin duk da cewa daya ne a ciki amma tafi wancan cikin girma, wannan yasa tun cikin yana waya bakwai na tattaro kayana na dawo kasa kusa da uwani kuma kullum ways ta tana kusa dani dan am not looking forward to haihuwa ni kadai irin waccan.

Amma lokacin da muka je scanning tare da Saghir, bayan an gama mun zauna sai doctor yace “am afraid ba zaki haihu da kanki ba, dole za’a yi miki cs ne” duk muka bude baki da mamaki, Saghir yace “ta taba haihuwa fa doctor, twins ma” doctor ya dauko takardar scan din yace “tana da abinda a likitance muke kira da placenta previa. A ka’ida in aka tashi haihuwa ɗa ne a farko sai an haife shi sannan sai mabiyya ta biyo baya. But in her case mabiyyar ce a farko sannan dan, meaning ko da ace ta fara labour to placenta ce zata yi blocking babyn yadda ba zai fito ba so babu yadda za’ayi sai dai ayi delivering through cs” na fara kuka, ni takaicina shine yanzu wai yanka cikina za’ayi a fito da babyn ni Diyam, kai mata munga ta kan mu. Saghir yayi tsaki yace “kuma menene abin kuka a ciki? Ke da ya kamata kiyi murna ma babu ke babu wahalar haihuwa. Sai ni aka bari da wahalar kudi”. 

Alayi fixing date, a week to my edd sai dai da sharadin in naji nakuda kafin lokacin muyi sauri mu tafi. Na dage kullum da addu’a, na kuma gayawa su inna suma suka tayani da addu’a har Allah ya nuna mana lokacin. Mama ce tazo gidan muka tafi tare, dama Inna tunda nayi aure bata taba zuwa gida na ba. Tun a day to aikin mukaje suka bamu gado muka kwana a can, sukayi duk gwaje gwajen da zasuyi sannan washegari sai ga Hajiya Yalwati tazo daga gidan Alhaji Babba, har aka zo aka gama shirya ni babu Saghir babu labarin sa. Naji duk jikina yayi sanyi. Anzo ance lokaci yayi na dauko waya ta and I found myself dialing number din Sadauki, hoping to hear his voice just once more amma naji a kashe na kashe wayar na ajiye feeling so lonely kanar ni kadai ce a duniyar. Mama da Hajiya Yalwati suna ta lallashina suna min addu’a a haka aka shiga dani.

Aikin mai bacci akayi min saboda jini na yaki karbar na ido biyun. Dan haka duk abinda akayi ban sani ba har aka gama aka fito dani dakin hutawa. Anan ne na dan farka kadan naga Inna a zaune kusa dani ta rike hannuna, gefe kuma Mama da baby a hannun ta “Sadauki” na fada cikin bacci, “inna ki kira Sadauki kice yazo ya duba ni” sai na kuma komawa bacci. Sanda na sake farkawa doctor na gani da nurse a kaina, suka yi min sannu daga nan na sake komawa.

Sanda nayi final farkawa kuma babu kowa a dakin sai ni kadai, na bude idona ina ta kalle kalle ina jin kaina yana ciwo sai na hango Saghir a can kusa da window da alama waya yakeyi. Irin yadda naga yana bada respect ga wanda suke wayar yasa ni son sanin ko wanene saboda ban taba ganin yana magana irin haka ba. Sai daya gama sannan ya juyo, muka hada ido yayi murmushi ya nuna wayar yace “my boss. Ya kira yaji ya jikin ki saboda na fada masa za’ayi miki aiki. Yana da kirki sosai. Can you believe he paid for everything hadda karin kudin ragon suna?” Na rufe idona na dauke kai ina jin haushinsa har cikin raina, wato abinda zai fara fadamin kenan bayan an yanka ni an fito da jaririn daya saka a ciki? 

Sai yazo ya dafa kafada ta “am sorry banzo ba tun jiya, I am not good at all this emotional stuff ne shi yasa nayi zamana a gida kawai” sai kuma ya juya ya tafi gurin crib din baby ya dauko yana murmushi, na yi kokarin tashi amma na kasa nace “kawo min, menene?” Yayi dariya “au baki ganta ba? Baby girl ce, so beautiful like her mother” this is the first time daya kirani beautiful. Ya karaso ya sunkuyo yana nuna min ita, and he was right, she is so beautiful but tafi kama dashi because she looked just like twins dina, just ta fisu girma sosai. 

Nayi murmushi ina jin attraction so much like wanda naji akan twins. Na daga hannu na shafa kanta ina murmushi, yace “inye, Diyam an zama uwa, sai ki daina yi min rashin kunya in ba haka ba zan saka take rama min” ya jima yana ta surutun sa shi kadai sannan ya mayar da babyn cikin crib dinta ya dauko waya yayi ta daukan ta pictures sannan yazo yayi kissing dina a goshi ya fita.

Four days nayi a asibitin. I was so in love with my daughter naji tamkar na samu another reason to live. Sau daya Saghir ya dawo ya tambayi Inna ko akwai abinda muke bukata, ya dauki daughter dinsa sannan yayi min sannu ya fita, and that was all, ko abinci ba’a taba kawo mana daga gidan Alhaji Babba ba. Wannan yasa ranar da aka sallame mu muka wuce gidan Inna, shi ogan ma baisan an sallame mu ba sai daya kira ni naki dauka sannan ya kira uwani tace ai an sallame mu sai kuma gashi a gidan Inna, wai ai ba’a gaya masa zan zo gida ba, ya gama rashin kunyar sa ya fita. Inna tana ta mitar abin, a raina nace “zabin ki ne dai”. Tunda Hajiya Babba taje ta dubani a asibiti bata kuma zuwa ba, shima Alhaji Babba ko leke sai yace ace min baya jin dadi ni kuwa nasan dan mace na haifa ne da namiji ne da ko da rarrafe sai yazo.

Kullum in ana kallon yarinyar nan sai na tuno Sadauki, lissafin mu ni da shi shine mu haifi girl mu saka mata Subay’a, to ga girl din kuma na samu amma bata Sadauki ba, gashi ko sunanta ban sani ba duk da nasan yayi mata huduba gaya min ne kawai baiyi ba. Sai ranar suna da safe ya kirani “anyi radin suna a gidan Alhaji. An saka mata Saratu” sunan Hajiya Babba. Na runtse idona ina jin haushin sunan, nace “Allah ya raya, zamu sami wani sunan da zamu ke gaya mata” yace “already na riga na samu, Subay’a” na maimaita cikin mamaki “Subay’a?” Yace “yes, ko ba kya so?” Nace “no, ina so, a ina ka sami sunan?” Yace “my boss called, ya nemi alfarmar duk sunan da aka sawa baby a ce mata Subay’a, and I see no harm in honouring his wish. Besides, shi ya sayi ragon suna” ya karashe maganar yana dariya. Na kashe wayar ina mamakin me yasa boss dinsa zai ce a gaya wa babyn mu Subay’a? Inna ta tambayeni suna nace mata sunan Hajiya Babba ne za’a ke ce mata Subay’a, ta maimaita sunan tana kallona.

An dan taru a gidan sunan babu laifi, duk da cewa yan’uwa ne kadai kuma yanuwana da nasa duk daya ne, sannan ni ba kawaye ba ba makota ba, sai makotan mu na nan gidan da suka shishshigo mana. Abincin suna ma Saghir baiyi ba, cewa yayi ai ba shi yace in taho gida ba dan haka wanda ya kawo ni gidan sai yayi abincin sunan. Ragon sunan ma a gidan Alhaji Babba aka yanka aka soya aka kuma raba sai namu rabon aka kawo mana a kwano.  Bayan suna Mama tazo ta dauke ni muka je asibiti, ni na dauka wani check up za’ayi min sai naga an saka min wani abu mai kamar allura a dantsen hannuna ashe abin family planning ne aka saka min na shekara biyar.

Satina biyu a gida Saghir yazo yace ai na warke haka, in shirya in koma. Haka ina kuka ina komai na hada kayana dana Subay’a, Allah ma yaso Asma’u tana hutu nace tazo mu tafi, itama kuma tana shiga mota yace da iznin wa zan tafi da ita? And that kept me wondering if I don’t have a say in my own marriage. Shin miji shi kadai ne mai making every decision, ita mace bata da nata ra’ayin? Ko kuma ita mace bata da zuciya ne a kirjinta?

Bayan komawar mu gida ne nayi realizing something, Saghir’s weakness lies in his daughter. Yana son Subay’a sosai da sosai dan zan iya cewa yana sonta fiye da komai a duniya. Kullum tana hannunsa sai dai in baya gida ko kuma in zanyi feeding dinta. A lokacin ne kuma aka fara daukan sabon session na makaranta, a lokacin yan set din mu zasu shiga ss3. Nayi wa Saghir maganar komawa ta school sai cewa yayi “ita kuma Subay’a fa? Yaya kike so ayi da ita? Sai dai ki bari sai wani session din kafin nan tayi kwari” sai ya kara da cewa “in kuma kafin nan kin kuma samun wani cikin shikenan” ban mayar masa da magana ba saboda bai san zancen implant dina ba, haka na hakura da zancen makaranta dan babu yadda zanyi, in nace zan kai kara ma bayan sa za’a bi ace in bari yarinya ta tayi kwari.

A lokacin ne kuma yake sanar dani cewa ogansa zai tafi kasar waje karatu “he will be managing the company from there, kin san komai yanzu an mayar dashi computerized ballantana manyan harkoki irin na wadannan mutanen”  nayi kamar ban ji shi ba dan ni har na gaji da maganar ogan nan, kullum oga this oga that, oga yace kaza oga yayi kaza, I wonder me suke yi a office din bayan zaman hira.

Manage this please. Ina dan busy ne kwana biyu but I promise you a sweet episode tomorrow insha Allah.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button