NOVELSUncategorized

DIYAM 39

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Thirty Nine : The Boss

Bayan Shekara Biyar
Shekaru biyar suka zo suka wuce. A cikin su abubuwa da dama sun faru, na farko Hardo da Uwani duk sun rasu sati daya a tsakaninsu, Hardo ne ya fara rasuwa munje Kollere zaman
makoki itama uwani ta kama jinya sannan ta rasu ranar sadakar bakwai dinsa. Naji mutuwar Uwani sosai kusan fiye da yadda naji ta Hardo.

Rayuwata a gidan Saghir babu abinda ya chanza sai abinda ya kara gaba, ya dawo da shaye shayensa, ya kuma mayar da neman matansa openly wanda da yana dan boyewa amma yanzu kiri kiri yake yi musamman tunda kudade suna shigo masa, har gida mata suke zuwa neman Saghir, tun yana yi min karyar cewa abokan aikin sa ne har ya daina. Lokuta da dama kuma yana dora min laifin neman matansa, yace nice na gaza sauke masa hakkin sa shi yasa yake zuwa yake nema a waje wanda ni kaina nasan ina da laifi ta wannan bangaren, nayi nayi in tursasa zuciyata ko yayane in saka Saghir a cikinta amma taki yarda, Sadauki ya riga ya chika duk wani lungu da sako na zuciyata yadda babu wani bugawar da zata yi wanda babu tunanin sa a ciki. It was so hard living with a man while my heart belongs to another. Another din da ban ma san inda yake ba, babu amo babu labarin sa daga shi har yaya ladi. Sometimes sai in samu kaina da tambayar ko wanne hali yake ciki? Ko ya samu admission din yayi karatun? Ko rayuwa tana tafiyar masa dai dai ko kuma akasin haka?

Amma kuma hausawa sunce idan bera da sata daddawa ma da warinta. Ina da laifi a zaman mu da Saghir na sani amma shima ai da laifinsa, at least da ace yana treating dina well da ko ban so shi ba bazan ki shi ba, da zan iya managing in faranta masa as long as nima yana faranta min amma Saghir was doing total opposite of faranta min. Tsawa, hantara, bakar magana and occational duka duk ina samu daga gurin Saghir. Yana ciyar dani, barely, dan duk ranar dana ganshi da leda a hannu ko kuma naga yana yi min murmushi to nasan wani abun yake nema a gurina ni kuma a lokacin zan tayar da tawa tsiyar har sai mun rabu baran baran. 

Na koma makaranta bayan na yaye Subay’a, shima da kyar Saghir ya bari har saida na hada shi ta Hardo lokacin yana da rai sannan ya saka ni a wata government school anan bayan layin mu. Na fuskanci challenges da yawa a lokacin musamman saboda kasancewa ta matar aure a makarantar yan mata, kuma duk yan class din na girme musu dan ma bani da girman jiki dan haka da wahala ma ka gane shekaru ma, babu kuma wanda yake yarda nina haifi subay’a musamman saboda tana da girma sosai ita. Har nuna ni ake yi, ni kuwa sai naja kaina gefe nayi facing karatuna kadai wannan yasa har na kammala banyi wadansu kawaye ba sai dai gaisawa kadai. 

Inna tana ci gaba da kasuwancin ta, dashi suke ci, sha da sutura ita da Asma’u kuma dashi take biya wa Asma’u kudin makaranta, ta gaya min cewa tunda ta bar gidan Alhaji Babba, kaf yanuwan Baffa babu wanda ya taba daukar kwandala ya bata yace ki siyawa Asma’u ruwa, komai ita take yi musu wani lokacin ma harni take dan dinkawa kaya ta aiko min dashi tunda nawa mijin ba mai yi bane ba. Zai dai dinkawa kansa suttura kamar banza, yayi ta shiga yana fita, mayukan shafawarsa da turarukansa ma kadai abin jinjinawa ne amma ni kayan kyalliya tun na lefe na, da suka kare da wahala yake siyamin wani abu dana yi maganar kayan lefe na ma sai cewa tayi “da uban waye ya siya miki kayan?”. 

A lokacin da nayi candy a lokacin nake da shekara ashirin da daya, Subay’a tana da shekaru biyar. Har lokacin kuma ina nan jiya  iyau, babu abinda na kara a girman jiki sai ma kara motsewa da nayi wadda rannan da Inna take mita naji Mama tace yana da dangantaka da planning din da nake yi, maybe in ya barni zan yi kibar. Sometimes Saghir ma da kansa yana complain “Diyam kina da kyau sosai a fuska, mu maza kuma ba wannan kadai muke bukata ba muna son mace mai lady body parts” yana magana yana nuna irin parts din da yake nufi, nakan bashi amsa da “ai bani na halicci kaina ba, dan haka bani zakayi wa complain ba”.

Ranar nan nayi bakuwa, Maman Iman, tazo ta wunar min ita da yaranta da Asma’u na wadda ta shiga ss2 yanzu. Sai Maman Iman ta dauko wasu kulle kulle a leda ta jani bedroom dina ta fara tsaramin 

“kinga wannan garin da nono zaki ke sha ko da madara, kamar bayan la’asar haka yadda kafin dare ya fara aiki. Shi kuma wannan gumba ce ki adaba kina cin kayar ki a hankali tana da amfani sosai, wannan kuma na tsuguno ne, ki barbada shi a garwashin wuta sai ki tsugunna a kai ya shiga jikin ki sosai” 

Nasan magungunan menene dan kusan duk sanda naje gida sai ta bani irinsu, wani lokacin ina fitowa nake zubawa a kwatar kofar gida inyi tafiya ta. Amma sai nace “maganin menene wannan maman iman? Maganin tajika ne ko kuma na mayu” ta harare ne “a’a maganin sihiri ne. Kar ki raina min hankali mana Diyam, kinsan nawa na saka na sayi maganin nan kuwa? Wannan na tsugunnon da kyar ma na same shi shine na raba biyu na kawo miki rabi amma zaki raina min hankali” nayi dariya nace “maida wukar yayata ta kaina. Amma ki tafi da kayanki kar inyi miki asarar kudi dan wallahi ba amfani zanyi dasu ba” na fada ina dora mata akan cinyarta, ta dawo min dasu kan tawa cinyar tace “wallahi ki gwada ki gani, matar data bani ta tabbatar min da cewa indai kika yi amfani da wannan yadda kika san cingam haka mijin ki zai manne miki” nayi dariya na sake mayar mata nace “bana son ya manne min kamar cingam, ki kara akan naki sai abban iman ya kara manne miki kamar superglue” kafin ta bani amsa aka budo kofar dakin da kallo, Saghir ya tsaya yana kallon mu sannan yace “dan wulakanci kinsan ma dawo amma kika yi zaman ki ba zaki zo ki bani abinci ba” Maman Iman ta gaishe shi, yayi mata kallo daya ya dauke kai fice. Na mike nabi bayansa idona blurry with tears, yaushe wannan zubar hawayen nawa zai kare? Indai har nayi baki, ko kuma shi yayi baki, to kuwa tabbas sai ya wulakanta ni a gabansu, shi yasa har banaso inyi baki indai tana gida.

Washegari muna kasa ina taya Subay’a yin homework dinta sai gashi ya dawo daga office. Ta tashi da gudu ta tafi gurinsa shi kuma ya daga ta sama yana juyata suna dariya. Na gaishe shi ya amsa ciki ciki sannan direct ya wuce dining ya zauna ya zaunar da Subay’a a kan table din ya fara zuba abinci suna hira. Na taso na karba ina zuba masa nace “Subay’a sauka ki zauna akan kujera, na hana ki zama akan table ko?” Ta kwabe fuska tana kallonsa yace “ita da gidan ubanta, table din ubanta kuma abincin ubanta” yana fada yana yi mata chakulkuli tana babbaka dariya, garin dariyar har ta zubar da abincin dana fara zuba masa. Nayi ajjiyar zuciya na zagaye su na wuce kitchen na dauko duster nayi clearing gurin, sannan na sake zuba masa wani. Ban mayi mata fada ba dan nasan indai yana gurin to ban isa ba, maybe a karshe ya kare da zagina a gabanta. Sai daya gama sannan ya kama hannunta suka yi sama sannan suka sake saukowa tare, ya chanza kaya, yace min “zan koma office, muna ta shirye shirye oga zai dawo office ranar monday” na gyada kai nace “a dawo lafiya” a raina ina cewa “gyara ya dawo din ai ko ka mayar da hankali gurin aikin” ni nayi mamaki ma da har yau basu kore shi ba saboda sai yayi sati baije ba, na kuma ji labarin cewa company basa yadda da irin wannan kailular. 

Ranar Monday din da yamma, ina daki ina karatun novels a waya ina ta murmushi ni kadai ganin yadda mata suke soyewa a gidan mazajen su, sai naji shigowar sa, nayi sauri na boye wayar dan ya hana ni yace anan nake kara koyon rashin kunya. Ya shigo dakin babu sallama kamar kullum, ya karaso ya tsaya a gaban gado da leda a hannunsa yace “ga wannan ki tashi kiyi wanka ki saka, and please kiyi kwalliya mai kyau, in an jima da dare zamuje party” na zauna ina fito da kayan nace “party? Biki ake yi?” Ya zauna a kusa dani yana cire takalmi yace “no, wani surprise party ne muka shirya wa ogan mu a office, manyan ma’aikata duk kowa zai zo da familyn sa shi kuma za’a kira shi as far ana nemansa dinnan da gaggawa sai yazo zai gan mu” yayi tsaki “ni idea din sam bata yi min ba, tunda akace zai dawo kowa sai wani rawar kai yakeyi kowa yana neman gindin zama”. Nayi murmushi kawai ina duba kayan. Doguwar riga ce mai dan karen kyau daga gani nasan an saka kudi masu yawa gurin siyan ta kuma ba dan ni aka siya ba sai dan a burge mutane. Nayi wani tunani, I had never been to a party before, what if naje na kwabsa mishi? What if yaje ya dizga ni a cikin mutane? 

Kamar yasan tunanin da nake yi sai cewa yayi “but please Diyam, please don’t embarrass me a cikin mutanen nan, my entire reputation depends on this, please don’t do anything stupid” na mayar da rigar cikin ledarta nace “if it will make you feel better, ka tafi kai kadai kawai. Ni ba saba shiga cikin irin wadannan mutanen nayi ba” ya bude baki yace “salon a raina ni? Ace bani da iyali? Ki shirya kawai muje Allah dai ya kiyaye ni da jin kunya”.

Shi ya dauko Subay’a daga islamiyya ya kaita makotan mu inda naje ajiyeta sanda ina school. Sannan ya dawo yace min in nayi sallar magrib in shirya shima zaije ya shirya. Na tashi na shiga wanka kawai naji jikina yayi wani irin sanyi zuciyata tana ta bugawa, ni duk ji nake yi bana son zuwa gurin taron nan nasu gani nake yi kamar wani abu ne zai faru idan naje amma babu yadda zanyi haka nayi wanka na fito, na shafa mai na saka rigar daya kawo min. Golden color ce da akayi mata agon stones na silver, sai veil silver da stones golden. Ina sakawa Saghir ya shigo yana fadan har yanzu ban gama shiryawa ba, sai kuma yayi shiru yana kare min kallo da sakakken baki. “You look really beautiful” na dauke kai ina kallon kaina a mirror, babu abinda na sakawa fuskata in banda kwalli amma ta fito fes tana kyalli, kayan jikina sun kara haskaka fatata, sai naga ya saka hannunsa a aljihu ya dauko wata sarkar gold ya karaso ya saka min a wuyana, sai kuma yayi kissing wuyan, nayi saurin matsawa ina wayencewa da saka yan kunnayen daya ajiye. Ya sake biyo ni ya dauki comb yana taje min gashin kaina zuwa baya sannan ya saka ribbon ya daure min shi a keya side din hagu ya zubo dashi ta kafada ta yana cewa “let’s show them abinda matan su basu dashi” Na cire ribbon din ina girgiza kaina nace “babu kyau fito da gashi ga wadanda ba muharramai ba” yayi tsaki, “ke chafsi ne dake wallahi” a raina nace ‘naji din’ na daure gashina a tsakiya kamar kullum sannan na nannade shi sai nayi rolling veil din irin yadda naga su Rumaisa yammata suna yi. Sai kawai na tsaya ina kallon kaina a madubi, ban taba ganin nayi kyau irin na ranar nan ba. I looked like baby doll din da kullum ake kwatanta ni da ita. Na rike clutch silver sannan na saka silver hills masu tsinin da suka kara min tsaho. Ya tsaya a bayana yana kallona ta cikin mirror yace “perfect, ina ma kin fi haka girma but hakan ma is okay. Am sure babu wanda zaizo da mata irin tawa”.

A hankali muke tafiya, kowa da abinda yake zuciyarsa. Ni tawa zuciyar wani irin bugawa take yi wanka har daci naje ji a bakina, a tsorace nake sosai kamar in bude motar in fita a guje. Har muka je gurin, wannan shine karo na na farko da naje companyn Abatcha Motors. Dare ne kuma kusan duk fitulun gurin a kashe suke saboda basa son idan ogan yazo yayi tunanin wani abu, dan haka a lokacin bazan iya adar da komai dangane da yanayin gurin ba, baya muka zagaya mukayi packing, nan naga duk kowa yana packing ana ta fitowa kowa da matarsa ko budurwar sa. Saghir ya juyo ya kalle ni yaga yadda nake a tsorace yace “bafa cinye ki za’ayi ba, just do as i do. Duk wanda kika ga nayi wa magana sai ki gaishe shi, ba kuma cewa nayi ki durkusa har kasa kina gaishe da mutane ba” na gyada masa kai muka fita a tare, ya zagayo ya zura hannunsa cikin nawa muka shiga cikin mutane. Faran faran muke gaisawa da mutane kowa yana introducing matarsa, Saghir proudly yake nuna ni a matsayin matarsa, ina kuma lura da yadda idanuwa suke bina da kallon yabawa. Sai da aka gama gaggaisawa sannan muka zagaya muka shiga cikin building din gaba ki daya, nan ma babu fitulu sai guda daya dan haka dimly kowa ya samu guri ya zauna ana jiran wanda ya tafi tahowa da oga su dawo.una nan zaune ana dan hira kadan kadan suka shigo, sai aka yi saurin kashe fitila dayar da aka kunna gurin yayi duhu daga ki daya. Muna jinsu suka karaso suna yan maganganu. And my heart stopped at the sound of the voice I heard.

Sukayi unlocking kofar suka shigo cikin inda muke, and I heard one of them said “Mubarak let’s hurry up and do this. I am kind of tired” clearly in Sadauki’s voice. Na zare hannuna daga cikin na Saghir na mike tsaye da sauri “Sadauki!” Na fada under my breath. Sai kuma lokaci daya fitulun gurin suka kama gaba-daya yan gurin kuma suka hada baki wajan ambaton “surprise!!” Then I saw Sadauki a tsaye a gaba na, idanunsa cikin nawa.

Komai ya tsaya min. Numfashi na ya dauke, na saki jakar dana ke rike da ita a hannuna and ikon Allah ne kadai yasa nima ban bi jakar na fadi ba. Sadaukin ne dai a tsaye yana kallona, my Sadauki. But he has changed alot, he has grown more bigger and more muscular, his dark skin shining as brightly as his bright eyes. He looked more matured, more handsome, more confident and he looked rich. Very rich. 

In a flash of second aka zagaye shi, kowa yana kokarin yi masa magana hakan yayi blocking view tsakanin mu, “what is Sadauki doing here?” Shine tambayar dana fara yiwa kaina a lokacin da numfashi na ya dawo jikina. Maganar Saghir da naji a kusa dani ita ta dawo dani hayyacina har na tuna me ya kawo mu gurin, but banji mai yaxe ba saboda voice dinsa sound so faraway kamar daga miles yake yi min maganar, the only sound da yayi filling kunnena shine na Sadauki yana gaisawa da mutane. Na girgiza kaina, trying to clear my head nace “me kace?” Tsaki kawai yayi, ya kama hannuna muma muka shiga mutanen da suka zagaye Sadauki suna gaishe shi tare dayi masa congratulations na kammala karatu. “karatu?” Na tambayi kaina. Menene hadin Sadauki da gurin nan wai? Mu ba zuwa mukayi mu taya ogan su Saghir murnar dawowa daga karatun sa ba? Ya naga kuma anayi wa Sadauki murna?

Ban samu amsar tambaya ta ba na ganmu tsaye a gaban Sadauki ni da Saghir, Saghir ya mika masa hannu yace “congratulations Mr Abatcha, and welcome back to Kano” sukayi shaking hands, nabi hannayen nasu da kallo sannan na sauke ido na akan Sadauki, trying to digest what I was beginning to understand. 

Mintsini Saghir ya sakar min a hannu sannan cikin whisper yace min “for God’s sake stop staring at him and greet him” sai kawai nabi Saghir din da kallo ba tare da nace komai ba, kamar daga sama naji muryar Sadauki yace “Hello Madam” na juya ina kallonsa, sai naga kamar ya saka wani mask ne yayi hiding Sadauki na, kamar this man is not the Sadauki I knew, this man is Mr Abatcha.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button