NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 6

???? *WA ZAI FURTA?*????
              0⃣6⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Masoyana ku sani cewa Ina alfahari da ku 100% a ko’ina kuke. Na gode da kauna*????????

       ****************
*Federal University dutsinma*
Duk dube dubenta bata hango ta inda zai bullo ba, juyawa tayi don tafiyar ta….. Saura kadan suyi karo.
Ta razana ainun, hazbunallah! Ta fada da sauri tare da yin baya kadan ……..harara ta banka mishi kafin tace. Wallahi ka tsoratani.
Ya danyi murmushi matsoraciya kawai meye zai kamaki Yanzu da rana gatsal cikin wannan bainar jama’ar?
Mtseww…… Ta gittashi zata wuce.
Ina zakije Kuma Ina ce nemana kikeyi.
Barshi kawai , ta fada tana Kara yin gaba.
Ikon Allah, ya fada tare da rufa mata baya….. Wai ke me yasa kin cika nemana da rigima?
Ta Dan harareshi, ni nake nemanka da rigima ko kuwa Kaine ke nemana da rigima?
Me nayi?
Saboda me yau kayi wa Suleiman wulakanci ni kuma ka kunyata ni?
Kunya ta ki Kuma?
Eh, ai kasan tare muke dashi sannan ka tabbatar idan na copy naka zai Sami damar yi shine ka rufe kayi biyu Kuma don mugunta baka tashi bani ba sai da aka ce submit.
Shine laifin da nayi?
Ban sani ba.
Allah ya Baki hakuri what next?
Kaje kaba Suleiman din hakuri……you are not well wallahi nine Zan ba Shi hakuri? Da na mishi me?
Shi ko kunya baya ji zai zauna mace na goya Shi Kuma……ai baya ganewa. 
Please Bilkisu come to your senses Mana. Me yasa kike kawo fada marar amfani tsakanin mu.
Ya ja ya tsaya Bari kiji na fada Miki, tunda Kika ajiye girman Kai Kika nuna kina son ki karu dani toba abinda bazan miki ba don naga kinyi passing no matter how, Amma duk masu zagi na suna mun shaidar banza a class kallonsa kawai nakeyi.
A gabanki ake cewa Ina da girman Kai, bani da kirki….this and that..Amma Ina so in tambayeki lokacin da Kika nuna Zan koya Miki karatu Kinga negative response a wurina?
Akwai Wanda Kika taba Jin yazo wurina da sunan Zan koya mishi karatu na koreshi ko Kuma nace  bazanyi ba?
Ko kuwa saboda kawai Ina son a yaba mun sai nayi ta yake baki Ina shelar ku taho kutaho Zan muku karatu imagine for God sake.
Eh na fahimceka amma ai baka sakin fuskar ma da za a tambayeka…..ke me yasa Kika tambayeni?
Tayi murmushi ai ni kace.
Ke Bilkisu ko?
Ashe ka gane ….ta fada tana Yar dariya.
Mtseww……ya kamata ki daina mun wannan rigimar gaskiya bana so…….. Sai kayi kokari ka canza Hali?
Nayi meye?
Na farko, Idan ka shigo class ka danyi wa mutane magana, na biyu, ka ringa yarda ana hada ido da Kai sai kayi Dan murmushi…….wata muguwar dariya ya saki har Yana buga kafa kasa.
Yarinyar nan wallahi kin rainani da yawa. Watan kaman wani karamin yaro ko?
Suka ci gaba da tafiya. 
Nidai na fada maka.
To naji, sai Kuma me?
…………. Shegen gora, wallahi daman sai da Anas yace tare da Bilkisu kake wannan ihun.
Dukkan su suka juya, sadeeq ne da Anas.
Yawwa sadeeq Allah ya kawoka zo ka taya ni yi mishi fada…….duk suka zaro ido fada Kuma? Ai wannan mugun dan daba ne wallahi yafi karfin mu.
Au baku fada mishi gaskiya kenan?
Kedai jaraba….suka ce tare da wucewa suna Yar dariya.
Shi kuwa sai hararar su yakeyi.
Ta rike baki….ohh, watan Kai kowa tsoron ka yakeyi……Banda ke,
Hmmm,ai wallahi koni ma ta Kara sauri sai anjima kaga tafiyata.
Shima ya Kara sauri Ina zakije Ina Jin yunwa muje ki siya mun abinci tunda kin Fara dandana mun…..eh lallai yi kokari ka cinye Yan pocket money din ta fada tana hararar sa.
Ba Shi kenan ba mun koma 1/1 kenan….. Amma muje Zan jira ki dafo mun indomie….ta zaro ido, Kai rufan asiri koma kada ma ka janyo mun surutai ace …….kin Fara yawo da Dan iska?
Ko kin Fara zuwa da Dan iska kofar gida……na tuba, ba haka nake nufi ba, inba haka kike nufi ba sai ki zabi daya, ko ki dafon indomie ko muje ki siya mun suya ko kaza ko chips……ta kyalkyace da dariya watan sai ma ka zaba, 
Ka jira anan naje na fito da kudin nan Babu a jaka, muje na ranta miki gobe ki fito mun da kudi.
Ikon Allah kamar cin rabo?
Eh, ai nasan karamin aikin ki ne idan kin shiga inji shiru kinki fitowa.
Mtseww……au abinda kasa ma ranka kenan…..ke mufa juya wallahi bazaki shiga gida ba.
Haka ta juya badon ranta yaso ba suka je shagon Alhaji Hari, ta kalleshi zabi abinda kakeso toh.
Ya koma gefe zabo mun dai ni wace gareni tunda kawoni akayi?
Kamar ta nutse kasa don kunya shagon cike mutane an musu ratai da ido. Kowa yasan Anwar Kuma Mai shagon yasan wanene Shi mamaki kawai yakeyi yau shine tare da mace?
Ta Sha mur Alhaji bani meat pie hudu, Pepsi biyu, shortbread biscuit din can manya biyu…..gaban Anwar ya Fadi Jin kayan tsadar da take lafto mishi Amma da ya tuna Shi zai biya kudin sai ya kyaleta.
Leda bammm aka cika. Ya mata totalling dubu hudu da dari shidda……. Ta bude jaka ta fiddo ATM Daman Yana da *POS* tace fidda kudin pls.
Ba karamin faduwa gaban Anwar yayi ba.
Ya rasa yanda zaiyi duk yaji wani iri.
Ta fito niki niki da leda  oya muje ta fada tana hararar sa. 
Ya sunne Yana Yar dariya.
Dan mashin ta tsaida mishi sannan ta kalleshi Yanzu ka shafan lafiya ka tafi ko?
Ya kyalkyace da dariya korata kikeyi?
Eh, ka isheni…go!
Wannan karon dariya sosai yayi, shikenan ba damuwa.
Zaki Kuma nemane ai.
Ta Mika mishi ledar bayan ya zauna kaci yau kaci gobe acici.
Wannan lokacin tare sukayi dariya.
Ta wuce tabarsu anan.
Tana niyyar tsallakawa titi ne suka suka zo zasu wuce yace: *A ringa duba titi*
Ta mishi murmushi kawai tare da daga hannu.
Haka kawai ta tsinci kanta cikin wani irin matsanan cin farin ciki,
Shi kuwa Anwar gaba daya ya kasa fassara yanayin da yake ciki haka  kawai fuskar sa ta kasa daina guntuwar dariyar da yakeyi lokacin da suka daga ma juna hannu.
Anas ya rabka salati……Wai da gaske Bilkisu ta maka shopping yau ma? 
Murmushi kawai yayi,
Sadeeq ya Kai mishi duka, munafuki kwa gama sumke sunken ku bayyana kanku, Daman na lura ka Fara tsanar Suleiman simply don Yana tare da ita, Kiri kiri dazun ka hanashi amsa wallahi baka kyauta ba Anwar……..suka dunga mishi surutai ya musu banza miskilin bai dai ce kunyi gaskiya ba bai Kuma karyata su ba.
    Duk abinda Bilkisu Bata so Yanzu kafa biyu Anwar gudun sa yakeyi.
 Ba Wai ajin nasu kadai ba har takai aji daya ma nemansa sukeyi don ya koya musu.
  Maimakon hakan yayi wa Bilkisun dadi sai ya kasance kullum cikin fada da rigima sukeyi musamman idan ta ganshi tsundum cikin mata sun saka Shi tsakiya kamar tayi hauka sai su kwana biyu uku Bata mishi magana ba Shi Kuma ya rasa dalili.
  Idan kuwa ya kuskure ya dauki hoto da wasu to sai sun kusa sati bai sanyata ido ba, ko lecture sai dai tasa a mata attendance.
Ya rasa inda zai saka kansa.
 Taki yarda suyi magana daya nemeta sai ta zille, 
Yan mata sunyo mishi chaaaaaa har Yan wasu department ashe daman ko wace ta ciki na ciki rashin bada fuska ne.
Hakan ya Kara harzuka Bilkisu Jin kowa Anwar …. Anwar.
Gashi ta riga ta Saba da bayanin sa, duk Wanda zai mata sai dai ya Gama babatunsa Amma Sam Bata fahimta.
Shi kansa yana bala’in son koya mata.
Ranar Alhamis ana fitowa lecture tana kokarin fita ya tare kofa ya maida ya kulle…….gaba daya ajin akayo masu chaaaaaa da ido.
Kamar ta bude kasa ta shige don kunya…..ke me na Miki kike fushi Dani?, Na gaji da fadan hakanan wallahi mu shirya…….Dan Allah bani wuri in wuce ji yanda kasa ake kallona.
Duk wannan mazuran naki yau bazasuyi tasiri ba sai kin fada mun Yanzu Kuma laifin me nayi naga abun naki Dada hauhawa yakeyi.
Ta kalleshi sama da kasa , sai naji zafin makara tukun ta ja kofar da karfi ta fice ya bita a fusace saboda yaji haushin abinda tayi…
Wai Bilkisu me na Miki haka? Ko kin gaji dani ne kina son in Baki wuri in kyaleki?
Yau kusan kwana uku Ina kokarin kizo muyi karatu kina zillewa…….ta dallo mishi manyan idanun ta, yaushe kake da wannan lokacin?
Ai Yanzu mutane sun Fara maka yawa batani kake ba……Nan da Nan ya sauko zuciyarsa tayi sanyi kalau sauran kadan dariya ma ta kubce mishi Wai yarinyar nan badai kishi ke damunta ba?
Ya tari gabanta…..jira muyi magana daina tafiya. 
Wallahi tallahi Ina da lokacin ki, basune suke zuwa na koya musu ba?
Ke kuwa nemanki nakeyi ko ranar Monday nace ki jira Ina son ganin ki kawai Kika gudu Kuma kece kemun fadan Ina sharesu da farko Yanzu kulawar ce zata haddasa Mana matsala?
Gabanta ya Fadi kada fa ya mata fassara.
Ta Fara in..in..in.
Bude Baki kiyi magana. Idan har Baki son in koya ma kowa wallahi daga yau na daina.
Ni Yanzu Kika ce Babu ruwan ki Dani Bilkisu ai na shiga uku waye zai ringa siya mun kayan dadi?
Bata San lokacin da ta yi dariya ba.
Shima dariyar yayi…kiyi hakuri na tuba bazan Kara ba. Daga Yanzu matukar kina son time dina ko wane lokaci ne Zan baki Ina ce Daman shine damuwar ko?
Ta Dan zumburo Baki eh.
Yayi murmushi, Zan kiyaye. Yanzu Ina zakije?
Daki.
Karatun fa?
Tayi shiru,
Kinji?
Ko har Yanzu Baki huce ba?…..
Kai Dan Allah. Ta fada tana Yar dariya.
To muje muyi ko sai anjima?
Eh,
Da karfe nawa?
Hudu.
Yanzu meye zakiyi idan kinje dakin?
Girki.
To zanci. Kizo mun dashi 4 din.
Okay.
In rakaki ko in kyaleki?
Kyaleni kada ka janyo mun duka gun Yan……maganar ta makale.
Ya zaro ido gun wa? Karasa Mana.
Tayi Yar dariya kawai, ya kuwa bita da kallo har tayi nisa…….. Kyaleta hakanan tunda tayi nisa maye. Sadeeq ya gani gabansa.
Ya dunkule hannu zai Kai mishi duka ya goje.
Zanci ubanka ne, na gaji da wannan sa idon naka Kuma da alama kaman Bilkisu kawai kake man wannan shisshigin.
Kai mugu ai na lura kwana biyu baka da sukuni saboda ta Fara daina kulaka.
Mtsew you are not well, ya fada tare da barinshi wurin tsaye .
           **************
*KADUNA RIGASA*
  Ya Fara dukan kofar kamar mahaukaci, Amira Ni Zaki rufewa kofa?
Naje na rufe, Daman baka shirya ma irin wannan ranar ba da mace zata hanaka barci ka karo auren?
Idan laifi kayi mata sai ka koma ka Bata hakuri ku sasanta da matar ka…idan kuma ita ce ke da laifi sai ka koyi yanda ake hukunta mace dai dai laifinta ba ka kaurace mata ba.
Kaine ka kawo dokar Banda raba kwana  Koda za’ayi soke soken wuka…au fadan na maganganu ka kasa dauka har Kaine yau zaka karya dokar ka da kanka?…….Amira ki dubi girman Allah ki buden kofa zuciyata na iya bugawa……
Wallahi bazan bude ba saboda hakan haramun ne a wurin ka dani.
Ka koma can dakin matar ka…..watan idan ana dadi zanji shiru sai ta baci …….kada kishi ya janyo kiyi mun butulci.
Butulci ai Kai ne kayi mun tunda har ka iya hango wata bayan ni…….kasa daurewa yayi yabar gidan a fusace………Ya duba agogo  karfe Sha daya saura, ya kuwa Danna Kira……
Bugu biyu ya dauka.
Hello Abokina ya?
Kazo gidana Yanzu Ina nemanka, Ummi na bani matsala mukhtar.
Gabansa ya Fadi yasan a rina, ko a gida Ummi bata da kunya ta Raina kowa.
Cikin mintuna Sha shidda ya karaso.
A waje ya tareshi saboda tun fitar sa zuwa gidan Amira itama ta garkame side din nasa.
Tare da mukhtar din sukayi ta dukan kofa Amma taking budewa su duka suka hasala.
Cikin fushi ya kalleshi Abokina gobe kawai ka maido Yar iska gida idan ta dandana zaman gidan a matsayin zawarci ……bani sakinta wallahi. Ya katseshi.
To ka mayar da ita duk da haka ka Bata hutu kamar na wata guda taji taji. Kuma kada kaje ka Bari Ni Zan ma su hajiya bayani babu ruwanka.
Yayi shiruuuuuuuuu……ya ka sa magana Yana dai nazari.


Ayi ta hakuri kaman yarda na ce Ina da hidindimu Shi yasa

*Zainab wowo ce*…✍????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button