NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 5

???? *WA ZAI FURTA?*????
              0⃣5⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

*Kinfi Alawiyya farin jini unex ta hannun damata ( Hussaina Nasir )* Allah yaba kauna. *Alawiyya*????????????
  *********************
*Federal University dutsinma*
Tana isowa ya tashi yabar gurin.
Haushi ya kamata ganin zai dizga ta bayan Kuma yasan cewa wurin Shi tazo.
Sai Shan kamshi yakeyi yau ta rasa dalili.
Ta kalli sadeeq yau me akayi wa abokin ka ko Yan wulakancin ne bisa Kai.?
Yayi murmushi to wa ya sani.?
Sadeeq Yana da kokari Shima sosai musamman bangaren calculation ya iya Math sosai da sosai.
Tayi murmushi kyaleshi don nace zamu zauna test tare ne yake faman hade rai.
Murmushi kawai sadeeq yayi.
Suleiman na zaune gefen ta, tace sadeeq kara nuna mun nan please ta bude littafi ( Bilkisu kenan ba girman Kai indai maganar karatu ne ), ya danyi Yar dariya bari in Kira Miki mutumen ki kada…….bana so kyaleshi kawai nunan.
Tare da Suleiman ya nuna musu sai ma ta ga cewa yafi Anwar iya koya lissafi Shi Kuma yafi iya theory ( labaran banza ).
Yana shigowa ajin ya gansu tare da sadeeq ya Kara hade rai, wani haushi ya turnukeshi ji yakeyi kamar ya rufesu da duka su biyun. 
Zai gitta sadeeq ya rikoshi malam zo ka koya mata…..kyaleshi banso ta fada a hasale.
Baka ga sai wani Shan mur yakeyi ba simply don nace Zan zauna test kusa dashi? Mtsew ta balla mishi harara.
Duk kunya ta kamashi,  saboda Shima fa bai San dalilin fushin nasa ba, 
Gaban sa ya fadi kaddai fa kishin yarinyar nan yakeyi. Yayi saurin kawar da tunanin yadanyi tsaki a hankali…..
Ke bana son Sheri, yaushe ma na ganki da har Zaki mun wannan shaidar.
Eh Mana, Ina ma ka ganni ai baka so ko ido mu hada kana ta wani muzurai……mtseew ya finciko sadeeq tashi munafuki. Ya zauna kusa da ita kamar ya ingije Suleiman yakeji , kawai baya son raini ya shiga tsakanin su.
 Zaka karya nine?
Ya mishi banza…, Ita ma bai Kara mata magana ba.
Suleiman dai na gefe ta juya tana mishi magana……idan na wanko ga Anwar ka wanka kada kayi kasa da guiywa….ya kyalkyace da dariya ita ma dariyar tayi.
Ya Kara hade Rai….yarinyar nan ma ta daukeni Dan iska Amma ba laifin ta bane Suleiman zanci ma uwa……akan me? Wata zuciyar ta bukata. Yayi saurin kawar da zancen ya maida Air piece dinsa a kunne. Ya ajiye littafin sa ya fita waje.
Kowa nata karatu Amma Shi ba yanda zaka ganshi da littafi.
Handsome and intelligence guy amma girman Kai da wulakanci sun bata Shi. Vivion dake zaune gaba na ta fada tare da kallon uchechi.
Ai ya Raina kowa don Yana da kokari.
Ga kyau Kuma ko?
Eh, Amma baya birgeni saboda gadarar sa, jiya munyi ta kiransa yaki daukar waya nida su faith.
Hmmm mu samun sa mukayi dazun after lecture muna son ya koya Mana Amma kowa ya kasa Masa magana…….. Maganar ta makale ganin Yana dawowa.
Ashe malamin nee gani ya taho.
Ko Zama baiyi ba ta nuna su uchechi gasu Nan suna son ka koya musu amma sun kasa tambayar ka……sai ke Mai Baki Zaki tambayeni?
Idan abun ya damesu ki bari su fada Mana.
Zata Kuma magana ya nuna mata hannu alamar ta duba ga malamin nan ya shigo.
Sadeeq na bayansa.
Ta fiddo paper zata rubuta suna yayi saurin daukewa ya rattaba nasa sunan ya wani hade Rai.
Ta kura mishi ido Baki bude…..gashi Bata da wata.
Ko wa ya dauke jakar sa….malamin ya fada.
Ya dauko jakar ta ya saka littafinsa Suleiman ya Miko nasa a saka mishi da wayar sa kawai ya Mike ya saka tashi wayar yakai jakar can gaban malamin.
Ita Bata San me yayi ba, Amma Shi Suleiman din yaji haushi sai dai Yana uchechi ta saka mishi a tata jakar.
Sadeeq kuwa dukewa yayi Yana sumke dariya.
Bilkisu tayi zugum tana zare ido Anwar ya kwace takarda.
Tana tsoron tayi magana ya canza mata wurin Zama.
Ko ajikin Anwar tuni ya Fara rattaba number sa bayan ya rubuta suna da course code.
Suleiman ya Ankara Ashe biyu gareshi. Ya Miko mata.
Wani sanyi taji ta balla ma Anwar harara sosai sannan ta Fara rubuta suna.
Gaba daya ajin yayi tsit!
Tana rubuta suna taga Anwar ya fiddo wata takardar ashe daman Yana da ita.
Haushi ya Kara kamata shin me take nufi da akoreta sit din ko meye? Nan da nan ta Kara kulewa.
Har malamin ya gama raba question paper Bata gama duminiyar Jan layi da rubuta suna ba.
Lokacin da ya bada umarnin a Fara kowa ya bude takardar Amma sai wutar kowa ta dauke saboda yanda ya mako muguwar tambaya Mai sarkakkiya.
Sadeeq taji na magana a hankali, Anwar wannan 35 din zamuyi amfani da ita kuwa?
Ya kada Kai alamar a’a.
Yawwa na gode.
Bilkisu tayi zugum, Suleiman ya zungurota alamar ta iya?
Ta girgiza Kai ya ce to kawai tayi ta kwafo musu na Anwar.
Ganin ya Fara rubutun tayi saurin maida hankali don samun abinda zata tsira.
Kamar injin haka yake rubutun zu..zu..zuu kafin tayi layi hudu har ya juya , haushi ya turnuketa bai jira ta gama? Wannan wace irin mugunta ce?
Nan da Nan ta zuciya kawai sai ta ci gaba da rubuta shirme.
Gara naci zero da in yi naka ….ta fada cikin zuciya.
Kafin kace kwabo har ya gama ya janyo wata sabuwar takardar, ya canza biro black ya ci gaba da rubutu, sakamakon ta farkon da ya Fara da blue biro.
Tana kallon sa ta wutsiyar ido ko ya Turo mata wacce ya Gama da ita ta rubuta sai ma ya sanyata kasan tashi , idanun ta har ruwa ruwa sukeyi saboda fushi .
Wallahi Ni da Anwar har abada au Ni zai ma rashin mutunci?
Duk inda ka waiga kowa sai mazurai yakeyi an kasa rubuta abin kirki.
Tana kallon sa ya gama kawai yasa hannu biyu a kirji.
Kamar tayi ta tsunkulinsa takeji don takaici.
*stop writing*, ya Fara karbar wadanda ke gaba layi layi……..ai kamar jira akeyi ajin yau dauki gungunai.
Jin haka kawai taga ya dauro mata takarda bisa tata.
Sunanta, number, course code…..da komai da komai.
Ta zaro ido Wai Daman biyu yayi tawa da tasa?
Tayi saurin kallon sa, ki soke wannan shirmen da kikayi kisa mistake. Ta kalli takardar ita ce ya Fara solving da blue biro.
Suleiman ya Fara kunno Kai zai Fara kwafa , malamin har ya zo wurin su, duk suka Mika.
Shiru Suleiman din yayi yama rasa meye zaiyi don takaici, Tabbas yasan don Shi Anwar yayi haka.
Ta kalli Suleiman din cike da damuwa ka gama kuwa?
Wallahi banyi komai ba ya fada Yana kakaro murmushi, 
Innalillahi….. Ta juya zata ma Anwar magana Ashe har ya bar class din.
Ta waiga ta Kara waigawa Amma Ina tuni yabar shiyyar class din ma.
Kayi hakuri , ta juya tana ma Suleiman magana.
Nima wallahi har na sadakas, ashe rubuta mun yayi. Kai Anwar karshe ne wallahi.
Murmushi kawai yayi.
Ai kaga da ya barni na kwafa har kaima kayi…..kayi hakuri Suleiman.
Haba ba komai wallahi. Ya fada Yana Yar dariya.
Haka suka fito duk jikinta wani iri.
Kai Anwar case ne. Watan Shi dole inba wulakanci yayi ba baya taba Jin dadi.
A bakin kofa sadeeq ya karaso Bilkisu ya test din….yawwa sadeeq zo kaji Dan Allah. Ta yi gaba Yana binta.
Sun danyi nisa kadan inda ba mutane sosai ta tsaya.
Ka ringa yi ma Anwar fada Dan Allah Shi me ya dauki rayuwa?
Me yayi ba dai tashi yayi ba ya bada ba tare da ya baku ba?
Hmmm , kusan haka.
Kaga yasan tare nake da Suleiman na Kuma fada mishi Amma sai ya hana in copying Yana ta sauri sauri Ashe so yakeyi yaci lokaci yayi nawa yayi nashi Kuma don mugunta bai bani ba har sai da za’ayi submitting saboda Allah ya kyauta?
Tun tsirewa yayi da dariya, Dan iska, abinda yayi kenan?
Wallahi kuwa, kaga ai Babu dadi.
Gaskiya ba dadi.
Kiyi hakuri Dan Allah Yana Ina yanzu?
Kasan halinsa ai, har ya gudu ya tafi.
Kiyi hakuri Zan mishi magana.
Ka kyaleshi Daman idan ka lura bai niyyar Zama Dani ba yau tun safe yake ta wani Shan kunu….. Baki tunanin ko kin Masa laifi? …Laifin meye?
Jiya ne mukayi Zan kirashi a waya na manta inaga kilan shine ……shine ma kawai.
Mtseww…..to kyaleshi .
Anwar na Bilkisu…. Bilkisu ta Anwar ai in ba keba Shi.
Kai ai kyaleshi zanyi don ban iya hakurin wannan mugun halin nasa.
Dariya sadeeq keyi sosai.
Ta wuce fuuuu.
Waya ta dauka, ta kirashi.
Yana tsaye zai siyi *Pepsi* yaga Kira.
True caller ta bayyana sunanta a screen din wayar sa *Balky gada*
Kawai sai yaji gabansa ya Fadi ras!
Ya danyi murmushi……. Hello
Kana Ina?, Ta fada?
Cikin dakewa kamar bai San wake magana ba yace Ina Ina?
Eh kana Ina?
Wake magana ne?
Bilkisu…..kana Ina Wai?
Wace Bilkisu ? Ya Kara bukata…. Dariya ta kusa kubuce mishi Jin har ta Fara hasala.
Bilkisu Gada ……. Oh ya fada tare da yin shiru.
Au shine kayi shiru mtseww…..ta katse waya.
Yabi fuskar wayar da kallo Yana kyalkyatar dariya ohh ni Hamza tawa ta sameni.
Wai yarinyar nan idan Sona takeyi haka zata shigar da kanta da tsiya ba da ARZIKI ba?
Ni wallahi na Fara tsarguwa da tambayoyin da nake faman amasawa kullum akanta .
Ya kirawo ta……kamar bazata dauka ba har ta fito cikin makarantar sun rabu da Suleiman tun a bakin gate.
Ai naji kana ta wani rainan wayo saboda nice na kiraka ba credit Dinka ba. …….Allah ya bada hakuri. Kina Ina ne?
Ni na Fara maka wannan tambayar baka bani amsa ba don haka……..ohhhhh na ma hangoki. Kawai ya kashe wayar.
Ta Fara waige waige….
**************
*KADUNA RIGASA*

Kutumar bala’i …..Kai Wai me aka daukeni gidan nan?
To bafa Zan Dauka ba.
Daman some somen hauka zubda miyau, Ni fa ko lallashin da akeyi ma Amarya ban samu ba, bani da wata kima sai ta bisa gado ya iya lallaba da lallashi bisa gado….yau za ayi ta takare.
Ta tashi Yana kwance rubda ciki, ta banka kofar da karfi har ya Dan razana….kace nan ba gidan mu bane daman na ce Nan din gidan mu ne?
Ya dago Kai da sauri ….kada ki kawo man hauka….an kawo ma hauka kayi maganina Mana mijin tace?
Nine mijin tace?
Kaine……kana da wani sunan da yafi wannan shanyayye?
To Bari kaji in fada maka idan an shanye ka ni ba’a shanye Ni ba, ba malam ba boka amma dole ka maidani gidan ubana bani wannan wahalallen auren naka marar fa’ida….. Ke ba a Isa a Gaya miki gaskiya ba ko? Duk lokacin da kikayi kuskure aka nemi a Miki gyara……haka ake gyara a wulakance da cin fuska?
Ai Daman kallon ka nakeyi tun kafin in zo gidannan kake nuna mun bani da wani matsayi sai matarka….. Shut up…..ya daka mata tsawa……bazanyi Shurin ba……ita ma ta daka mishi tsawa….ka sake Ni a yau Mana idan kana ganin Kai ke iko da kanka ba wat ke juya ka ba. Idan Kuma baka iyawa …..ta bude kofa kazo ka wuce ka tambayo ta idan ta amince yau ka bani takarda ta ita wacce ke auren naka.
Kai Bari kaji in fada ma Bashir…..wallahi wallahi baka cikin tsarin mazan da nake so in aura saboda Ni duk Mai mata baya gabana musamman Wanda bai da gabata irinka sai abinda aka gindaya mishi…..Ummi Ashe Baki da kunya?…. Yau ne kasan haka?
Kai baka iya maganin rashin kunya ba?
Ka je ka tambayo ta ya ake maganin marar kunya sai kazo kayi hakan Dani mijin tace….fuuuuu ya tashi yabar dakin ta bishi tana balbala bala’i ta inda take shiga Bata Nan take fita ba….idan hankalinsa tayi dubu yau a tashi yake, yayi hanyar dakin Amirar….ta daga murya….Arrrrrr Ni nasan baka da idea din kanka sai wacce aka saka maka…….nesa nesa yake Jin maganar.
Da karfi yake buga mata kofa…..a rude tazo cikin tsoro take magana…wanene?
….ke bude nine….da sauri ta bude….lafiya baban Ahmed?
Waccen yarinyar Bata da tarbiyya Amira wallahi wallahi ban tunanin Zan iya Zama da ita…..Nan da Nan tamu ta mata ta motsa ( kishi )….to Yanzu me kake nufi?
Zan kwanta anan ne saboda……..saboda ita tafi karfin ka?
To ba anan ba wallahi.
Ta barshi tsaye ta shige dakinta kawai tasa key……..
Ya zaro ido???????????????? 

Nima na zaro nawa????……..✍????

Ayi hakuri da kadan…….✍???? *ZAINAB WOWO*
*Maman Abdallah*????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button