NOVELSUncategorized

DIYAM 43

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Forty Three : Heartless
Raina ya kara baci, ina mamakin anya kuwa wannan Sadauki nane? Sadaukin da na sani will never do that amma kuma sai nayi wani tunani. Yes, Sadauki yana da kirki da kyawun hali sosai amma bashi da yafiya,
musamman idan akan abinda ya shafe ni ne Sadauki bai taba daga kafa ba ko da kuwa waye ya taba nin indai ba Inna ko Baffa ba, na tuno ranar daya doka wa yaya Mukhtar ball aka a gaban Inna. Sadauki bashi da tsoro ko kadan tun a lokacin da bashi da komai ma, ballantana kuma yanzu da yake da masu garin. 

Nace “abinda kake so kenan? Abinda kake after kenan? Revenge?” Ya girgiza kai “this is not revenge, this is justice” nace “wanne justice din ne kuma wanda yafi wanda Allah ya riga yayi? Shin in kayi haka Sadauki ka gode wa Allah kenan? Kaga kuwa halin da Alhaji Babba yake ciki a yanzu? Ka kuma duba kaga halin da kai kake ciki a yanzu, kai kanka ka fada, the table have turned, menene kuma saura? Shin in ka yafe wa Alhaji Babba mai zai ragu daga jikin ka? Sai ma daraja da hakan zai kara maka a gurin ubangiji. Yanzu in ya siyar da gidansa ina zai kai iyalinsa?” ya bar inda yake tsaye ya zagawa gurin kujerar sa ya zauna yace “sai su dawo gidan ku ku zauna tare, ai naga kuna da bene, sai su zauna a sama ku kuma a kasa” na saki baki ina kallonsa sai ya danna wani button a jikin table din sai naga kofar dana shigo ta bude, ya kalle ni yace “goodbye, Diyam” na tsaya kawai ina kallonsa ina girgiza kai, I can’t believe Sadauki yayi tauri har haka, sai na je na tsaya a gaban table dinsa nace “I don’t like this Mr Abatcha da nake gani a gabana, I want my Sadauki back, I want my brother back” sai na juya da sauri na bar office din.

Ina jin matar nan ta waje tana yi min magana amma ban ma fahimci abinda tace ba ni dai na gyada mata kai kawai na fita da sauri. Da saurin kuma na karasa wajen gate na tari abin hawa na shiga muka tafi. Sai da muka bar gurin sannan na saki kukan da nake rikewa, ma dauka hawaye ne kadai nake yi bansan ya fito fili ba sai da naji drivern yace “yammata kiyi hakuri, komai na duniya mai wucewa ne watarana sai kiga kamar ba’ayi ba” a goge hawaye na ina jinjina maganar sa, watarana zanga kamar ba’ayi ba? Yaushe?

Sai dana je gida sannan nayi realizing wani abu guda daya, ni da na tafi gurin Sadauki da niyyar samun answers amma ban samu ko daya ba sai karin tambayoyi da na debo wa kaina. Na sani Alhaji Babba ya zalunce ni kuma ya zalunci Sadauki kuma har cikin raina ban damu ba in wani abin ya same shi a saboda abinda yayi, abinda na damu dashi shine Sadauki, I don’t like this person he as turned to bana son wannan hanyar da yake tafiya a kai. Ni da zai aje duk wannan kudin nasa ya koma former Sadaukin da na sani da sai nafi jin dadi.

Na biya na dauko Subay’a sannan muka karasa gida. Muna zuwa na shiga daki na hada mana kayan mu ni da ita a akwati na chanza mata kaya muka fito. Mai gadi yace tafiya zakuyi ne haka Hajiya?” Nace “cikin gari zamu shiga baba iliya, sai Sunday zamu dawo” ya taro mana abin hawa ya saka mana kayan mu muka tafi Subay’a tana ta murna.

Muna shiga gida naga Inna duk tayi wani jeme jeme da ita, bayan mun gaishe ta ta kalli akwatin kayan mu tace “da fatan ba yaji kika yo ba Diyam” na girgiza kaina nace “yayi tafiya ne Inna, shine muka zo gida muyi dan kwana biyu” ta gyada kai tace “duk da haka ina fatan da amincewarsa kika taho gidan. Nasan ba kya son Saghir, kin fada kin kara fada cewa ba kya son sa kuma har yau nasan ba kya son nasa din. Amma kuma rashin son nasa da ba kya yi ba zai cire shi daga matsayin mijinki ba. Ni nasan kiyayya Diyam nasan illolinta, tun zamanin yammatanci na na dora wa zuciyata kiyayyar Zainab kawai saboda baffanku yana sonta ni kuma ina sonsa. Kiyayyar ta karu lokacin da aka aura masa ni ina matsayin matarsa amma kullum sai ya tuna min cewa dole aka aura masa ni, sai ya gaya min cewa ga wadda zuciyarsa take so. Na kara kin ta kuma lokacin daya aure ta ya kawo ta gidan nan duk kuwa da cewa tayi aure ta fito amma bai rage soyayyar ta ba daga zuciyarsa. Sai ma ya dauki wani son daban ya dora akan agolan da tazo dashi har a gurina nake ganin kamar yafi sonsa akan ku yayan da na haifa masa. Sai ni kuma na tsani yaron ba tare daya yi min komai ba. Har yau ni bazan iya fadar wani abu na rashin kyautawa ko rashin kunya da Sadauki ya taba yi min ba. Na tsane shine kawai saboda na tsani uwarsa. A gaban Sadauki zan gaggayawa Zainab magana amma baya kulani saboda ta hana shi tace babu ruwansa da tsakanin mu. Amma haka na cigaba da rura wutan kiyayyar sa a zuciya ta yadda har mutuwar ita kanta wadda ta haife shi da wanda ya kawo su gidan bata wanke kinsa a raina ba a karshe ina ji ina gani na saka rayuwar yata ta cikina a wahala kawai saboda in bakanta masa” sai ta rufe fuskarta ta kama kuka “Diyam ki gafarta min abinda nayi miki,ni na haife ki amma na tauye miki hakkin ki na bawa azzalumai damar zaluntarki” sai na tashi daga gabanta na koma kusa da ita na dora kaina a kafadarta na fara kuka. Ta saka hannu tana shafa kaina tace “nayi nadama, nadama mai tsanani. Maganar baffanku ta tabbata, yan uwanmu sun watsar damu a titi Sadauki yazo ya dauke mu. Ohh duniya. Duk wanda bai godewa rahamar Allah ba to kuwa tabbas zai godewa azabtar sa. Diyam nayi nadama a lokacin da nadama bata da amfani. Wallahi da ace igiyar auren ki a hannuna take Diyam da tun haihuwar ki ta farko zan gutsire auren gwara ki dawo gida ki zauna a gaba na akan auren Saghir. Amma na kai ki na baro ki. Babu abinda zanyi sai dai in nemi gafarar ki” na rungume ta nace “Inna kinfi karfin haka ai, ni dama ban rike ki a zuciyata ba ballantana ki nemi gafara ta. Wanda zaki nemi gafara shine Sadauki. Shi kika fi zalunta ba ni ba” tace ” to ni Diyam ina zanga Sadauki? Tunda ya kawo mu nan ya ajiye mu bai dawo ba. A lokacin na gaya masa ina son magana dashi sai yace min zai dawo amma tun lokacin nake zuba idon ganin sa sai dai shiru babu shi babu labarin sa”. 

Sai na bata labari. Na bata labarin asalin ko wanene Sadauki a yanzu sannan kuma na gaya mata yadda mukayi da Alhaji Babba da kuma irin amsar da Sadaukin ya bayar. Na karashe da “yanzu dai Sadauki yace Alhaji Babba yana da dama uku. Ko dai ya bamu gidan da yake ciki a maimakon kudin mu, ko yayi jail time, ko kuma yaje gaban Sadauki ya durkusa yana kuka ya roke shi gafara a bisa dukkan abinda yayi masa” Inna ta rike baki ta kasa magana. Nayi shiru ina kallon ta ina jiran ta inda zata fara jero tsinuwa ga Sadauki amma sai naji tace “to, kudin nan dai namu ne gabaki daya, ni dai abinda yake hakkina a cikin kudin nan na yafe wa Alhaji Babba tare da fatan Allah zai dubi niyya ta nima ya yafe min wasu daga cikin laifuffuka na. Amma a cikin ku ban tilastawa kowa ta yafe nata ba, duk wadda taga bata yafe ba sai ta bawa Sadauki goyon baya gurin karbo muku abin ku. Shima kuma Diyam kar ki kuma kokarin hanashi karbar hakkinsa, in ma zubarwa zaiyi ai nasa ne ko? Da basu san kina da amfani ba sai yanzu? Babu ruwan ki, ki fita daga harkar” na gyada kaina. Sai kuma ta tambaye mu in mun yafewa Alhaji Babba, nace “ni dama ai ni yace yayi wa kaya da kudin, to in ma ina da ciko na bar masa, wanda ya tara dukiyar ma ya tafi ya barta” Asma’u tace “ni kam in dai har hamma Sadauki zai iya karbar kudin nan to ina son kaso na. Shi da bai taimaka min da komai ba ni ba zan bar masa hakkina ba” na harare ta sai ta daga kafada tace “Inna tace kowa ya fadi ra’ayin sa”.

Da daddare tare muka kwana gabaki daya a kan gado daya muna ta hira, Asma’u sai labarin motar Sadauki take yi min “wallahi ban taba ganin mota mai kyau da dadin wannan motar ba. Kai Adda ina ma dai shi kika aura da yanzu a wannan motar za’a ke kaiki unguwa kin huta da dan sahu. Nima in naje gidanki a irinta za’ake kawo ni gida” nayi juyi nace “Asma’u dan Allah ki rabu dani, bashi na aura ba chapter closed” sai kuma nace “motoci fa yake siyarwa. Dole ya hau mota me kyau”.

Washegari na shirya, na bar Subay’a anan gidan na tafi gidan Alhaji Babba. Direct part dinsa na tafi tunda yanzu ba sai anyi wa mutum iso ba. Na same shi a zaune yana lazimi, sai da ya shafa sannan ya tambaye ni “Diyam kin same shi? Me yace? Jibi ne fa zamu fara zuwa court” nace “na same shi Alhaji” sai kuma na lissafa masa abinda yace. Ya kama salati, amma wannan yaro anyi asarar haihuwa, yanzu ni tsofai tsofai dani zaice in je in durkusa a gabansa? Sakayyar da zai yiwa rikon da Usman yayi masa kenan? Gwara da Allah yasa bamu bashi aurenki ba Diyam da yanzu da surikin mu zamu shiga Shari’a” ni dai nayi masa sallama na fita ina jinsa yana cigaba da maganganu shi kadai.

A cikin gidan ne zuciyata ta karye. Hajiya Babba ita kanta a jigace take dan yan uwanta sun gaji da taimaka mata. Muka gaisa tace “Diyam baku kyauta mana ba ke da Saghir, yanzu ace tafiya ta same shi amma sai bayan da yayi ta zamuji labari?” Nace “Hajiya ni wallahi bansan be fada muku ba, na dauka duk kun sani” ta girgiza kai tace “ina fa, mu Saghir sai yayi sati ban saka shi a ido na ba sai dai in na kira shi nace ina nemansa. Yanzu idan kunyi waya dan Allah kice masa ya kira ni” nace “to”.

Dana shiga dakin Hajiya Yalwati ne na tarar dasu abin tausayi. Aunty amarya dama ta kara mai ta bar yaranta guda uku duk suna gurin Hajiya Yalwati ga sauran yayan da ake bari a gidan duk mata, ga kuma nata yaran dam haka wajan yara goma ne a part dinta, dan abinda manyan ƴaƴanta suke taimakawa dashi da kyar yake ciyar dasu. Ga yara uku sun isa aure sun kuma samu mazaje amma babu halin yi musu auren. Muka gaisa itama tayi min mita “yanzu Diyam shi mijinki ko shinkafa ba zai ke siyowa yana kawowa gidan nan ba?” Ni dai bance komai ba saboda bazanyi alkawarin da nasan ba zan cika ba.

Washegari Saghir ya kira wayata. Dama tunda ya tafi kullum sai ya kira sai in bawa Subay’a su gama maganganun su in kashe. Ranar sai yace ta bani zaiyi magana dani. Ina karba ya fara fada “da izinin waye kika fita kika je gidan Alhaji?” Nace “Alhajin ai shi yayi kirana ya hada ni da Allah da Annabi inje in taimaka masa” yace “ke kuma sai kika fita, saboda kina sauri za’a tura ki gurin saurayin ki ko? Ai Alhajin duk ya gaya min abinda yake faruwa, shegen yaro da bai san darajar manya ba wai har zaice zai kar Alhaji kara ya biya shi gadon uwarsa? Yanzu haka kudin wiwin da yake sha ne ya kare shi e yake neman refill” nace “amma Alhaji bai gaya maka lauyoyi ya dauka har guda uku ba? In kudin wiwi yake nema ya siya mana da kudin daya biya lawyers din dashi? In fitsari abinyi ne kaza tayi mana mu gani” yace “kar ki gaya min magana, kinsan dai dan bana gari ne da tuni zan biya shi kudin sa, ko Mr Abatcha na gayawa a take zai bani kudin in bashi” na girgiza kaina ina jinjinawa rashin sani da hausawa suka ce yafi dare duhu. Sai nace “to ko a daga shari’ar ne sai ka dawo sai ka karba a gurin Mr Abatcha ka bawa Sadauki?” Yace “to kudin ma ba Alhaji yace dasu akayi miki kayan daki ba? Ki gayawa Sadaukin haka in yaso in karar ce sai ya kai ki ke ki biya shi” sai na gaya nasa jimlar kudin, nace “ni nafi tunanin bayan kayan daki na har gidan da muke zaune a ciki da kudin aka siya, sannan aka kara jari da sauran. Dan haka dani da kai za’a gamai biyan kudi”.

Da daddare lawyer din Sadauki ya kira ni, wai Sadauki yace kar muje court gobe. Inna tace ai dama babu inda zamuje. Washegari suka zauna a court. Sadauki ma baije ba kamar yadda nayi tsammani, lawyers dinsa ne kawai suka je a madadin sa. Suka gabatar da dukkan takardu da kuma dukkan shaidu da suka tabbatar da wanzuwar garejin da kuma filin, sannan suka kawo shaidun cewa an siyar, har wadanda aka siyarwa ne suka zo sukayi testifying da kansu suka kuma fadi kudin da suka siya. Alkali ya nemi Alhaji Babba daya fito da kudi shi kuma ya tabbatar cewa kudi dai babu su kuma bashi da hanyar samun su a yanzu, sai dai yana neman alfarmar a bashi lokaci yake biya a hankali har ya gama. A take lawyers din Sadauki suka gabatar wa court da shaidar cewa Alhaji Babba yana da gida mai number 43 a unguwar sharada, har da estimate na kudin gidan, dan haka suna so Alhaji Babba ya siyar da wannan gidan nasa ya biya wadannan kudade, a take alkali ya amince kuma ya bawa Alhaji Babba kayyadadden lokaci na siyar da gida shi kuma Alhaji Babba sai ya nuna cewa lokacin yayi kadan saboda sai ya samu mai siya, anyi ciniki anyi komai. A take lawyers suka ce Sadauki yace zai siya, ai kuwa alkali ya bada lokaci yace aje a daidaita a kan price.

Ana fitowa daga court kawu isa ya kira Inna ga Alhaji Babba nan hawan jini ya tashi an kaishi asibiti. Haka Inna ta saka mu a gaba muka tafi dubiya ni dai ba’a son raina ba amma dana ganshi sai naji zuciyata ta tsinke. Yana ta kuka shabe shabe da hawaye. “Yanzu ya zanyi in siyar masa da gidana? Gidan dana gina tun auren fari da gumina. In na siyar da gidana a ina zan saka iyalina kuma?” Sai naji tausayinsa,ko babu komai yayan Baffa ne shi uwa daya uba daya. Sannan ga tausayin iyalinsa ina zasu je? They are innocent. Su zan iya rantsewa basu mori ko kwandala a kudin ba.

Na fita na dauki waya ta nayi ta kiran number din Sadauki bata shiga. Ko kuma blocking dina yayi ne oho. Da daddare kawu Isa yazo gurin Inna, wannan shine zuwansa gidan mu na farko tun da su Inna suka dawo. Yace “kudi dai da za’a bawa yaron nan babu su. Dan ni kaina in nace zan fitar da kudin nan to kuwa tabbas zan kassara kasuwanci na. Gida kuma kamar yadda Alhaji ya fada in ya siyar ya kai iyalinsa ina? Dan haka third option shine a kira yaron nan a bashi hakuri, ku zakuyi mana jagora zuwa gurinsa a sasanta maganar nan as a family tunda shima ai kusan family din ne, shekarar sa ashirin a hannun dan uwan mu”.

Ni aka saka in kira Sadauki. Na gaya musu ba dauka zaiyi ba amma suka ki dan haka a gabansu na kira kuma taki shiga din. Sai na tura masa text. “Third option. Kazo a baka hakurin da kake so” na tura masa. An jima kadan yayo reply “tomorrow evening. Gidan Baffa” na gayawa kawu Isa abinda yace sannan ya tafi da niyyar gobe zai zo tare da Alhaji Babba.

Washegari. Inna har dayiwa Sadauki girki tana ta gyaran gida ni dai ina kallonta kawai. Su Alhaji Babba ne suka fara zuwa, sai a lokacin ma yasan akwai yan haya a gidan mu. Suka zauna nan palo aka bawa Alhaji pillow ya dan kashingida saboda babu lfy. Sai after 5 Sadauki ya shigo gidan. Shi kadai, babu wani abu a jikinsa da zai nuna cewa shi mai kudi ne dan shirt da wando ne kawai a jikinsa ko agogo babu a hannunsa. Sai naga ya koma min wancan Sadaukin da na sani ba wai Mr Abatcha ba, kuma ganinsa a cikin gidan mu sai yayi adding to that feeling. 

Yana shigowa palon muka hada ido sai ya dauke kai, fuskarsa babu walwala ko ta cikin cokali sai kawai naji gabana ya fadi. Ya gaishe da Inna ta amsa, the first time da naji Inna ta amsa gaisuwar Sadauki. Sai ya samu guri ya zauna yana kallon Alhaji Babba yace “ina jin ka,” kawu Isa yace “dama cewa mukayi a kira ka muyi magana. Ayi hakuri a bar maganar nan ta wuce” sai yace “ba kai zaka bada hakurin ba ai” Alhaji Babba ya tashi daga kwanciyar da yayi ya matso gaban Sadauki yace “ka duba darajar rikon da Usman yayi maka, da kuma darajar yanuwantakar da take tsakanin mu ka bar maganar nan. In na baka gidana iyalina kuma ina zan kaisu? Ka duba halin da nake ciki na karayar arziki data same ni ka yafe min kudin nan. Banyi dai dai ba na sani, na aikata maka laifuffuka na sani, amma na hada ka da Allah kayi hakuri ka bar maganar nan” sai naji zuciyata ta karye, hawaye ya fara bin fuskata amma dana kalli Sadauki sai naga kamar da dutse ake magana. Sai ya mike tsaye yana kallon Alhaji Babba yace “na yafe maka kudin gadon Ummah. Amma kudin fili na ban yafe ba dan haka zan aiko a yankar min wani part na gidan ka a maimakon fili na, dama ina da sha’awar yin kiwon kaji sai inyi a gurin”.

Na mike da sauri ina kallonsa cikin mamaki. Can his heart really be this dry? Bai jira sauran magana ba yayi hanyar waje na bishi da sauri ma sha gabansa nace “this is not you Sadauki. Ba kai bane wannan. Kai kace minzaka yafe masa in ya durkusa a gabanka ya roke ka and he did just that” ya harde hannayensa a kirjinsa yana kallona yace “ni ba haka na ce miki ba. Cewa nayi in ya durkusa ya roke ni gafara in naki yi masa a lokacin ne zai fahimci irin yadda naji. So, nayi kokari ma ai, na yafe masa rabi saura rabi”.

Na dafe kirjina nace “are you this heartless Sadauki?” Yana kallona with straight face yace “do you blame me? Yes, I am heartless because they took away my heart. You are my heart remember?” Sai ya juya ya fice ya barni a tsaye.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button