NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 10

???? *WA ZAI FURTA?*????
             1⃣0⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

************
*KADUNA RIGASA*

Tun daga bakin gate yake jiyo kamshi, mamaki ya cika Shi, shin ko yayi batan lissafi ne gidan Amira yake ba Ummi ba?
Tana tsaye cikin Riga da skirt na leshi tasha ado ya shigo.
Da gudu ta rungumeshi yaji wani tsammmmmmm…… Anya Ummi ce?
   Nan danan ta Fara sabon salo. Shigowa yayi kawai ya ajiye jaka ya wuce wurin Amira sannan ya dawo Amma inaaaa tuni hankalin ya karkata……..  Bayan yayi wanka, ta zauna tana bashi abinci kamar yaron goye tun a daki da ya motsa sai ta bashi hakuri yanzun ma tana bashi abincin tana Kara lallashi duk ya sukukunce ya rikice.
    Ya kalleta wallahi Ummi Ina sonki, kawai halayenki ne suka Sanya mun ko kwanto a zuciya Shi…….ta rufe bakin da chokaci ta debo peppé soup, sorry my love zaka ga changi I promise…… Ai na ga changi wallahi please keep it up…….
Amira Bata Sanya Shi ido ba sai bayan isha’i ta gama kulewa ta Kai karshe………

        **************
*Federal University dutsinma*
  Kowa yasan sadeeq baida fitina, murmushi kawai yayi yabarshi a wurin yana babatu.
  Sai kawai ya Fara fushi dashi.
Cikin bacin rai sadeeq ya samu Anas, Yana fada mishi abinda Anwar din yayi mishi Kashi na biyu akan Bilkisu.
Yaja guntun tsaki, kayi hakuri sadeeq wallahi *So* ke wahalar dasu duka for now ka bashi time zai nemeka.
Tun daga ranar Bilkisu ta koma sadeeq ke nuna mata, sun kyale Anwar.
Hankalin Anwar yayi matukar tashi ga exams na karatowa, hanya ma idan ta hango shi canzawa takeyi.
  Ya rasa inda zai saka ransa.
Ko kallo bai isheta ba. Idan ta zo school amma tana komawa daki zata ci kukan ta tayi ma’ishi.
Yanzu fa kowa ya fahimci an bata Bilkisu da Anwar. Tsalle da Murna mufeeda ta ringa yi.
Tana zaune class za’a yi lecture ya shigo.
 Yana ganin ta yayi saurin shiga sit din zai zauna kusa da ita…… Sai da ya karaso gaf! Daman can karshe take sai kawai ta kwashi kayanta ta dora waya a kunne , helllooo….yes inajinki. 
Tayi waje kamar me amsa wayar gaske.
Tana fita tayi jimmm sannan ta dawo tare da canza layi ma gaba daya.
    Ransa ya baci, hankalin sa ya Kara tashi, kowa ya fahimci abinda tayi.
Sam ta rage fara’a in kaga tana dariya to tare take da Suleiman.
Ana gama lecture ya tsaya bakin kofa yasa hannu duk Wanda zai fita sai ya mishi magana, tana ganin haka ta yi zamanta, Shima ya ayyana a ransa wallahi yau Kam sai dai su kwana haka.
   Masu shigowa da masu fita kowa sai ya mishi magana sannan.
Ta dawo gaban sit suna magana da chinyere, tayi sa’a ya juya suna magana da wani dan aji daya da alama bayani yakeyi mishi har ya manta ya saki hannu Yana magana cikin nuni da hannu….tayi wuf, ta wuce ko alama bai lura ba sai da tayi nisa ya waiga class din da sauri ya tabbatar lallai ita ce………wani mugun tsoki yaja tare da dunkule hannu ya daki bango har yaron ya tsorata.
Cikin tsawa yace yaron ya bace mishi da gani…..
Daki ya tarar da sadeeq nacin abinci. Yasa chokali kawai Shima, ya kalleshi malam zaka Sanya mun Rani…..dama jira yakeyi yayi magana ko sa shirya. 
Anje an Sanya.
Ya Galla mishi harara kawai.
Anwar din ya rike kunnuwa biyu am sorry my friend pls sorry.
Murmushi sadeeq din yayi kawai.
Ya Fara magiya, har Anas ya shigo yasa baki.
Nan da nan aka koma normal.
Ya kallesu kamar zaiyi kuka. Dan Allah ku shiryani da Bilkisu yarinyar nan tayi fushi dani sosai.
 Wallahi nayi tunanin bayan kwana biyu zata bani hakuri shikenan komai ya wuce ashe ita zafin nata yafi nawa……
Anas ya harareshi, kunfi kusa, a da idan kunyi fadan ku waye ke shirya ki?
Wallahi tsoronta nake yanzu, bana iya tunkarar ta ku taimaka ku shirya mu….
Zamu jaraba gobe….inji sadeeq.
Duk an Fara covering ana shirye shiryen tafiya sallah break ( babbar sallah ), da andawo Kuma da sati za’a Fara exam.
Tana zaune can baya sadeeq ya sameta.
Bayan sun gama gaisawa ya kalleta.
Bilkisu ya kamata ku shirya keda Anwar fadan ya Isa hakanan Dan Allah Kinga……. Mikewa tayi tsaye, tace, sadeeq Ina ganin kimarka da mutunci wallahi duk ranar da ka Kara mun maganar Anwar kaima Zan daina magana dakai har nabar makarantar Nan………ta kwashi books dinta lecture din da bata dauka ba kenan ranar.
Gaban Anwar sai faduwa yakeyi…… Tana fita ya koma inda ta tashi… Yaya?
Sadeeq din ya bata rai tare da fada mishi abinda tace, sai kawai ya dora Kai bisa table yayi shiruuuu!
 Ya dan sunkuya da Kai Anwar idan kana son yarinyar nan ka sameta ku daidaita……..mtseww Shima ya figi takardu yayi waje….ya bishi da ido yace ikon Allah!
    Anas ya taso Yana dariya…… sadeeq ma ya kyalkyace da dariya suka tafa.
Ni naga karshen wannan girman Kan nasu, ko wane ta ciki na ciki sai wahalar da juna ake….
Laifin Anwar ne kasan Allah sadeeq maganinsa Bilkisu.
   Bashi da aiki sai dai ya dauko waya yayi ma sunan ta zuruu Yana kallo. Text din da ta mishi na birthday ya Zama tamkar paracetamol ga Mai ciwon Kai.
 Kwance yake ruf da ciki suka iso, Anas ya tabo Shi …abokina barci kakeyi?
Ya tashi firgigi yace no, Ina jinku kawai na kwanta ne na huta Yaya?
   Ya Mika mishi littafi exercise question din nan zaka solver Mana please…… Wallahi tallahi bazan kara koya ma kowa ba school din nan inbaku shiryani da Bilkisu ba…..hada rantsuwa sadeeq ya zaro ido.
Kana wasa ko?
  Ya Kara Bata rai try me and see. Ya koma ya kife a katifa.
  Nan da nan suka shiga damuwa, Anas ya kalli sadeeq lallai abun nan ya girmama.
  Sadeeq ya nisaaa, kagane kamata yayi mu Sami Suleiman da Helen muje mu Kara bata hakuri kasan Dan iskan yaron nan fa zai Kira Mana ruwa mu shiga uku.
  Yana zaune ya ajiye littafi alamar ita ya ajiyewa sit sakamakon ita ce lecture karshe kowa yayi covering shine yayi saura.
Suka Mika mishi hannuwa ya bisu da ido Yana mamaki saboda yasan clique din su basu daukeshi bakin komai ba har gara gara sadeeq suna gaisawa jefi jefi idan Yana tare da Bilkisu.
Suleiman wannan zuwan naka ne, 
Toh, gani lafiya dai ko?
Da sauki gaskiya, akan Anwar ne da Bilkisu ya rantse cewa duk semester din Nan ba Wanda zai karu dashi matukar ba’a shirya su da ita ba Kuma wallahi ni dana Mata magana cewa tayi na Kara Nima zata daina mun magana.
Murmushi kawai yayi.
Anas yayi karaf! Yace, shine muka yanke shawara mu sameka Dan Allah kasa Baki muje mu Bata hakuri.
Ya Kara murmushi okay ba damuwa.
Har aka tashi class bata zo ba,kawai suka yanke shawarar zuwa gida su sameta .
  Aisha ta Fara haduwa dasu ta fito da alama garin zata bari take shaida masu ai tun karfe bakwai Bilkisun ta tafi Kano zata hau jirgi ta tafi Abuja……….
Kofin dake hannun Anwar ya Fadi ji kake tartsatsatsa…… Lokacin da Anas ke Mata bayani.
Ya kallesu asanyaye… shikenan tunda ta tafi.
 Washe gari Shima suka tafi.
   Abinda yafi komai bata mishi rai shine bata chatting, ya Kira duk wadanda suke tare ko tana da wani layin na daban Amma sunce layinta daya ne kwal!
   Ba abinda ta boye ma mommy hada kukanta.
Yar dariya kawai tayi tace zaku shirya karatu ya gaji haka…….zumburar baki tayi kawai ta wuce ciki.
   Shima ya kasa sukuni, ya gama ayyana ma ransa dole ya kirata ranar sallah ya Mata Barka da sallah tunda ranar kowa na cikin farinciki yasan dole ta saurareshi Kuma ta sauko.
  Hakan kuwa akayi, misalin Sha daya na safe taci kwalliya tana tsaye kitchen tana zuba gasassar hanta a plate Kiran ya shigo…..
*Anwar* shine abinda true caller ta nuna Mata, kamar zata ki dauka sai Kuma ta tuna gara ta dauka ya gane cewar ko number sa bata dashi ……..
Assalamu alaikum. Ta fada a hankali…….luuuuu ya tafi tare da lumshe ido kafin yace wa’alaiki Salam *Barka da sallah*……. Wake magana?
Ta bukata a dake,
Ya zaro ido kamar tana kallonsa…. Bilkisu kin goge number ta?
Tayi shiru kwalla sun taru idonta….
Kinji? Na ce kin goge number ta awayarki?
Kwallah suka shatato Mata tayi tsoki kawai ta kashe wayar……yace what???
Ya Kara Kira.
Tana kallo taki dauka sai da yayi missed call biyar amma Bata dauka ba.
Ya dankara wayar a kasa ta tarwatse sannan ya dafe Kai saboda juya mishi da yakeyi.
Ita kuwa sadadawa tayi zuwa dakinta taci kuka Mai isar ta tukun sai bayan azahar ta fito Shima fa’iza ce ta kirawo ta su fito zasu tafi millennium Park duka gidan.
Tambayar duniya gida Anyi ma Anwar cewar meke damunsa amma yace ba komai fargabar jarabawa ce .
  Sati daya ya koma school ita kuwa sai ana gobe jarabawa sannan.
Don haka basu hadu ba sai dakin jarabawa, ya hangota can gaba, tun kafin su shiga sadeeq ya fada ma Suleiman ya tsaidata ko ta gama don su ganta.
Sai gashi ma duk sun rigata fitowa har Anwar din.
 Ya tafi can nesa bakin bedi ya tsaya su Kuma suna gaban class suna jiranta.
Suleiman man ya Fara tarar ta sannan sauran suka matso aka Mata zobe .
Ya kalli kowa, sannan ya kalleta wannan zuwan naki ne fa, Dan Allah kiyi hakuri ku shirya da Anwar haka nan kinji yace matukar ba’a shirya ku ba ya gama koya ma kowa karatu……..and then?
Sai su dage su koya da kansu Shima ba da iyawa aka haifeshi ba, Suleiman ka fita maganar Nan ba huruminka bane…….ta juya tayi tafiyar ta.
Anas ya zaro ido…. Suleiman ya kallesu Yana murmushi ku Kyaleta Zan lallabeta zasu shirya…… please try your best Dan Allah sadeeq ya fada tana wucewa Anwar ya karaso. Yaya?
Anas ya dankara mishi harara yayi gaba kawai. 
Hankalin sa ya Kara tashi jin ba wata nasara. Amma Suleiman din ya masu alkawarin zai shawo kanta.Hankalin kowa a tashe yake cikin department ganin da gaske Anwar yake bazai koya ma kowa ba matukar bai shirya da Bilkisu ba.
   Ya daina ma kowa dariya tun su sadeeq na daukar abin wasa har suka ga lallai da gasken gaske yake fa.
     Ba Wanda ke iya tunkarar sa,  idanun sa  cikin facing cap yake shigowa Yana rubuta jarabawar za a nemeshi a rasa.
Courses din ana Shan wahalar su, Bilkisu kuwa tuni ta sadakas, idan tana ta exam 3 tun 7 take shiga library sallah kawai ke fiddo ta. A cewar ta in kaji maraya raggo.
  Bai taba tunanin Bilkisu zatayi wannan zuciyar ba Yana tunanin yanda ta Saba da tutorial din sa bazata taba karatu babu Shi ba. 
    Sun Sami interval na kwana daya, da marece tana class tana karatu Suleiman yazo.
   Suka Fara karatun tare…… Wani wuri ya Dan kakare masu.
Yayi murmushi Kinga da kin huce da duk wannan wahalar bamu Sha ta gashi kinja ma kowa, Anwar…… Suleiman ka kasa ganewa na fada maka wallahi ko sunan Anwar bana son inji an fada…..
Saboda me?
Ni bakiyi mun adalci ba wallahi sai nake ganin kamar bani da kima ko mutunci a idon ki, tunda ya Baki hakuri Nima na Baki sai ki……yaushe ya bani hakuri? Wallahi bai bani hakuri ba.
   Mutane nawa ya Aiko Miki? 
To ai mutane kace Shi in person baizo ba ta Yaya Zan San cewar ya gane kuskuren sa?
  …… Yanzu idan yazo da kansa ya Baki hakuri Zaki hakura ku koma normal?……
Tayi shiruuuuu…. Me yasa Suleiman zai Sanya ta kwana.
Kinji? Dan Allah Ina son Anwar yaci albarkaci na ki yi hakuri Kinga Yanzu idan ya dauke hannunsa ga kowa tabbas an Sami matsala Kuma kece sila…… Ni?
Yayi murmushi, kiyi hakuri Bilkisu Yanzu dai, Dan Allah kiyi hakuri.
Ya Gama daureta ta ko’ina, tafi mintuna hudu bata ce komai ba.
Ya Kara kallon ta, Ni zakiyi ma wannan alfarmar ba kowa ba kiyi hakuri.
Kwalla suka suka zuba Mata…… Ta mayar dasu da karfin tsiya sannan ta ce shikenan ya wuce…… Ya zaburo, kin hakura?
Eh, amma ka sani saboda Kai…… Na sani wallahi. Na sani Bilkisu na gode na gode words cannot express my gratitude.
  Suka jero tare ya rakata har bakin gida sannan ya tafi.
Hostel yayi ma tsinke, kamar daga sama suka ganshi karon farko da ya taba zuwa dakinsu.
   Anwar na kishingide Koda Suleiman man din ya shigo ya maida ido ya rufe kunnen sa like da ear piece, ba wani music da ya kunna duk Yana jinsu,
Sadeeq ya fadada murmushi wannan babban bako ne sannu da zuwa Suleiman. Ya ce yawwa tare da Mika ma kowa hannu Banda Anwar.
  Ya kalli sadeeq muje in ganka…… Suka fita tare.
Anas ya kaima Anwar duka Amma Kai Dan iska ne wallahi. Yaron nannya shigo don wulakanci shine ka rufe ido Dan ubanka….. Mtsew yaja tsoki kawai.
Ya kalli sadeeq, na shawo Kan mutuniyar ku, ta hakura ta ce komai ya wuce sai ka fadawa Anwar din saboda kasan……..ya riko hannunsa duka biyunKace wallahi……
Yayi murmushi wallahi kuwa. Amma Suleiman mun gode Allah yabar zumunci dama inata zullumi ranar juma’a za ayi econometrics gashi yayi burus da kowa…..Ya Mika mishi hannu suka Kara gaisawa sannan yace mun gode fa bari naje na mishi albishir …..ya koma daki da sauri.
  Kallo yayi ma sadeeq ya watsar. 
Ni kakeyi ma wannan Dan iskan kallon? To Suleiman zuwa yayi ya fada Mana ya shawo Kan Bilkisu tace ta hakura zaku koma normal…….zumbur ya Mike… Are you serious????
Ya galla mishi harara na ban sani ba kaga wulakancin da kayi mashi da yazo ko kallo……forger about that please ta hakura????
Anas yaja dogon tsoki sai kaje ka fada Mata ka kusa mutuwa….. Ya kyalkyace da dariya a’a ka manta mutuwar nayi.
  Eh Mana, Kuna ta wahalar da kanku a banza……. We are just friends jor what are you talking about???
Ai maganin sa Bilkisun, nifa yarinyar ta bala’in birgeni wallahi ta nuna mishi ita din ta daban ce……Anas ya fada Yana Kara doka mishi harara.
Ya lumshe ido ya koma ta baya ya kwanta…ku yau kuka San Bilkisu ta dabance ko?
   Duk suka dunkule hannu suka Kai mishi duka … sadeeq yace asirinka dai ya tonu munafuki…..ya Kara bushewa da dariya.
 Washegari suna da exam 3, karfe biyu ta fito library jikin wata bishiya bisa kujera ta Kira Suleiman…… Hello ka shigo? 
Eh, kina Ina ne?
Ina ta wajen library wallahi na kasa game wannan last part din, zo kamun dalla dalla please….. Okay Ina zuwa.
Ashe tun karfe tara suna tare da Anwar Yana koya musu a class, ya kalleshi cikin kosawa…….Yaya?
Dariya yayi kafin yace, last part din nan ne bata gane ba take so na nuna……tashi muje ya Mike…..
Anas ya kalleshi Dan uwarka mu Kuma fa ?
Ya dalla mishi harara ku gane …yayi waje.
Daga nesa ta hangosu , tayi saurin boyewa bayan bishiya sannan ta saka wayar ta Airplane mode.
Tana kallonsu sai safa da marwa sukeyi amma ta boye. Har kusan uku saura kwata sannan ta hangosu sunyi hanyar class din da zasuyi jarabawar……… Watan Suleiman kiranshi yayi ko? Ta buga tsoki.
Lokacin da ta Isa har sun zauna invigilators sunzo, ta shiga…idon sa na kanta, Koda wasa Bata yarda ta kalli inda yake ba, Suleiman na bayansa ya Dan gyara alamar ta zauna sai kawai ta wuce kamar bata lura ba.
Ana gama jarabawar, tayi saurin submitting tabar shiyyar.
  Suleiman na fitowa ya kamo hannun sa, kaga ta tafi ko?
Murmushi kawai yayi.
Abu kamar wasa har saura exam uku su gama amma Bata yarda sun hadu ba.
Ya Sami Suleiman kamar zai mishi kuka yace shifa bai gane ba.
    Dole ya sameta yace Dan Allah tayi hakuri ta saurareshi.
Tasha mur, au ni zan sameshi bashine zaizo yaban hakuri ba?…… Ohhh toooo kiyi hakuri zaizo, ta wuce abinta tabarshi wurin saboda yama bata haushi.
Suna rabuwa ya Kira Anwar din yace tace Shi baida bakin bata hakuri ne?
Gaban sa ya Fadi…..Anya zai iya tunkarar ta Yanzu Kam har ga Allah tsoron ta ma yakeyi.
Haka ya kwana dardarce, ko barci kirki ya kasayi da ya tuna sai ya yi firgigi ya tashi zumbur.
   Jarabawar ta safe ce, farar shirt ya saka Mai kwala tana da ratsin ja, da farin jeans sai jar facing cap. Agogon hannun sa kirar *Rado* baka .
Ya rufe ido da makeken glass dinsa Baki. ( Anwar akwai kyau da iya wanka ).
Ba abinda gabansa keyi sai faduwa Anya zai iya mata magana?
Duk inda ya gitta sai an kalleshi ya wanku iyakar wanka sai kamshi ke tashi.
  Yana tsaye jikin taga ya hangota sun taho tare dasu Aisha sai faman dariya sukeyi.
Ya bude littafi kamar Yana karatu amma ita kawai yake kallo…..tana matsowa kirjinshi na Kara bugawa…..kafin ta iso har invigilators sun iso, dole ya shiga hall din ya zauna.
Yana Zama tazo zata wuce yasa kafa tun daga nesa ta hango abinda yayi sai kawai tabi dayan layin.
  Ya rigata fitowa, Banda faduwar gaba har Yar kyarma ya Fara lokacin da ya hango tana fitowa.
Ta zukunna gaban Helen tana fadin …..duba mun wannan shin sune characteristics din nan?…….
   Kamar daga sama taking yace *Bilkisu*……..
Gabanta ya bada rasss!!! Maganar ta makale Mata…….ya Kara kiranta a hankali Yana tsaye bayanta….. *Bilkisu*………..Zainab wowo ce✍????????????????


Ayi hakuri da kadan

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button